zababun Aiyuka-Mahimancin Addu'a
shirinzai yi dubu ne kan mahimancin Addu'a gami da irin tarin albarkatun dake tattare da wanda ya dawwama da yin ita
Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. A shirin da ya gabata munyi magana ne dangane da yadda aka umarcemu da Soyayyar Ahlulbait wato iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka tare da yin koyi da biyayya a gareisu, a yau kuma shirin namu zai yi dubu ne kan mahimancin Addu'a gami da irin tarin albarkatun dake tattare da wanda ya dawwama da yin ita, amma kafin nan bari mu sausari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.
Musuc********************************************
Hakika babban malamin nan masanin Fikhu kuma Arifi Sheik Ahmad bn Fahad Alhilly cikin littafinsa (عدة الداعي)ya rawaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka inda yake cewa fiyayyar Ibada a wajen Allah madaukakin sarki Addu'a, idan Allah ya baiwa bawansa izinin yin Adu'a sai ya bude masa kofofin Rahamarsa kuma lalle shi wannan bawa ba zai hallaka matukar yana yin du'a'i.
Har ila sheihun malamamin ya rawaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) inda daya daga cikin sahabansa suka tambayeshi shin minene yafi tsakanin yawan karatu da yawan yin Addu'a? sai Imam(a.s) yace masa yawan yin Addu'a yafi sannan sai ya karanto masa wannan Aya ta Alkur'ani mai tsari cikin suratu furkan kamar haka ka ce ba ruwan ubangijina da ku in ba don Addu'arku ba.
Har ila yau Imam Bakir (a.s) yace babu abinda Allah madaukakin sarki ya fi so ga bawansa kamar ya yi tambaya ya roki bukatunsa a gareishi.
A cikin littafin Kafi shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) yana cewa fiyayyen aikin da Allah madaukakin sarki yafi so a doron kasa ita ce Addu'a kuma fiyayar Ibada wadda a kayi cikin nutsuwa.
Babu shakka Addu'a na daga cikin fiyayun aiyuka wadanda suke kusantar da bayi ga mahalicinsu kamar yadda shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya bayyana mana yace Na horeku da yawaita yin Addu'a domin babu abinda ya fi kusantar da bawa ga mahalicinsa kamar Addu'a. har ila yau a cikin Littafin Kafin shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik ya bayyana irin mahimancin Addu'a tare da irin dunbun Albarkar dake cikinta a rayuwanmu ta Duniya da Lahira a yayin da yake yin wasiya ga Sahabansa yana mai cewa na horeku da Addu'a domin babu wani abu da yafi Addu'a ga musulmai wajen samun biyan bukatu a wajen ubangijinsu,ku yawaita yin Addu'a da meka bukatunku tare da kaskantar da kai zuwa ga Allah, ku yawaita tambaya ,ku yawaita meka bukatunku a wajen Allah ,ku amsa kirar da yayi muku domin ku rabauta kuma ku tsira daga Azabar Allah.
Musuc*********************************************
Masu saurare barkanku da sake da saduwa, a ci gaban shirin muna dauke da wasu hadisai wadanda suke shiryar damu wajen yin kokari tare Ijtihadi wajen karfafrawa Imani da Allah madaukakin sarki tare da samun tunani mai kau na neman kara sani ga mahalicinmu da kuma dogaro a gareishi tare da kore duk wani kokonto wanda zai bata mana Imaninmu.
Masu saurare babu shakka yin tutani a kan ayoyin Allah madaukakin sarki na daga cikin hanyoyin dake karfafa imanin Bawa haka zalika yin irin wannan tunani ga sunayansa tsarkaka da kuma yadda ya halincin Duniya kuma yake tafiyar da Al'amuran bayinsa kamar yadda shugabanmu Imam Rida (a.s) ke bayyana mana a hadisin da aka ruwaito cikin littafin Kafi kamar haka:yawaita Salla da Azimi ba shi ba ne kawai Ibada sai dai yin tunani da Nazari a kan Al'amuran Allah madaukakin sarki shima babbar ibada ce.
Sheik Saduk (r,t.a) cikin littafinsa mai suna kitabul Khisal ya rawaito wani hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) yace ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace fiyayyen aiyuka a wajen Allah madaukakin sarki,yin Imani ba tare da wani kokonto ba, yin jahadi ba tare da satar ganima ba, aikin hajji da a kayi ba tare da wani sabo ba, wato ya zamanto kudaden da a kayi aikin hajjin kudaden halak ne kuma an kiyaye yin sabo wajen gudanar da dukkanin aiyukan sai Imam ya ci gaba da cewa farkon wanda zai shiga Aljanna Shahidi wato wanda ya rasa ransa ta hanyar Allah musaman ma wanda ya mutu a wajen yaki saboda Allah sai kuma na biyu bawan da ya kautata bautarsa ga mahalicinsa sannan kuma yayi nasiha ga shugabaninsa, na uku Mai kamewa wanda baya meka hanunsa ga wani idan ba Allah ba kuma ko da yana cikin mawuyacin hali kuma ya nada yawan iyali.sannan kuma wanda zai fara shiga cikin wuta shugaban da yaki babakere a kan komai kuma baya yin adalci, na biyu wanda ya samu dukiya mai yawa kuma bai hudda hakin dukiyar wato baya bayar da sadaka kuma baya fidda zakka baya kauta wannan abubuwa guda 3 hakin dukiya ne wanda wajibi ne ga duk wanda ya mallaki dukiya ya fitar da su domin hakki ne a kansa yayi hakan, sai kuma na gaba shine Tallaka mai yawan Alfahari. Allah subhanahu wata'alla ya bamu ikon kiyaye duk wani mumunan abu da kuma tabbatar da duk wasu aiyuka masu kau da aka umarcemu.
A cikin Littafin fikhu Rida(a.s) an rawaito wani hadisi wanda ke cewa wata rana wani Mutune ya je wajen Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace masa ya ma'aikin Allah bani labarin fiyayun aiyuka a wajen Allah madaukakin sarki Sai Ma'aikin Allah yace: Imani da Allah, sai kuma yace bayan shi fa? Sai Ma'aikin Allah yace sada zumunci, sai Mutuman nan ya kara cewa bani labarin aiyukan da Allah ya fi fishi da su ,sai Ma'aikin Allah yace masa aikata shirka wato hada wani abin bauta da Allah madaukakin sarki, sai mutuman nan ya ci gaba da cewa bayansa fa? Sai Ma'aikin Allah yace:yanke zumunci sannan sai wannan ya ci gaba da cewa bayan su kuma fa? Sai Ma'aikin Allah yace masa yin umarni da sabo tare da yin hani ga aiyuka nanagarta.
Musuc**************************************************
Masu saurare anan muka kawo karshen shirin na yau sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin in Allah ya yarda a madadin wanda ya hada shirin a ka saurara ni da na shirya ni ke mukun alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.