Mar 04, 2016 03:13 UTC
  • zababun Aiyuka-mahimancin zaman jira na bayyanar  Imam Mahdi

shirin n zai yi bayyani kan mahimancin zaman jira na bayyanar cikomakin wasiyan Manzon Allah Bakiyatullah Imam Mahdi Ajjalallahu ta’ala farjuhu


Masu saurare Assalama aleikum barkanmu da sake saduwa da ku cikin wani sabon shiri na zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin na mu na yau zai yi magana ne a kan mahimancin zaman jira na bayyanar cikomakin wasiyan Manzon Allah Bakiyatullah Imam Mahdi Ajjalallahu ta’ala farjuhu domin hakan na daga cikin zababbun aiyukan musulinci kamar yadda hadisai da dama suka tabbatar da hakan amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


Musuc**********************************************************


Sheik Tanukhi ya nakalto wata riwaya a cikin littfinsa, juzi’I na farko babin dake bayani kan bayyanar Imam bayan zaman tsanani na zaman jira kamar haka. An rawaito hadisin ne daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib karramallahu wajhaho yana cewa babu wani abu da aka jarabci Al’umma da shi kamar zaman jira na bayyanar Imami zaman , hakuri  bisa duk wani bala’I da bawa ya hadu da shi domin sakamakon hakuri shine Nasara kuma duk mai hakuri ba zai tabe ba a bisa kyakyawan zatonsa.


Abinda ke cike tabbacin zaman jira na bayyanar Imam shine riko da Addinin gaskiya  tare da yawaita yin du’a’I da kuma karkata zuwa ga Allah madaukakin sarki kamar yadda hadisai da dama suka bayyana.


A cikin littafin kamalu din na sheik Saduk an rawaito wani hadisi daga managarcin bawan nan Jabir Ju’ufi wacce ya nakalto daga Imam Abi Ja’afar Albakir (a.s) ya ce : zai zo wani lokaci ga Mutane wanda imaminsu zai fake ,farinciki ga wadanda suka rike Addini kuma suka yi riko da Al’amuranmu a wannan lokacin, karamin abinda za su samu na sakamako shine Allah madaukakin sarki zai kira su ya ce ma su ya bayi na hakika kun yi imani da sirrina, kuma kun gasganta Gaibina , ina muku albishin da kyakyawan sakamako daga gareni, na amince da ku a matsayin bayina na gaskiya,zan amshi addu’I’inku, zanyi muku afuya, zan gafarta maku, kuma sabo da ku zan sabkar da ruwa ga bayina tare da hana sabkar duk wani bala’I, in bad an ku ba da na sabkar da azabata.Jabir ya ce :sai na ce ya Dan Ma’aikin Allah wani aiki ne ya cancanta ga mumuni ya aikata a wannan lokaci?sai Imam Bakir (a.s) ya ce masa kiyaye harshe tare da lazamtar zaman gida.wato a wannan lokaci a na son mumuni ya kiyaye bakinsa da firta duk wasu kaalaman da ba su dace ba tare da sa ido sasai ga iyalansa saboda lokaci da Albahasha da sabon Allah ya zamanto wani abin ado wajen mafi yawan Mutane a Duniya.


Musuc********************************************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a ci gaban shirin za muyi bayyani ne dangane da mahimanci kyautata yin aiyuka na gari ba tare da yin alfakhari ba.


A cikin littafin Algabat an rawaito wani hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tbbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa Aikin da yafi ko wanne lada shine wanda aka aikata shi cikin sirri .


Hakika an rawaito hadisai da dama wadanda suke bayyani dangane da dunbun lada wadanda aka yi tanadi ga masu anbaton Allah a boye da masu bada sadaka cikin sirri da makamatansu.


A cikin littafin kafi an rawaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) an tambaye shi wace sallar ce tafi wacce sunna ta amfata? Sai ya ce dukkanin raka’o’I hamsin wato sallar farilla tare da dukkanin Nafilfilu na yini sune za su hadu su zamanto raka’a khamsin. Har ila yau an rawaito wani Hadisi makamancin wannan daga Imam Hasan Askari (a.s)inda yake bayyana cewa hakika yin raka’o’I khamsin da daya cikin yini na daga cikin alamar imani.


Amma zababbun ayoyin da aka fi so a karanta cikin sallar farilla bayan karanta suratul Hamdu,a kawai suratu Kadri kamar yadda riwayar shugabanmu Bakir (a.s) ke yin ishara da hakan , a cikin littafin Almahasin an rawaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) na cewa duk wanda ya karanta suratu kadri a sallarsa za a daga sallar zuwa cikin illiyina, (illiyina littafi ne wanda ake tara aiyukan alkhairi na Mala’iku da mumunai a cikin wani guri a sama kalkashin Al’arshi) kuma wannan za ta zamanto karbabbiya tare da rubunya ladanta, sannan duk wanda ya karanta wannan Sura ta Kadri bayanta ya roki Ubangijansa Allah zai amshi rokonsa sannan a daga Addu’ar ta sa zuwa lauhul Mahfuz.


Hakika hadisai da dama sunyi bayyani kan fifikon karanta suratul kardi bayan karatun Fatiha a raka’a ta farko cikin sallar farilla da kuma fifikon karantun suratul Ikhlasi a raka’a ta biyu bayan karatun fatiha, yawan hadisan a wannan fage shi ke tabbatar da inganci wadannan riwayoyi.


Nitsuwa tare  fiskantar Allah madaukakin sarki  cikin tunani a cikin Salla na daga cikin gimshikin salla kamar yadda wani hadisi daga  shugabanmu Imam Bakir (a.s) ke bayyani a kan hakan, a cikin littafin Mahasin an rawaito hadisi daga Imam bakir (a.s) na cewa duk wanda ya fuskanci Alkibla domin tseda salla ,ya fuskanci mai rahama ne da dukkanin sassan jikinsa wanda babu wani abin bauta da gaskiya face shi.har ila yau a cikin littafin na Almahasin an rawaito wani hadisi daga Shugaban mumunai Aliyu bn abi talib (a.s) na cewa duk wanda ya kabarta salla to a kwai wasu abubuwa guda uku tare da shin a farka mala’ikan Allah madaukakin sarki za su kewayesa,sannan biyayya zata kara tabbatuwa a gareishi, sai kuma a kwai mala’ika guda a hanunsa na dama da kuma hanunsa na hagum idan