zababun Aiyuka-Wasioyin Iyalin Gidan Ma'aikin Allah
shirin zai yi dubu ne kan kan wasu daga cikin wasiyoyi na iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Masu saurare Asslama aleikum barka da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin Zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin namu na yau zaiyi dubi ne kan wasu daga cikin wasiyoyi na iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka. Amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
Musuc**************************************************
Masu saurare daga cikin wasiyoyin Iyalan Gidan Ma'aikin Allah tsarkaka za mu fara ne da wasiyar Shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib(a.s) wacce yayi ga Dansa Shugaban samarin Aljanna Imam Hasan (a.s) a lokacin da yake bisa gadonsa na kaura daga wannan duniya . Sheikh Mufid (rta) ya rawaito wannan wasiya cikin littafinsa Al'amaly yana mai cewa Ya Hasan ina yimaka Wasiya da irin wasiyar da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi a gareini kadda ka meda Duniya ita ce mahangarka wato kadda ka sanya Duniya a gaba, Ya kai Dana ina horonka da tsaida Salla a farkon lokaci,bayan da Zakka ga mutanan da su dace a baiwa kuma a lokacinta, shuru a kuraren da yin magana bata da wani amfani ,ka zamanto mai tattali a aiyukanka, mai adalci a lokacin dakecikin fishi ko kuma akasain haka, yin makobtaka da Mutanan kirki,kirmama Baki,tare da yin Rahama ga masu rauni da kuma Mutanan da suka shiga cikin wani Bala'I, kuma ka zamanto mai sada zumunci tare da nuna Soyayya ga miskinai ka zauna tare da su ya kai dana, wannan na daga cikin zababbun aiyuka da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa.
A cikin littafin Uyunul Hikam wal Mawa'iz an rawaito wasu daga cikin wasiyoyin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka wadanda za su yi mana jagora wajen hayewa zuwa kololuwar Imani tare da samun rabauta a Duniya da Lahira. Daga cikin wannan wasiyoyi Imam Ali (a.s) yana cewa na horeku da kamun kai tare da rikon Amana domin sune za su mutunta duk wani sirrinku da kuma abinda kuka bayyana, wannan shine fiyayen tanadi da za kuyi a nan Duniya ,na horeku na wannan Alkur'ani, ku halarta abinda ya halarta kuma ku haramta duk abinda ya haramta, ku nemi sanin ilimin dake cikinsa ,inda yake da shubuha ku maida shi ga Ahalinsa wato ku tambayi masanansa domin sune shaida a gareiku , kuma shine fiyayyen abinda za kuyi dogaro da shi, na horeku da kirmama rayuka ko na minene don biyan bukatunku, hakan ya zamanto shine gimshikin aiyukanku hakan sai sanya ku kubuta daga duk wata yaudara da shaidan, na horeku da yin Gaskiya a duk aiyukan da za ku aikakta , masu Ikhlasi a dukkanin aiyukanku, masu kyakyawar Niya a aiyukansu , wannan shine fiyayen ibadar makusanta, Na horeku da dawwama wajen godeya mahalicinku, kuma masu hakuri domin yin hakan na kara maku Ni'imar Ubagijinku, kuma ya kore maku duk wata damuwa.
Musuc*******************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, daga cikin zababbun aikuwa da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa a kwai aikata aiyuka na gari musaman ma a bagen mu'amalar mutun da 'yan uwansa.
A cikin littafin khisal an rawaito wani hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa fiyayyar kautar da Allah madaukakin sarki yayi ga musulmi itace kyakyawar dabi'a.
Har ila yau sanya farin ciki a zukatan mumunai na daga cikin kyakyawan Dabi'u kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ke cewa a cikin riwayar da aka rawaito cikin Kamilu Ziyarat daga cikin aiyukan da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa a kwai Ziyarar kabarin Imam Husain (a.s) da kuma sanya farin ciki a zukatan mumunai kuma lokacin da bawa yafi kusanci da mahalicinsa shine lokacin da yake cikin sujada kuma yana kuka saboda tsaron Ubangijinsa.
Har ila yau a cikin littafin Kamilu Ziyarat an rawaito wani hadisi wanda ke bayani a kan falalar ziyarar kabarin Imam Husain (a.s). an tambaye Imam Sadik (a.s) minene zai cimma ga wanda ya kai ziyara a kabarin Imam Husain bn Ali (a.s) sai Imam Sadik (a.s) yace zai cimma fiye da abinda zai samu daga Aiyukansa managarta.
Masu saurare bari mu koma kan batun kyawawen dabi'u ganin irin dunbun ladan da Allah madaukakin sarki yayi tanadi ga masu wannan siffofi tare da masu kokarin yin mu'alar mai kau tare da Mutane.a cikin littafin Tuhuful Ukul an rawaito wani hadisi daga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yana cewa Ya Allah wannan shine addinin da na yarda da shi ni kaina ,kuma babu abinda zai kyara shi sai kyauta da kyawawan dabi'u,Ya Allah ka kirmama shi da su da kuma wadanda suke tare da shi.
Kuma Ma'aikin Allah Ya ce:wanda ya fi imani daga cikinsu wanda ya fi ku tabi'u masu kwau.
Masu dabi'u mai kwau suna samun darajar wadanda suka dawwama da yin Azumi tare da raya dare wajen salla da karatun Alkur'ani mai tsarki.kamar Manzan Allah ya bayyana a yayin da aka tambaya shi daga cikin kautukan da aka baiwa bawa wannene ya fi sai yace kyawawen Dabi'u.kuma a wani hadisin Ma'aikin Allah na cewa kyakyawar dabi'a ta Dan Adam ita ke tabbatar da Soyayarsa a garemu.
Har ila yau masu saurare a wani Hadisi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa zababbu daga cikinku wanda suka fi kowa dabi'u masu kwau wadanda kyauwawan dabi'unsu zai sanya Mutane su zamanto suna kodayin yin mu'amala da su.
Musuc *****************************************
Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe ,sai kuma a Maku na gana za a jimu dauke da wani shirin idan Allah ya yarda, a madadin Aminu Ibrahim Kiyawa da ya hada shirin aka saurare, ni da na shirya kuma na gabatar na ke muku fatan Alkhairi, wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.