zababun Aiyuka-mahimancin yin riko da Addini
shirin zai yi dubu kan mahimancin yin riko da Addini cikin mawuyacin hali yayin fakuwar shugabanmu Bakiyatullah Imam Mahdi
Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. A shirin da ya gabata munyi magana ne kan mahimancin karatun Alkur'ani mai tsarki tare da irin tanadin da Allah madaukakin sarki yayiwa makaranta da kuma mahardantar Alkur'ani mai tsarki a yau shirin namu zaiyi magana ne kan mahimancin yin riko da Addini cikin mawuyacin hali yayin fakuwar shugabanmu Bakiyatullah Imam Mahdi عجل الله تعالی فرجه، ama kafin mu shiga mu shiga cikin shirin ga wannan
Musuc**********************************************
Sikatul Islam Kulaini ya rawaito hadisi a cikin Littafinsa Alkafi daga Amar Sabati yardar Allah ta tabbata a gareshi yace nacewa babban Abdullah Sadik (a.s) wata Ibada ce ta fi lada tsakanin yin Ibada cikin sirri a daular karya kuma lokacin fakuwar Imam Zaman cikin zaman jiran bayyanarsa da kuma Ibada a lokacin bayyanar gaskiya kalkashin daular Imam (a.s)? sai Imam (a.s) yace min Ya Amar bayar da Sadaka cikin sirri wallafi tafi wadda aka bayar a bayyanai haka zalika yin ibada cikin sirri yayin fakuwar Imami kalkashin Daular Karya tafi ibadar da a kayi a kakashin daular Gaskiya wadda Imamin wannan Lokacin ke jagoranta.domin ba daya ba ne yin ibada a cikin tsoro kalkashin daular zalinci da kuma ibadar da a kayi cikin konciyar hankali ba tare da wani haufi ba kuma kalakshin hukumar Limamin Gaskiya.ku sani cewa duk wanda ya sallaci wata salla ta Farilla cikin Jam'u kuma ya tsaidata kamar yadda aka yi umarni lokacin da yake cikin tsoro na makiya, Allah zai rubuta masa ladan salla 50 wadda aka sallata a jam'u ba cikin wannan yanayi ba .haka zalika duk wanda ya sallati sallar farilla guda a fakaice kuma ya cikkata kamar yadda aka yi umarni yayin da yake cikin tsoron makiya to Allah zai rubuta masa ladan sallar farilla 25 kuma duk wanda ya sallaci sallar nafila a irin wannan lokaci kuma ya cikata kamar yadda aka umarceshi Allah zai rubuta masa Ladan sallar Nafila guda10 har ila yau duk wanda ya aikata wani aiki mai kau a irin wannan lokaci na fakuwar Imam, Allah zai bashi lada 20 kuma ya rubunyamasa kyawawen aiyuka na mumunai idan ya kautata aikin nasa,yayin da yayi takiya don kare Addininsa da Imaminsa da kuma kansa daga kaidin makiya ya rike bakinsa Allah zai rubunya masa lada rubi rubi domin Allah madaukakin sarki mai kirma ne.
Masu saurare bayan Imam (a.s) ya bayyana mana falalar riko da addinin Gaskiya a lokacin fakuwar Imam har ila yau Imam ya bayyana mana falalar yin ibada yayin da Dan Adam ke fuskantar wani hadari a yayin da Amar Sabadi ya tambayesa yace na sadaukar da kaina a gareiku hakika wallahi ina kodayin yin aiyuka managarta amma yanzu kun karya mini gwiwa amma ku bani labari yaya za ayi Ibadarmu tafi ta Mutanan da suke cikin jiran Imaminsu a lokacin fakuwarsa alhali Addininmu guda ne? Sai Imam (a.s) yace masa Ibadarku tafi ta su saboda ku kun gabace su shiga cikin Addinin Allah madaukakin sarki kuma kun rigayesu tseda salla,azumtar Azumi, yin aikin Hajji da ma duk wasu aiyukan Alkhairi tare da ibadar Allah madaukakin sarki kuna masu buwa daga duk wani sharri na makiyanku kun kare Imaminku daga duk wani sharri na makiya kuma kuna biyayya a gareishi kuma masu hakuri tare dashi,kuna masu zaman jiran bayyana Daular gaskiya, kuna masu tsoro a kan abinda zai samu Imaminku da kawunanku daga sarkunan zalinci, har ila yau kuna masu zaman jira na kwato da hakin Imaminku da kuma hakkokinku daga hanun Azzalimai, babu shakka sun hanaku kuma ba zu su baku ba har abada, sun sanyaku kuna cikin dardar wajen neman abincinku da gudanar da ibadarku haka zalika ku kayi hakuri da rikon Addininku ku kayi ibadanku a wannan yanayi tare da yin biyayya ga Imaminku duk da irin fargabar da kuke da ita ta Makiyanku saboda haka Allah madaukakin sarki zai rubunya muku ladan aiyukanku kuma ina taya ku murna a kan hakan.
Musuc**********************************************
Masu saurare barkanku da sake saduwa,bayan mun bayyani kan mahimancin riko da Addini a lokacin fakuwar Imam(a.s) shirin namu zai ci gaba da bayyanan mahimancin dawamma a kan aikata aiyuka managaranta kamar su yin Ibada da saurensu.
A cikin littafin Mizanil Hikma na Ayyatullahi Rai shahri an rawaito wani hadisi wanda yake cewa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya kasance yanada wani abin shunfuda guda idan yayi sallar dare a kasance sai ya shunfudashi da safe kuma ya zauna a bisan shi sai Sahabansa suka fara koykoyansa a kan hakan har masu koykoyon suka yi yawa sai wata rana Manzon Rahama yace masu Ya Ku Mutane kuyi koyi da abinda za ku iya domin Allah madaukakin sarki ya fi so aikin da bawa zai yi ya dawwama da yinsa komin kadan kinsa babu shakka iyalan gidan Annabi duk aiyukan da suka fara suna ci gaba da shi wato suna dawwama wajen yinsa.
Har ila yau an rawaito wani hadisi daga Imam Sadik (a.s) cikin littafin Alwasa’il inda hadisin ke cewa Imam Sadik (a.s) ya kasance yana ta Ambato wannan Magana yana cewa hakika Aba ja’afar(a.s) yana nifin babansa Imam Bakir yana cewa babu abinda nafi so kamar in dawwama a kan aiyukan da na sabawa kaina da shi,idan aikin da nake yi na dare ya bar ni sai in ramasa da rana haka zalika idan aikin na rana ne ya bar ni sai in ramashi da daddare domin babu aikin da Allah madaukakin sarki ya fi so kamar aikin da aka dawwama ana aikata shi.
Muna rokon Allah madaukakin sarki ya bamu ikon dawwama a kan aikata aiyukan alkhairi komin kanantarsu
Musuc*********************************************
Masu saurare anan muka kawo karshen shirin na yau sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin in Allah ya yarda a madadin wanda ya hada shirin a ka saurara ni da na shirya ni ke mukun alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.