Mar 04, 2016 06:32 UTC
  • zababun Aiyuka-Taimako ga mabukata

shrin zai yi bayyani kan mahimancin yin taimako ga mabukata tare da yin kokarin wajen biyan bukatun bayin Allah


Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. A shirin da ya gabata munyi bayani ne dangane da hadisai wadanda suke shiryar da bawi wajen karfafa imaninsu ga mahalicinsu, a yau kwa shirin namu zaiyi magana ne kan mahimancin yin taimako ga mabukata tare da yin kokarin wajen biyan bukatun bayin Allah , amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


 


Musuc*************************************


 


Hakika sheik Saduk (r.t.a) ya rawaito wani hadisi cikin littafinsa manla yahduruhul Fakih daga Maimun bn Mehran yace:na kasance a zaune wajen Imam Hasan Dan Aliyu bn Abi Talib(a.s) shi kuma yana cikin I'itikafi a Massalacin Annabi(s.a.w) sai wani Mutune ya zo masa yace Ya Dan Ma'aikin Allah a kwai wani Mutune da yake bina bashin kudi kuma yayi barazanar daure ni idan har ban biya shi ba, sai Imam Hasan(a.s) yace wallahi bani da kudi wanda zan biya maka wannan bashi a halin yanzu, sai wannan Mutuman yace masa to kayi masa magana wata kila zai amince ya bani wani lokaci, sai Imam Hasan (a.s) ya sanya takalminsa ya tashi da niyar su tafi wajen mai kudin tare da wannan bawan Allah sai nace masa ya Dan Ma'aikin Allah shin ka mance da cewa kana cikin I'itikafi ne? sai yace mani ban manta ba saidai naji babana Aliyu bn Abi talib (a.s)yana cewa kakana Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa duk wanda yayi kokari wajen magance wata haja ta dan uwansa musulmi kamar ya bautawa Allah madaukakin sarki tsahon shekaru dubu tara yana azumtar dukkanin ranaikun wannan shekaru tare da raya daren baki daya.


Har ila yau an rawaito wani hadisi a cikin littafin  مشكاة الأنوار في غرر الأخبار daga Ma'aikin Allah (s.a.w.s) na cewa taimako ga masu rauni na daga cikin fiyayyar Sadaka.


Shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa duk wanda ya bada lunfashinsa guda daya wajen kore wata damuwa ta Dan uwansa musulmi yafi dukkanina Azumin da azumta tare da sallolin da ya sallata  lada kuma wannan na daga cikin fiyayun aiyukan dake kusantar da bawa zuwa ga Allah madaukakin sarki.har ila yau a wani hadisi na daban Imam Sadik (a.s) duk wanda ya taimaki wani mabukaci (wato mabukacin ko an zalince shine ko kuma yayi wata asara ce )ko kuma ya taimaka wajen ganin an magance wata matsala da mumuni ya shiga Allah zai rubuta masa Rahamarsa so 73sai ya ajje masa guda 72 har ranar Lahira sannan ya bashi guda a nan Duniya.


 A cikin Littafin (الإحتجاج) na sheik Tabrasi yardar Allah ta tabbata a gareishi an rawaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Aliyu bn Musa Arrida (a.s)yana cewa  fiyayan aikin da wani Malami daga cikin Masoyanmu da mabiyanmu zai iya tanadarwa kansa a ranar talucinsa,bukatrsa kaskancinsa wato wannan rana itace ranar Kiyama ya ceci wani miskini daga masoyanmu daga hanun makiyanmu , makiya Allah da ma'aikinsa a nan Duniya sai Imam (a.s) ya ci gaba da bayyana albarkar dake cikin wannan aiki a ranan tashin Alkiyama yana me cewa zai tashi daga cikin Kabarinsa tare da Mala'ikan Allah sahu-sahu za su masa rakiya har zuwa cikin Aljanna za su dauki shi a bisa fika fikansu  suna masu taya sa murna suna cewa madalla da abinda  ka samu muna tayaka murna da wannan.


A cikin littafin Almahasin an rawaito wani hadisi daga Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa na cewa aiyukan da Allah madaukakin sarki ya fi so guda uku ne, na farko ciyar da musulmi mabukaci,na biyu biyamasa bashinsa, na uku magance matsala ko damuwarsa.


 


Musuc*************************************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a ci gaban shirin muna dauke da wasu hadisai masu bayanai dangane da Tauhidi.a cikin Littafin Almahasin na babban malamin hadisin nan Albarki an rawaito hadisi daga manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa fiyayyar Ibada firta Kalmar tauhidi ma'ana cewa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah tare da cewa babu tsimi babu dabara sai dai ga Allah kuma mafi Alkhairin Du'a'I shine yawaita yin  Istigfari.


A bayyanai yake cewa wadannan Azkar na daga cikin anbaton Allah masu tsarkake zukata daga duk wani nau'in shirka tare da duk wani nau'I na zunubai kuma firta kalamar cewa babu tsimi babu dabara sai dai ga Allah shike tabbatar bawa cewa ba zai iya komai ba idan ba Allah ya so ba don haka wannan kalma za ta bashi karfin gwuwa wajen neman dogaro ga Allah madaukakin sarki da duk wata ibada da zai aikata tare da ko wani irin akin da yake son gudanarwa.


Masu saurare babban abu mai mahimancin shine ya kasance gudanar da Azkar ya zamanto cikin sani domin hakan zai sanya bawa yin kodayi ga rahamar ubangijinsa kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) yace fiyayyar Ibada sanin Allah. Wato wajibi ga bawa ya nemi sanin ubangijinsa kafin ya bauta masa.


A cikin littafin Kafi na sheik Kulaini yardar Allah ta tabbata a gareishi an rawaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) na cewa duk wanda ya karanto wannan zikiri so 15 a rana (ga zikirin  لا إله إلا الله حقاً حقاً، لا إله إلا الله عبودية ورقاً، لا إله إلا الله إيماناً وتصديقا Allah madaukakin sarki zai karkata mahangarsa zuwa gareishi kuma ba za canzata ba har sai ya shiga cikin Aljanna.


Masu saurare daga cikin bayanai na hakikanin aiki da kamal shahada shine bayanin da shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib yayi a cikin Littafin Nahju Balaga inda yake cewa zan baku labarin abubuwa guda biyar wanda idan har kuka hau kansu kuka yi aiki da su babu shakka za ku samu rabauta kuma duk irin neman da za kuyi ba za ku samu kamar su ba.sai Imam ya ci gaba da cewa kadda kuji tsoron wani idan ba Allah ba kuma ku tabbatar da wannan hakan a aikace kadda ya kuyi kodayin wani abu a wajen wani in ba Allah, kuma kadda wani Malami yayi kunyar cewa bai sani ba idan aka tambayeshi abinda bai sani ba, kuma kadda wanda bai sani ba ya ji kunyar neman Ilimi, kuma kuyi hakuri a kan dukkanin Al'amura.


Muna rokon Allah madaukakin sarki da ya bamu damar yin aiki da wannan nasihohi na shugabanin shiriya


 


Musuc*******************************************


 


 Masu saurare anan muka kawo karshen shirin na yau sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin in Allah ya yarda a madadin wanda ya hada shirin a ka saurara ni da na shirya ni ke mukun alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.