Mar 04, 2016 06:46 UTC
  • zababun Aiyuka-Falalar azumin Nafila

shirin zai yi bayyani dangane da falalar azumi na Nafila tare da zababbun lokcin yin azumin kamar yadda sunar ma'aikin Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka ta yi umarce da su


Masu saurare Assalama aleikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shiri na zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin na mu na yau zai yi magana ne dangane da falalar azumi na Nafila tare da zababbun lokcin yin azumin kamar yadda sunar ma'aikin Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka ta yi umarce da su. Amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan


 


Musuc********************************************************


 


Hakikia sheik Kulaini ya nakalto wani hadisi daga Zuraratu bn A'ayun cikin littafinsa mai Albarka Alkafi inda Zuraratu bn A'ayun ke cewa  na tambayi babban Abdallahi Sadik (a.s) a kan cewa minene sunna ta yi umarni da shi  wajen  yin azumin nafila? Sai Imam Sadik (a.s)ya ce  azumin kwanaki uku a ko wani wata, na farko azumtar farkon Alkhamisin ko wani wata, rana ta biyu azumtar  ranar laraba ta ko wani tsakiyar wata, rana ta uku azumtar ko wata ranar Alkhamis ta ko wani karshen wata.wato wadannan lokuta guda uku sune zababbun lokuta na yin Azumin Nafila a musulinci.


Har ila yau daga cikin zababbun aiyuka , amsa kiran Dan uwansa musulmi idan ya gayyace shi wajen cin abinci  matukar Bawa ba shi  da wani uziri koda  yana azzumin Nafila matukar ba  azumin farilla ne yake ba kamar yadda aka rawaito wani hadisi cikin littafin Ja'afariyat daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa abinda ya fi kwau ga mai yin azumi idan dan uwansa musulmi ya gayyace shi wajen cin abinci to ya bar azumin na shi na wannan rana wato ya shi abinci tare da wanda ya gayyace shi matukar azumin na shin na wannan rana ba na farilla ba ne ba, ko kuma na ramuwa ne , ko na Nazr ne wato wanda aka dauki alkawalin yin Azumi matukar anyi sharidin yin nasa sakamakon wata bukata da aka gabatar a wajen Allah madaukakin sarki kuma bukatar ta cika. Masu saurare wannan shine irin mahimanci da Addinin musulnci ya baiwa sada zumunci inda ya fifita amsa kiran dan uwa gami  da cin abinci tare da shi a kan azumin Nafila.


Har ila yau daga cikin mahimancin gayyatar musulmai zuwa cin abinci sheik saduk ya rawaito wani hadisi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidan tsarkaka a cikin wani littafinsa mai suna (مصادقة الإخوان) inda Monzan Allah ke cewa:duk wanda ya ciyar da musulmi guda uku abinci Allah zai ci yar da shi daga abincin Aljanna guda uku,ta farko wacce ke cikin malakutu Sama'a wato Aljannar dake cikin milkin Allah a Sararin samaniya, ta biyu itace Aljannar Firdausi sai kuma ta uku Aljanna wacce koramunta ke gudanya kuma Allah da kansa ne ya ginata.


Har ila yau a cikin wannan littafi an rawaito wani hadisi daga Imam Bakir (a.s) na cewa daga cikin zababbun aiyuka a kwai abubuwa guda uku na farko toshe yinwar dan ukanka musulimi , warware matsalarsa kuma da suturtar da shi .


  


masu saurare daga cikin zababbun aiyukan Hajji shine cewa idan Bawa ya gudiri zuwa aikin hajji yaje a kafafunsa har isa zuwa ga Dakin Allah madaukakin sarki , hakika an rawaito hadisi a cikin Littafin  (غوالي اللئالي) daga zababben mai shiriya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa fiyayyen abinda Bawa zai fi kusanci da shi ga Allah madaukain sarki shine idan ya tashi tafiya aikin hajji ya tafi da kafafuwansa kuma wannan shine Allah ya fi so daga bayinsa.


dangane da mahimancin wannan riwaya an rawaito hadisai da dama kan tafarkin shugabanin shiriya kuma samarin gidan Aljanna Imam Hasan da imam Husaini (a.s) an bayyana cewa a rayuwarsu sun je aikin hajji so 25 da kafafuwansu tare da rakiyar zababbiyar tawagga.


 


Musuc**************************************************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a ci gaban shirin za muyi bayani ne dangane da mahinmancin yin tunani ga kudrar Allah madaukakin sarki wacce ke karawa bawa karfin imani tare da kodaitar da shi aikata alkhairi. A kan haka an rawaito hadisai da dama daga iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka.


Sheik Abu Ja'afarur Barki ya rawaito hadisi cikin Littafinsa Almahasin daga Husaini Sukail (r.t.a) ya ce na tambayi babban Abadallah Imam Sadik (a.s) kan wannan hadisi shin wai da gaske ne cewa tunanin Awa guda ya fi ibada tsakiyar Dare? Sai Imam Sadik(a.s) ya ce hakane domin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa yin tunani na Awa guda ya fi ibada tsakiyar Dare sai aka tambayeshi shin wani irin tunani Ya ma'aikin Allah? sai Ma'aikin Allah ya ce kamar yadda bawa zai fice daga rusasun gidaje sai ya tambayesu shin ina wadanda suka ginaku? Ina wadanda suka zauna a cikinku? Shin mi nene ya sa ba ku magana wato ba  su bada amsarawa?irin wannan tunani shi ke sanya bawa ya tuna da cewa kamar yadda wadanda suka gida wadannan gidaje da suka ruje suka koma ga Allah shima wanda yayi saura zai koma ga Allah.


Har ila yau a cikin littafin Al'amaly sheik saduk ya rawaito wani hadisi inda aka bayyana cewa Haruna Abbasi ya rubutawa  babban Hasan Musa bn ja'afar (a.s) wata wasika inda ya bukace shi yayi masa galgadi amma a takaice sai Imam Kazim (a.s) ya rubuta masa cewa duk abinda idanuwanka suka ganemaka to hakika a kwai Mu'ijizar Allah madaukakin sarki a cikinsa.


Masu saurare daga cikin tsani na tunani a kwai yin tunani ga abubuwan da suka shafi rayuwa ta yau da kulun wanda zai sanya Dan Adam ya dauki darasi daga cikinsa.a cikin littafin Khisal an rawaito wani Hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa:ya kasance mafi yawan Ibadar Abi Zarrul Gafar  Allah yayi masa rahama yin tunani a batuwan da suka shafi na rayiwa tare da dauka Darusa daga cikinsu.


Har ila yau daga cikin tsaunin na tunani a kwai yin tunani ga Ayoyin Allah madaukakin sarki da kuma kudurarsa wanda hakan na daga cikin abubuwan dake karfafa Imanin Dan Adam amma hakan baya samuwa ga ko wani dan Adam sai wanda yake da sani ga ilimin Addini.


A cikin littafin Kafi an rawaito wani hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa fiyayyar Ibada yin tunani ga Allah madaukakin sarki tare da kudurarsa.har ila yau a cikin wannan littafi an rawaito hadisi daga Imam Rida(a.s) na cewa yawan salla da yawan Azumi ba shi ba ne hakikanin ibada saidai yawan tunani a al'amuran Allah madaukakin sarki. Masu saurare  irin wannan tunani shine zai kasance garkuwa wajen aikata aiyuka na gari kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s)ya bayyana cewa tunani shine wanda zai mana jogora ko kuma mai shiryar da mu zuwa yin biyayya tare da aikata ayyuka managarta.


muna rokon Allah madaukain sarki ya bamu damar yin tunani wanda zai mana jagora wajen kara yin biyyaya a gareishi tare da aikata aiyuka na gari


 


Musuc*********************************************


 


Masu saurare a nan za mu dasa aya sai kuma a maku na gaba idan Allah ya kaimu za a jimu dauke da wani sabon shiri a madadin Aminu Ibrahim Kiyawa da ya hada shirin aka saurara ni madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.