Mar 04, 2016 03:18 UTC
  • zababun Aiyuka-Sanya farin ziki a zukatan Al'umma

Shirin zai yi bayyani kan mahimancin sanya farin ziki a zukatan Al'umma


Masu saurare Assalama Aleikum barkanmu da sake saduwa a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin na mu na yau zaiyi magana ne kan mahimancin sanya farin ziki a zukatan Al'umma, amma kafin nan bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.


 


Musuc************************************************


Ba shakka ,kautatawa tare da sanya fara'a a zukatan bayi na daga cikin zababbun aiyuka wanda Allah madaukakin sarki yayi umarni, a kwai hadisai da dama wanda suke bayyani dangane da mahimancin kautatawa , sanya fara'a a zukatan bayi musaman ma Mumunai da kuma irin  dunbin ladan da Allah madaukakin sarki yayi tanadi  ga masu aikata wannan aiki mai daraja. A cikin Littafin kafi an rawaito hadisi daga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan Gidansa tsarkaka na cewa ba shakka daga cikin aiyukan da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa sanya farin ciki a zukatan mumunai.


Har ila yau a cikin wannan littafi mai albarka an rawaito hadisi daga Imam Ja'afaru Sadik (a.s) na yi mana albishi dangane da irin girman sakamako da Allah madaukakin sarki yayi tanadi ga mai aikata hakan.inda yace hakika Allah madaukakin sarki yayi wahayi ga Annabi Daoud (a.s) yana mai ce masa hakika duk wani Bawa daga cikin Bayina idan yazo min da wannan aiki mai kyau zan sanya shi cikin Aljanna Sai Annabi Daoud (a.s) ya ce Ya Ubangiji na wani kyakyawan aiki ne wannan? Sai Allah madaukakin sarki ya ce sanya fara'a a zukatan mumunai ko da da Dabinu guna. Sai Annabi Daoud (a.s) ya ce hakika  ya ubangiji babu shakka ga duk wanda ya sanka ba zai yanke kauna ba daga gareika.


Masu saurare hakika daga cikinmu babu wani wanda zai ki yayi wani aiki wanda zai faranta zuciyar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka ba,to wannan aiki kwa shine sanya far'a a zukatan mumunai kamar yadda wannan riwaya ke yima bayyani ,a cikin littafin kafi an rawito hadisi daga Imam Sadik(a.s) ya ce: kadda da yanku ya ga cewa idan ya sanya fara'a a zuciya wani mumuni ya sanya wannan farin ciki ne kawai ga wannan mumuni ba , babu shakka hakan bai takaita ba kawai ga wannan mumuni ba wallahi duk wanda ya sanya farin cikin a zuciya mumuni kamar ya sanya farin ciki ne a garemu sannan yace kai bari wallahi kamar ya saya fara'a ne a cikin zucuyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka. Har ila yau masu saurare Imam Sadik(a.s) ya ci gaba da yin bayyani dangane da irin tarun Albarka dake tattare da wannan aiki mai daraja yana mai cewa idan Allah madaukakin sarki ya tayar da mumuni daga kabarinsa  sai ya fito tare da wani aiki wanda zai masa jagora, duk lokacin da mumuni ya ga wani abu mai tayar masa da hankali na ranar tashin Alkiyama sai wannan aiki ya ce masa kadda kaji tsoho ko fargaba ina yimaka Albishir da farin ciki tare da kirmamawa daga Allah madaukakin sarki har sai wannan aiki yayi wa wannan mumuni jagora zuwa ga mahalicinsa a yi masa hisabi mai sauki sannan ayi ma wannan jagora umarni ya isa da shi zuwa gidan Aljanna,sai wannan mumuni yacewa jagoran nasa Allah yayi maka rahama naji dadin wannan aiki wanda na tashi tare da shi daga cikin Kabari na, ka kasance kana mai yi mani albishir na farin cikin da Karama daga mahaliccina har saida naga haza shin wai wanene kai? Sai wannan  aiki yace masa :nine wannan farin ciki wanda ka sanya shi ga Dan'uwanka mumuni a Duniya, Allah madaukaki sarki ya halicceni domin in kasance tare da kai kuma in zamanto mai albashir a gareika.


Muna rokon Allah madaukakin da ya bamu ikon aikata wannan aiki mai albarka kuma ya sanya mu daga cikin wadanda za su tashi daga cikin kabuburansu tare da wannan aiki.


 


Musuc**************************************************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a ci gaban shirin muna dauki da wasu zababbun aiyuka wanda Allah madaukakin sarki ya umarci bayinsa da aikatasu.


Hakika Sheik Saduk (r.t.a) ya rawaito wani hadisi cikin Littafinsa mai albarka Ilalu Shara'I'I daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yana cewa idan bawa yana son ya gane shin a kwai Alkhairi a gareishi to ya dibi zuciyarsa idan akwai soyayyar masu da'a ga umarnin Allah madaukin sarki kuma yana kiyayya ga masu sabon Allah, idan ya tabbatar da hakan to babu shakka a kwai alkhairi a gareishi kuma yana daga cikin masoyar Allah madaukakin sarki, amma duk Zuciyar da ta ga tana kiyayya da masu biyayya ga Allah kuma tana son masu sabon Allah to babu shakka wannan zuciya na tare da shari kuma Allah na kiyayya da ita,domin ko wata zuciya na tare da masoyinta.


Hakika  yawaita Addu'a da Munajati na daga zababbun aiyuka wadanda za su sa musa rabauta ga Soyayyar Allah tare da yardar sa domin shi Allah mai ramana ne.Amirur mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) na cewa.fiyayyan aiyukan da Allah madaukakin sarki ya fi so a doron kasa shine Addu'a. Imam Sadik (a.s) na cewa Shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya kasance mai yawan Addu'a.


 


Amirur Mumunin (a.s) na cewa Allah madaukakin sarki yana son mai yawan Addu'a sannan ya bayyana mana mahimancin Addu'a inda yake cewa Addu'a mabudin rahama ce da rabauta, mafi alkhairin Du'a'I wacce ta fito daga bakunar masu tsoron Allah ko kuma zukatan masu tsoron Allah.


A cikin Littafin Kafi an rawaito hadisi daga Imam Sadik (a.s)yana cewa na hore ku da yin Addu'a domin Addu'a waraka ce ga ko wata irin cuta.


 


Musuc*********************************************


 


Masu saurare a nan za mu dasa aya sai kuma a maku na gaba idan Allah ya kaimu za a jimu dauke da wani sabon shiri a madadin Aminu Ibrahim Kiyawa da ya hada shirin aka saurara ni madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu