Mar 04, 2016 05:47 UTC
  • zababun Aiyuka-Soyayyar iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

shirin zai yi bayyani dangane da Soyayyar iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka tare da yin da'a a gareisu kamar yadda hadisai masu yawa suka yi ishara a kan hakan


Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. A shirin da ya gabata munyi magana ne kan mahimancin riko da Addini Allah madaukakin sarki a cikin yanyin kunci na wahala tare da fargaba na tsoron  na makiya Addini a yayin fakuwar Imamu Zaman (a.s) a yau shirin namu zaiyi magane ne dangane da Soyayyar iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka tare da yin da'a a gareisu kamar yadda hadisai masu yawa suka yi ishara a kan hakan  amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari wannan


 


Musuc**********************************


 


Hakika an rawaito hadisi cikin littafin Almahasin daga shugabanmu Imam Aliyu bn Musa Arrida (a.s) yana cewa duk wanda yake farincikin ganin Allah ba tare da hijabi kuma Allah madaukakin sarki ya kalleshi ba tare da wani hijabi ba, to ya so Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka kuma yayi koyi da su  sannan ya kauracewa duk wani makiyansu sannan ya tsika biyayar tashi da shugaban mumunai daga cikin su wato yayi biyayya da shugaban mumunai na lokacinshi daga iyalan gidan Monzon Allah tsarkaka, ranar Alkiyama Allah zai kallesa ba tare da wani hijabi ba kuma shima zaiga Allah ba tare da hijabi ba. Abinda ake nufi da kallo a wannan riwaya ba wai kallo na ido da ido ba abinda ake nufi shine tsananin kusanci  da bawa zai yi Allah madaukakin sarki tare da rahamarsa


Har ila yau a cikin Littafin na Almahasin an rawaito wani hadisi daga Fudail yana cewa na cewa Babbab Hasan Rida (a.s) wani Aiki ne ya fi kusantar da bawi zuwa ga Allah? Sai Imam Rida (a.s) yace fiyayyen aikin da yafi kusantar da bayi zuwa ga mahalicinsu shine biyayya ga Allah da ma'aikinsa, soyayyar Allah da kuma Ma'aikinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka ta kuma biyayya ga majibinta Al'auranku domin Abu Ja'afar Albakir (a.s) ya kasance yana fadar cewa (sayayya a gareimu imani ne kuma kiyayya a garimu Kafirci ne ).


Har ila yau an rawaito wani hadisi daga Amiril mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s)yacewa Abi Abdullahi Judly shin kana so in baka labarin kyakyawan aikin wanda duk wanda ya zo da shi ranar Alkiyama zai amintu daga tsoron wannan rana, da kuma mumunan aikin da duk wanda yaje da shi Lahira zai Allah zai watsa masa kayansa a wuta? Sai Abi Abdullahi Jadly yace Na'am ya kai shugaban mumunai sai Aliyu bn Abi talib (a.s) yace masa kyakyawan aikin shine soyayyarmu kuma mumunan aiki shine yin kiyayya a gareimu.


 


Masu saurare daga cikin wasiyoyin da Imam Rida(a.s)yayi, musaman ma na cikin littafin Fikhu Rida ya bayyana cewa ku yawaita yin Salati ga Manzon Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka, da kuma yawaita yin addu'a ga mumnai Maza da Mata dare da rana, domin yiwa Annabi salati tare da iyalan gidansa tsarkaka na daga cikin fiyayyun aiyuka wanda Allah madaukakin sarki yayi umarni da shi, kuyi to kokarin na biyan bukatun Mumunai , da sanya farin ciki a zukatan mumunai tare da kore duk wani bacin raid a damuwa da suka shiga domin babu wani aiki da Allah madaukakin sarki ya fi so bayan ayyukan farilla kamar sanya farin ciki a zukatan mumunai, kadda ku bar ayyukan mangarta tare da kokari cikin ibada Allah saboda dogaro na Soyayyar Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarka, haka zalika kadda ku bar soyayyar iyalan Gidan Ma'aikin Allah tsarkaka  da kuma  biyayya a gareisu saboda riko da Ibada domin su abu biyu daya baya wadatarwa said an uwansa guda.


 


Musuc***************************************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa  a cikin gaban shirin har yanzu muna dauke da wasu riwayoyi wadanda suke magana dangane da mahimancin biyayya ga Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka.


A cikin littafin Amahasin an rawaito wani hadisi daga Manzon Allah yana cewa ku lazumci Soyayyarmu mu Ahlulbait domin duk wanda ya hadu da Allah madaukakin sarki cikin soyayyarmu Ahlulbait zai shiga Aljanna da tsetonmu na rance da wanda ke raina ke hanunsa babu wani aikin Bawa da zai masa amfani matukar bai san hakkinmu ba.


An samo wani hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yana cewa duk wanda yake sonmu Ahlulbait kuma ya tabbatar da Soyayyarmu a cikin zuciyarsa babu shakka kalaman hikma za su rika gudana a halshansa kuma Imani zai tabbatu a cikin zuciyarsa.