zababun Aiyuka-Jihadi fi sabilillah
Shirin zai yi bayyani ne dangane da jihadi fi sabilillah ko kuma muce yaki saboda Allah tare da irin tanadin da Allah madaukakin sarki yayi ga mujahidai wato masu yin jihadin
Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun ayyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. A shirin da ya gabata munyi bayani ne dangane da wasu hadisai wadanda suka bayyanai ne kan mahimancin Tauhidi, shirin namu na yau zai yi bayyani ne dangane da jihadi fi sabilillah ko kuma muce yaki saboda Allah tare da irin tanadin da Allah madaukakin sarki yayi ga mujahidai wato masu yin jihadin amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan
Musuc***********************************************
Hakika masu saurare akwai ayoyi da dama cikin kur'ani mai tsarki tare da hadisai masu dunbun yawa wadanda suka bayani a kan mahimancin Jihadi a tafarkin Allah musaman ma kan irin dunbun ladan da Allah madaukakin sarki yayi ga mujahidai, saboda mahimancinsa tare da yawan ladansa har yasa idan ana so a bayyana yawan lada na wani managarci aiki da sakamasako mai yawa sai a kwatamta shi da ladan yin jihadi saboda Allah madaukakin sarki. A shirin namu na yau mun zabo wani hadisi jami'I wato wanda yake bayyanai ga dukkanin daki daki na Jihadi saboda Allah tare da bayanai dunbun ladan da a kayi ga mayinsa.
Hakika Sikatu Islman kulaini ya rawaito hadisi cikin littafinsa Alkafi daga Fudail bn Ayad yace na tambayi babban Abdallah Imam Sadik (a.s) dangane da hukuncin jihadi a musulinci shin farilla ne ko kuma sunna ne?Sai Imam Sadik (a.s) yace jihadi kashi 4 ne kashi na farko da na biyu farilla ne, kashi na uku suna ne amma da sharadi, kashi na hudu kuwa Sun ace ba tare da wani sharadi ba, na farko yadda Bawa sai yaki juciyarsa wajen hanata aikata sabo , wannan shi ne babban jihadi, na biyu kwa yakar wadanda suke zarkinku daga kafirai farilla ne, na uku wanda ya kasance sunna ci amma bisa sharadi, shardin kuwa shine Imami wato wasiyin Manzon Allah na wannan lokaci sunna ce a kansa. babu shakka yakar makiya farilla ne bisa dukkanin Al’umma kuma mai yuyuwa idan sun kaucewa yin yakin wato suka ki zuwa yaki bayan Imaminsu ya basu umarni Azaba ta sauka a kansu irin wannan nau’in azaba ita ce azabar da Al’umma ta kira da kanta, irin wannan jihadi sunna ne a kan wasiyin Monzan Allah kawai na kowani lokaci don haka Imami daga Imaman Gidan Ma'aikin Allah shi kadai ne a ka baiwa dammar fiddo Al’umma don yakar makiya kuma shine ya kasance a kansa Sunna amma ga Al'umma farilla ne saboda biyayya a gareisu wajibi ne, kashi na hudu kwa shine duk wata sunna ta ma’aikin allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka idan bawa yayi kokarin tabbatar da ita kuma yayi jihadi wajen tsedata da rayata to hakan na daga cikin zababbun aiyuka domin yin hakan shine raya sunar ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka kuma Ma’aikin Allah na cewa duk wanda ya aikata wata Sunna mai kwau za a bashi Ladanta da ladan wadanda suka aikatata har zuwa ranar Alkiyama ba tare da an ragemasa komai ba daga cikin wannan lada na wadanda suka aikata wannan kyakkyawar sunnar.
Masu saurare muna rokon Allah madaukakin sarki da ya sanyamu daga cikin Mutanan da basa shagaltuwa wajen aikata aiyukan Alkhairi tare da raya sunar Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.
Musuc********************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a ci gaban shirin za mu yi bayani ne dangane da mahimancin yin Addu'a tare da Tahajuddi a cikin Dare kamar yadda Sahaban Ma'aikin Allah suka samu rabauta saboda aikata hakan tare da irin Addu'o'I da Ma'aikin Allah masu buko da kari kan yadda ya roka masu Ubangijinsa domin su samu Rahamarsa da Albarka mai dunbun yawa.
A cikin littafin مستدرك الوسائل an rawaito hadisi daga Ma'aikin Allah ya na cewa Allah yayi Rahama ga duk Bawan dake Tashi cikin Dare yayi salla kuma ya umarci Iyalansa suyi salla, ku saurara sallar Dare na daga cikin zabbabun aiyuka da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa
A cikn Littafin(عيون الحكم والمواعظ) na Wasidi an rawaito wani hadisi daga shugaban muwahidai Imam Ali(a.s) yana cewa :fiyayar Ibada hana Idanu barci wajen anbaton Allah madaukakin sarki ko bada himma wajen anbaton Allah ,domin yin zikri na haskaka zukata kuma shi ne fiyayyar Ibada, wanda yafi kowa karfin Imani shine wanda ya fi su dogaro ga Allah.
A cikin littafin biharu Anwar an rawaito wani hadisi daga Imam Sadik (a.s) a lokacin da yake bayyanawa daya daga sahabansa mahimancin anbaton Allah tare da zababben lokuta na ambaton Allah,yana mai cewa Ya Fadl: fiyayyen lokaci na anbaton Allah shi ne karshen Dare domin Allah madaukakin sarki na cewa A Lokacin Sahur kuma Su, suna neman gafara.
A cikin wani hadisi na Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbatar a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka an bayyana cewa yin Istigfari a lokacin Sahur na daga cikin zababbun Addu'a na Shur kuma na daga cikin fiyayun aiyuka da Allah madaukakin sarki ya fi so bugo da kari ya nada Lada mai tarin yawa gami da Albarka wacce ba ta da iyaka.
A cikin wata riwaya kuwa ,shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa babu wani dikon hawaye da ya zuwa, wanda Allah madaukakin sarki ya fi so kamar wanda aka zubar da shi cikin duhun Dare dan tsoron Allah kuma babu wani karfin hali ko karfin Zuciya da Allah ya fi so ga bawansa kamar idan ya shiga wata damuwa ko wata musiba ya taushe zuciyar ya hana kansa aikata sabo wato yayi hakuri kadda ya fada cikin sabo.
Masu saurare a bayyanai yake babu zababbun aiyuka da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa kamar neman gafara tare da yawaita yin istigfari a cikin dare don meman Allah madaukakin sarki ya yafe masu kurakuren da suka aikata kamar yadda a bangaren farko da wannan hadisi aka bayyana hakan sai kuma bangare na biyu inda hadisin yayi bayyani dangane da mahimancin juriya da karfin hali wajen saba wa zuciya aikata sabo ko kuma meda martani ga wanda yayi maka mumunan abu.
Musuc*******************************************
Masu saurare ganin lokaci na hararanmu a nan zamu dasa Aya sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin in Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim Kiyawa ya hada shirin a ka saurara ni da na shirya kuma na gabatar ni ke mukun fatan alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.