zababun Aiyuka-Tabi'ar Dan Adam
Shirin zai yi bayyani kan dabi'ar Dan Adam na nemawa kansa Alheri tare da ki wa kansa duk wani sharri
Masu saurare Assalama Aleikum Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. Sanannan abu ka ko wani Mutne , ko wani Dan Adam na neman sani tare da bin abubuwan da suka fi komai a ko wani fage na rayuwa Hakika ko wani Mutune a Duniya na bayan abinda yafi kau wajen gudanar da rayuwarsa, wannan itace tabi'ar da ko wani Dan Adam ke neman asarta a rayuwarsa ta Duniya
Hakika amsar wannan tambaya Nassosi na Shari'ar Musulinci sun bayar da amsar . amsar kwa itace aikata kyawawen aiyuka domin shine ke sanya nutsuwa a cikin zuciya tare da samun Hakikanin jindadi na rayuwar Duniya da Lahira.
Bayan haka, Nassosi na musulinci sun koyar da mu fiyayun aiyuka kyawawa wanda a hakinkanin Gaskiya hakan na daga cikin tabbatuwar Rahama da Allah madaukakin sarki yayi a kan bayinsa gami da fiyayyar rabauta na jin dadi da kuma yardar Allah madaukakin sarki a Duniya da Lahira.
Masu saurare wannan shiri zai dubu ne ga wasu Hadisai tare riwayoyi na musulci wadanda za su mana jagora wajen aikata fiyayun aiyuka domin samun rabauta a rayuwarmu ta Duniya da Lahira.amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
Musuc****************************************
Masu saurare shirin namu na yau zai fara ne da wasu hadisai dake ishara kan fiyayyun Ayyuka wadanda za su mana jagora zuwa ga hasken Allah madaukakin sarki wanda a hakikanin Gaskiya wannan wata kauta ce da Allah subhanahu wa ta'ala yayi ga bayinsa don samun rabauta a Duniya da lahira .Hakika Sheik Saduk ya rawaito wani Hadisi daga Ma'aikin Allah kuma masoyinsa, Rahama ga Talikai baki daya Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka cikin littafinsa mai suna Kitabul Sawabul A'amal wal Khisal inda a cikin wannan riwaya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa abubuwa guda hudu duk wanda ya kasance a cikinsa zai kasance cikin Hasken Allah madaukakin sarki: na farko duk wanda ya kasance karshen Al'amuransa ya firta kalmar لا اله الا الله و انا رسول الله wato babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah kuma ya shaida cewa ni Ma'aikin Allah ne ma'ana duk wanda ya kasance a kan kadonsa da mutuwa kuma karshen lokacin da zai koma ga Allah madaukakin sarki ya firta yafirta arlar shahada ,na biyu duk wanda wata Musiba ta samaishi zai ce daga Allah muke kuma a gareishi za mu koma , na ukku duk wanda wani abun Alkhari ya same shi zai ce dukkan yabo ya tabbata ga Allah ubangijin Talikai na hudu shine duk wanda ya aikata kuskure zaice ina neman Gafara ga Allah sannan kuma ina tuba a gareishi.masu saurare wadannan sifoffi guda hudu sune Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace mana duk ya kasance yana da su zai kasance cikin hasken Allah madaukakin sarki .
Riwayarmu ta gaba za ta yi dubu ne kan fiyayun aiyuka wadanda ke baiwa Dan Adam damar kammala Hakikanin Imaninsa.Hakika Sheik Barki ya rawaito hadisi cikin Littafinsa mai suna Almahasin inda a cikin wannan Riwaya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidan tsarkaka na cewa duk wanda ya cika Alwallarsa ya kyautata Sallarsa,ya kuma bayar da zakarsa ,ya kame fishinsa ko kuma ya hadiye fishinsa , ya kamai bakinsa daga fadar munanan kalamai kuma ya nemi gafarar ubangijinsa kan irin kuskuran da ya aikata sannan ya yi aiki da Nasihar iyalan gidan Ma'aikin Allah , babu shakka ya kammala hakikanin Imani kuma Kofofin Aljanna a bude suke a gareishi.
Musuc********************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a cigaban shirin muna dauke da wasu riwayoyi wadanda suke bayyani kan makamai masu kare mumuni a rayuwarsa mai albarka.
Sheik saduk yardar Allah ta tabbata a gareishi ya rawaito wani hadisi cikin Littafinsa mai Albarka daga Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan tsarkaka inda wata rana yace wa Sahabansa shin kuna son in bakun labarin wani makami wanda zai tsirar da ku daga makiyanku kuma ya kara maku arzikin ku? Sai suka ce Na'am ya ma'aikin Allah sai Annabi(s.a.w.) ya ce masu ku roki ubangijinku dare da rana domin Addu'a takobin mumuni ce.
Ba shakka masu saurare, abinda Ma'aikin Allah ya ke nifi a wannan riwaya bai takaita ba kawai da zama dare da rana wajen karanta Addu'a ba, har da yadda Bawa zai zamanto ya zuya Al'amarunsa zuwa ga Allah ya zuwa zuciyar, harshensa, aiyukansa kai duk abinda zaiyi ya zamnto yayi saboda Allah ko ya na cikin tsanani ko akasin haka.
Imam Ja'afar bn Muhamad Assadik (a.s) yana cewa Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya kasance yana fadar cewa babu wani Mutune wanda zai shiga cikin wata jarrabawa komin girmanta idan yayi Addu'a zai samu waraka sannan ya amintu daga duk wani bala'i.
A cikin wata riwaya Kwa Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa Addu'a takobin mumuni ce,kuma kimshikin Addini ce har ila yau hasken samai da kasai ce. Domin haka Addu'a ta kasance wata garkuwa ga Annabawan Allah aminci ya tabbata a gareisu kamar yadda shugaban Imam Rida (a.s) ya kasance a ko wani lokaci yana yiwa sahabansa wannan wasiya yana mai cewa nah ore ku da makaman Annabawa sai sahabansa suke cewa mi nene makaman Annabawa? Sai Imam Rida (a.s) yace ma su Addu'a.
Kamar yadda aka rawaito a cikin littatafan Addu'a na cewa Addu'a garkuwar mumuni ce, a wata Addu'a ta Imam Ali (a.s) yana isharar cewa Addu'a garkuwar mumuni ce duk lokacin da aka yawaita yin Addu'a sai kokofin Rahama su bude.fiyayyar Addu'a yiwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare iyalangida tsarkaka salati kamar yadda aka rawaito cikin litattafai da dama na musulinci.
اللهم صل على محمد وآل محمد الأوصياء المرضيين بأفضل صلواتك وبارك عليهم بأفضل بركاتك والسلام عليه وعليهم وعلى أرواحهم وأجسادهم ورحمة الله وبركاته".
Musuc*****************************************
Masu saurare a nan shirin namu na yau zai dasa Aya sai kuma a Maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda, a madadin Aminu Ibrahim Kiyawa da ya hada shirin aka saurara ni madugun shirin ni ke muku fatan Alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.