Mar 04, 2016 06:54 UTC
  • zababun Aiyuka-Kwadayin aikata alheri

Shirin zai yi bayyani kan kwadaitar da Mutane aikata yin Alkheiri tare da taimakon mabukata


Masu saurare Assalama aleikum barka da sake saduwa da ku a cikin shirin kyawawen dabi'un musulnci wanda ni Aminou Abdou ke gabatar das hi.daga cikin kyawawen Dabi'un musulnci wanda ayoyi da dama suka yi ishara a kansu a kwai kwadaitar da Mutane aikata yin Alkheiri tare da taimakon mabukata akwai ayoyi da dama wadanda suke magana kan taimako har inda Allah madaukain sariki wanda shine mawadaci sannan dukkanin bayi a wajensa suke meka bukatarsu yana cewa wane ne zai ramta wa Allah rance kyakkawa saboda haka ubangiji ya nunka masa sakamako ninke-ninke masu yawa ,wannan kira da Allah madaukakin sarki yayi ga bayinsa saboda ya kwadaitar da su aikata Alkheiri tare da irin falalar sakamakonsa a ranar hisabi,kuma irin wannan kyawawen dabi'u Allah ya tabbatar da su kan tafarkin waliyan bayinsa makusanta amincin Allah ya tabbata a gareisu.amma kafin mu fara karanto riwayoyin na mu nay au bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan inji.


 


A cikin littafin Biharu Anwar an nakalto riwaya daga littafi mai suna كتاب قضاء حقوق الإخوان na baban malamin hadisi Assury yardarm Allah ta tabbata a gareishi tare da sanadinsa daga Ishak bn Ibrahim bn Yakub yace :mun kasance a wajen Abi Abdallah sadi (a.s) da ni da Mu'ala bn Khanis sai ga wani bawan Allah daga cikin Mutanan Khurasan ya shigo yayi sallama aka amsamasa sai yace ya Dan Ma'aikin Allah ni ina daga cikin mabiyanku iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka sannan tsakanin Garinmu da inda kukai akwai tazara mai yawa gashi kuma guzirina ya kawo karshe ba zan iya komawa ba gurin iyalaina sai an taimaka mini.wanda ya rawaito wannan riwaya sai yace Imam Sadik (a.s) ya dubi damarsa da hakum sannan ya ce shin kun saurari abubuwan da Dan uwanku ya fada? Lalle kyautatawa itace wanda ka bada tun farko ba tare da an tanbayeka ba , amma abinda ka bayar bayan an tanbayeka  kyauta ce bayan Mutune ya zubar da mutuncin sa domin wanda bashi da shi zai kwana ne cikin dar dar tsakanin kauna da yankan kauna domin bai san inda zai meka bukatar sa ba , shin zai samu ko ba zai samu ba, haka zai tun kari wanda zai maika bukatarsa a wajensa cikin rawan jiki tare da zubar da mutuncinsa a gabansa ,bayan haka bai sani ba shin zai tafi da fakin cikin zubar da mutuncin sa ba ba tare da an biya masa bukatrsa ba ko kuma zai tafi cikin fara'a bayan an biya masa bukatar sa ,idan ka biya masa bukatarsa wato ka bashi abinda ya tambaya hakika ka kara dankon zumunci domin na ji ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa na cewa Na rance da wanda ya fitar da kwaya sannan ya aiko ni da Gaskiya Annabi duk wanda zai daure ya bijuro da bukatarsa a wajenka ladansa ya fi abinda zai samu daga gareka,wanda ya rawaito wannan riwaya sai yace sai aka hada wannan bawan Allah matafayi Dan Kasar Khurasan Dinare dubu 5 aka ba shi.


 


Masu saurare riwayarmu ta gaba tana magana ne kan sasanta bayin Allah idan suna cikin wani rikici domin shima na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci


Sikkatul Islman Kulaini ya rawaito hadisi cikin shahararren littafinsa mai suna Kafi tare da sanadinsa daga Dan Hanifa wanda yake jagora ne na baki a Garin Madina yace watarana ni da khansi muna rikici kan wani Gado sai ga Muffadal ya tsaya a kusanmu kimanin awa guda, bayan ya saurari rikicin da muke yi  sai ya bukace mu mu tafi Gidansa, a yayin da muka isa Gidansa sai ya sasanta mu tare da Dirhami dubu 4 wato ya bamu dirhami dubu hudu saboda ya kashe rikicin da muke yi ,bayan dukkaninmu mun dawo hayyacinmu sai muka gane cewa wannan dirhamin dubu hunu ba namu ba ne ba,sai muka ce masa wannan Dirhamin Dubu 4 ay ba namu ba ne ba ,sai Muffadal shima yace nima ba kudi na ba ne ba, wadannan kudaden Imam Sadik(a.s) ne domin shi ya umarce ni a duk lokacin da naga wasu Mutane biyu suna rikici a tsaknin su in sasanta su ko da yakance da kudadansa ne ,wannan kudi da na baku kudin Imam Sadik (a.s).


 


Masu saurare har ila yau muna bin tafarkin shugabanmu ne Imami na shidda daga cikin Imaman iyalan  Gidan Manzan Allah tsarkaka wato Imam Sadik (a.s)


An samo riwaya daga Sufyanu Sauri ya na cewa wata rana na shiga wajen Imam Sadik (a.s) sai nasa meshi fiskarsa ta canza ma'ana akwai alamar damuwa a gareishi sai na tambaye shi kan minene sanadiyar damuwarshi sai Imam(a.s) yace mani na hana su hawan Katanga amma basu hanu ba a yau na shigo gida sai na samu wata baiwa daga cikin bayina wadda itace mai renon Diyana tana bisa katanka dauke da daya daga cikin 'ya'yana , a yayin da ta ganni sai tsoro ya kamata ta fara rawar jiki har yaron yakubce daga hannunta ya fado sannan Allah ya amshi abinsa wato ya rasu ,Imam ya ci gaba da cewa Babar damuwata shine yadda na sanya tsaro a cikin zuyiyarsa ,ba mutuwar Yaron ba sannan daga karshe Imam Sadik (a.s)ya ce wa wannan baiwa ta tafi Ya 'yan tar da ita saboda Allah Madaukakin sarki kuma dangane da laifin da ta aikata yace ya yafe mata har so biyu.


 


Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka dibawa shirin  ya kawo karshe sai kuma a sati na gaba za ku jimu da ci gaban shirin idan Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada Shirin  a ka saurara ni da na jagoranci ni ke cewa wassalamu aleikum warahamtullahi wa barkatuhu.