Mahimancin Ikhlasi cikin Niya
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, Shirin na Yau zai bayyani,a shirin da ya gabata mun dauko bayyani kan mahimancin Ikhalsi cikin Niya, domin wannan dabi'a na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah madaukakin sarki ke so ga bayinsa,domin mahimancin wannan maudi'I, shirin na yau ma zai ci gaba da shi, amma kafin nan bari saurari wannan.
*********************Musuc****************************
Masu saurare,kamar yadda muka bayyana a shirin da ya gabata,ma'anar Ikhlasi cikin Niya shi ne duk aikin da Bawa zai yi don neman yardar Allah da kuma yin biyayya gare shi,kuma ta hakan Mutum zai samu tsira a Duniya da Lahira, a cikin Littafin Kafi na shekh Kulaini, an ruwaito Hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(ta hanyar Ikhlasi Bawa kan samun 'yantuwa daga kangi Duniya da Lahira) har ila yau cikin wani hadisi na daban, Imam (a.s) ya ce:(Albarka ta tabbata ga wanda ya yi ikhlasi cikin Ibada, da Addu'a, bai shagalta zuciyarsa da abinda idanuwansa suka gani ba, kuma bai manta da ambaton Allah ga abinda kunnayansa ke ji ba, zuciyarsa ba ta yi bakin ciki ga abinda aka ba waninta ba), Masu saurare, dabi'antuwa da dabi'ar Ikhlasi saboda Allah shi ke sanya aikin Mutum mafi kyakkyawan aiyuka.kamar yadda ya zo cikin Littafin cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi daga Imam Sadik (a.s) yayin da yake Tafsirin wannan Aya mai albarka(Wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku, (Ya ga) waye a cikinku ya fi kyakkyawan aiki.Shi kuma Mabuwayi ne Mai yawan gafara ne) suratu Mulki Aya ta 2.sai Imam (a.s) ya ce:(ba a na nufin yawan aiki ba, saidai abinda ake nufi mafi kyawan aiki, kuma mafi Kyawan aiki shi ne tsoron Allah, gaskiyar Niya da kuma khalisi ko kuma tsarkakekken aiki wanda Bawa zai yi, ba ya bukatar ko wani mahluki ya gode masa face Allah madaukakin sarki).daga cikin albarkar dake tattare da wannan dabi'a mai albarka duk wanda ya aikata wani aiki cikin ikhlasi komin kankantarsa za a sanya shi cikin Aljanna, a cikin Littafin Almahasin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Hakika Ubangijinku mai jin kai ne yana godewa kadan, idan Bawa ya sallaci raka'a biyu domin Nemam yardar Allah sai Allah ya sanya shi Aljanna, kuma Hakika idan Bawa ya yi sadaka da Dirhami guda domin Neman yardar Allah, sai Allah tabaraka wa ta'ala ya sanya shi Aljanna).har ila yau cikin wata riwaya ta daban , Imam (a.s) na cewa:(duk wanda yake neman yardar Allah da aiki kadan, Allah zai bayyana masa aikin sa , mafi girma ga abinda shi kansa yake nufi,kuma duk wanda yake neman Allah da aikinsa mai yawa cikin kajiyar da jikinsa ya kuma raya Dare matukar babu Ikhlasi a cikin sa Allah zai rage shi daga gani da kuma ji kamar yadda shi yake so a gani ko kuma yake so a fada). Masu saurare, har ila yau daga cikin girman albarkar dake tattare da dabi'ar Ikhlasi saboda Allah a aiki, cimmawa hikimar da a cikin ta a kwai alheri mai yawa, kuma ya samu rabauta a Duniya da Lahira, wannan shi ne abinda Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya yi ishara da shi cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Kafi, inda Imam (a.s) ya ce:(babu Bawan da zai tsarkaken imaninsa da Allah cikin Ikhlasi kwanaki 40,ko kuma cikin wata riwayar aka bayyana cewa Duk Bawan da ya kyautata ambaton Allah kwanaki 40, Allah madaukakin sarki zai sanya shi mai tsoron Allah a nan Duniya ya kuma fahimtar da shi tsutar ta da kuma maganin ta, Hikima kuma ta tabbatu cikin zuciyarsa ya kuma bayyanar da ita a harshensa watau a basa hikima da za ta gudana a harshensa) har ila yau cikin wani hadisi na daban an bayyana cewa dabi'antuwa da wannan dabi'a mai albarka ya kamata ta zamanto a dukkanin Al'amuran Mutum, a cikin Littafin Tuhuful-Ukul, an ruwaito hadisi daga Shugaban masu kadaita Allah, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(madalla ga wanda ya tsarkake ko kuma ya yi Ikhlasi na aikinsa, iliminsa, Soyayyarsa da kiyayarsa, daukansa da barinsa, maganarsa da shuru dinsa, aikinsa da fadar sa saboda Allah madaukakin sarki) har ila yau cikin wani Hadisi na daban Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya bayyana mana cewa dabi'antuwa da dabi'ar Ikhlasi mabudin rabauta ne da kuma samun taimakon Ubangiji a Duniya da Lahira, Imam (a.s) ya ce:(duk mai Ikhlasi don Allah, rayuwar sa za ta karfafa a Duniya a Lahira).
*********************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran, a ci gaban shirin zai bayyani kan dabi'ar kunyar Allah madaukakin sarki domin wannan ma'ana abin yabo ce, kamar yadda shehin malamin nan Sayyid Kutubu din Rawandi yardar Allah ta tabbata a gare shi cikin Littafin sa Dau'u Shihab ya ce:(Kunya ita ce rike kai daga aikata mumuna da kuma barinta aikata hakan, mafi yawan abinda dabi'ar kunya ke hanawa, aikata Zunubai da alfahasha), Masu cikin wani hadisi an bayyana cewa dabi'ar kunya na daga cikin mahiman batutuwan da suke sanya mai wannan dabi'a ya rabauta da Soyayyar Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Amaly na shekh Mufid, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Hakika Allah ya na son mai kunya kuma mai kamun kai, ya na kuma fishi da maras kunya mai yawan tambaya) domin haka ne ma Masu saurare a wasu riwayoyin na daban za mu ga cewa Ma'aikin Allah (s.a.w.a) yana yi mana wasici da dabi'ar kunya kuma yana bayyana mana misdakinta, a cikin Littafin Kurbul-isnad, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce: ( ku kasance masu jin kunyar Allah Hakikanin Kunya sai sahabai suka ce ya ya za mu yi Ya Ma'aikin Allah? Sai Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce idan ku kasance masu masu aikata wani aiki, kadda dayanku ya bayyana face ajalinsa a kan idanuwansa, ku kiyaye aikata zunubi,Kai da abinda yake aikatawa, Ciki da abinda yake ci da sha, kuma ku kasance masu tuna kabari da azabar dake cikinsa) har ila yau masu saurare, Kunyar Allah madaukakin sarki ita ce mafi karama na Adon Mutum, a cikin Littafin Amaly na shekh Tusy an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce (Alfahsha ba ta kasance wani Abu ga Mutum ba face dauda, kunya kuma ba ta kasance ga Mumuni ba face ado), har ila yau Masu saurare dabi'antuwa da kyakkyauwar dabi'ar Kunyar Allah madaukakin sarki tana hadawa Mutum dukkanin alheri, a cikin Littafin Ma'anin Akhbar, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na ce:(Kunya alheri gaba dayanta), har ila yau dabi'antuwa da dabi'ar kunya na daga cikin hanyoyin dake tabbatar da hakikanin Imani, Hakika Shekh Saduk, cikin Littafinsa Ma'anil Akhbar, ya ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na cewa:(Kunya da Imani na cikin karni guda duk lokacin da dayansu ya kushe dayan zai bi bayansa), har ila yau wani hadisin ya bayyana cewa dabi'ar ta Kunya na daga mafi fadadar kofofi zuwa shiga Aljanna, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru sadik (a.s) ya ce:(Kunya daga Imani ne, kuma Imani ne ke sanya Mutum Aljanna), hakika masu saurare wannan hadisi mai albarka yana karfafa Imanin Mutum ga Allah madaukakin sarki.
*********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.