zababun Aiyuka-Mahimancin Addu'a
Shirin zai yi bayyani kan mahimancin Addu'a ga Dan Adam tare da zababban lokaci da a kafi so bawa ya kadaita ga ubangijinsa,a shirin namu na yau za muyi dubi ne kan wasu Hadisai wadanda suka yi bayyani kan kaucewa sabon Allah
Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. A shirin da ya gabata munyi magana ne dangane da mahimancin Addu'a ga Dan Adam tare da zababban lokaci da a kafi so bawa ya kadaita ga ubangijinsa,a shirin namu na yau za muyi dubi ne kan wasu Hadisai wadanda suka yi bayyani kan kaucewa sabon Allah amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
Musuc****************************************
Ba shakka kaucewa sabon Allah na daga cikin zababbun aiyuka da Allah madaukakin sarki ya umarci bayinsa da shi,wanda hakan shi zai sanya Dan Adam ya samu kyakyawar makoma kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ke bayyana wa sahabansa a cikin riwayar da aka rawaito cikin Uyunul Akhbar da ke cewa: (idan Bawa yana son ya gama lafiya wato yayi kyakyawan karshe to ya kasance yana aikata aiyuka managarta kuma ya girmama Hakkin Allah da yake kansa sannan ya kaucewa sabon Allah komai kankantarsa, ya girmama duk wanda yake kiran kansa a matsayin masoyanmu babu ruwan shi da cewa karya ne yake ko Gaskiya, yayi aiki da niyarsa ta Alkheiri idan karye ce yake to shi da Allah.
Masu saurare a cikin wasiyoyin Manzon Allah tsira da amince Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan Gidansa tsarkaka ga sahabbansa, Ma'aikin Allah ya sha jadadda musu wajibcin riko da Addinin Allah, tsoron Allah tare da kaucewa duk wani sabo komai kankantarsa kuwa. Kamar yadda yayi bayyani a khudubarsa wadda take bayyani kan falalar Azumi da sheik Saduk (r.t.a) ya rawaito cikin littafinsa mai suna Al'amaly, ganin cewa riwayar tana da tsawon gaske, mun dauko karshen wannan riwayar ce , inda a karshenta Imam Ali(a.s) na cewa sai na tashi tsaye na ce Ya Ma'aikin Allah wani aiki ne yafi a cikin wannan wata mai Alfarma ?(wato watan Azumi) sai Ma'aikin Allah yace Ya Baban Hasan fiyayyen aiki a cikin wannan wata shi ne kaucewa sabon Allah madaukakin sarki sannan sai ya fashe da kuka sai nace masa ya Ma'aikin Allah mene ne ya sanya ka kuka? Sai yace Ya Ali ina kuka ne saboda abin da zai same ka a cikin wannan wata, kamar ina kallonka a lokacin da kake salla kana saduwa da Ubangijinka sai wanda yafi kowa shakiyanci a nan duniya da lahira bayan wanda ya kashe Taguwar Samudawa, ya sare ka da takobinsa har jini sai ya hade da gemunka. Sai Amirul mumunin (a.s) yace ya Ma'aikin Allah shin hakan na daga cikin Maslaha ga Addinina ,sai Ma'aikin Allah yace masa eh hakan yana cikin aminci ga Addininka Sannan Manzon Allah ya ci gaba da cewa Ya Ali duk wanda ya kashe ka kamar ya kashe ni ne, duk wanda ya sanya ka fishi kamar ya sanya nine, duk wanda ya zage ka kamar ya zage ni ne domin kai daga ni ka ke ruhin ka daga ruhi na ne? Domin Allah madaukakin sarki ya halicce mu ne daga ruhi guda sannan ya zabe ni tare da kai kuma ya zabe ni a matsayin Annabi sannan ya zabe ka a matsayin Khalifa na duk wanda yayi inkarin Khalifancinka kamar yayi inkarin Annabtata ne,Ya Ali kaine Wasiyina baban Jikokina mijin Diyata Fatima kuma Khalifa na ga Al'ummata a rayuwata da kuma Lokacin da na kaura, bin umarninka kamar bin Umarni nane, saba maka kamar an saba mini ne, na rantsee da wanda ya aiko ni a matsayin Annabi kuma ya sanya ni mafi Alkhairin Halitta lalle kaine hujjar Allah a kan bayinsa kuma aminceccensa a kan duk wani sirrinsa kuma khalifansa a kan Bayinsa.
Musuc**************************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa , a ci gaban shirin za mu karanto wasu daga cikin wasiyoyin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidan tsarkaka. Daga cikin zababbun wasiyoyi na Ma'aikin Allah wadanda za su mana jagora ga samun rabauta a Duniya da Lahira akwai wacce ta fito daga bakin Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) kamar yadda aka rawaito a cikin littafin Nahjul Balaga inda Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ke cewa: fiyayyen abinda masu neman dogaro za su yi dogaro da shi wajen Allah, Imani da Allah tare da Ma'aikinsa da yin Jihadi bisa tafarkin Allah madaukakin sarki domin wadannan sune tushen musulinci, fadar Kalmar tauhidi ita kuma Fitirar Dan Adam ce, tseda salla kuwa shi ne tafarkin tabbatar da Addinin musulinci , bayar da zakka kuwa wajibi ne ga duk wanda Allah ya mallaka masa Dukiya, Azumtar Watan Ramadana garkuwa ce daga wuta, yin aikin Haj da Umara kwa su kuma suna kore talauci tare da shafe zunubai, sada zumunci kuwa na kara Arziki kuma yana kara kwanaki, bayar da sadaka cikin sirri tana kore dukkanin kurakure, bayar da sadaka a bayyane na kiyaye mutuwa ta kai tsaye, aikata aiyuka managarta na karfafa Bawa tare da yin kokowa dangane da irin raunin da Adam ke da shi.
Har ila yau masu saurare muna tare da kalaman Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) inda yake bayyana mana mahimancin ambaton Allah madaukakin sarki tare da karatun kur'ani mai tsarki.
Imam Ali (a.s) yana cewa ku yawaita anbaton Allah madaukakin sarki domin shine mafi kyawon zikiri,ku kyadaito da abinda Allah yayiwa bayinsa masu tsoransa alkawali,domin wa'adinsa gaskiya ne, kuyi koyi da tafarkin Annabinku domin shine fiyayyen shiriya, kuyi koyi da sunnarsa domin itace fiyayyar shiriya, ku koyi karatun Alkur'ani domin shine mafi kyawan hadisi, ku nemi sanin ilimin dake cikin Alkur'ani domin yin hakan na tausasa zukata, ku nemi waraka da haskensa domin shi hasken zukata ne,ku kyautata yin tilawarsa domin a cikinsa akwai mafi kyawawen Kissosi,hakika duk malamin da baiyi aiki da iliminsa ba to kamar jahili mai rauni wanda ya gafala wajen neman Ilimi saboda rauninsa kai gwara shima da malamin da baya aiki da iliminsa saboda shi yana da hujja ta sani kuma baiyi aiki da shima don haka yafi kowa hasara a Duniya da Lahira kuma zaifi fuskantar zarki fiye da kowa a wajen Allah madaukakin sarki.
Musuc**************************************************
Masu saurare ganin lokaci na hararamu a nan za mu dasa aya sai kuma a muku na gaba za'a jimu da wani sabon shiri idan Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada shirin aka saurara ni da na gabatar da shi nike muku fatan Alkhairi wassalama aleikum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.