Kyakkyawar Dabi'ar Kunya
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, Shirin na Yau zai bayyani,a shirin da ya gabata mun dauko bayyani kan mahimancin kyakkyawar dabi'ar Kunya musaman ma ga Allah madaukakin sarki, domin mahimancin wannan maudi'I shirin na yauda zai dora daga inda muka tsaya a shirin da ya gabata, amma kafin nan bari mu saurari wannan.
***********************Musuc****************************
Masu saurare, dabi'ar kunyar Allah madaukakin sarki na daga cikin kyawawen dabi'un da wasiyar Anabta ta yi kira a kan sa, shirin na yau zai fara da hadisin da Shekh Mufid ya ruwaito cikin Littafinsa Al-ikhtisas daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Allah ya jikan Bawan da ya ji kunyar Ubangijinsa hakikanin kunya, ya kiyaye Kansa da ya abinda ya gumshe shi, ya kuma kiyaye Cikinsa da kuma abinda yake ci da sha, ya ke kuma ambaton Kabari da azabar sa, ya kuma yi tunanin cewa Lahira ita ce makoma ).Masu saurare, abin fahimta a wannan hadisi mai albarka shi ne duk wanda ya yi kokari wajen dabi'antuwa da dabi'ar kunya daga Allah madaukakin sarki na farko shi ne rabauta da Addu'ar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da ta kasance karbarbiya ce da rahamar Ubangiji, na biyu kuma shi ne bayyanar dabi'antuwa da wannan dabi'a shi ne Mumuni ya kiyaye dukkanin gabobin jikinsa wajen sabon Allah madaukakin sarki tare da tabbatar da cewa dukkanin abinda ke yi Allah madaukakin sarki na ganin sa.a cikin Littafin Raudatul Wa'izin an ruwaito wani Hadisi inda a cikin sa aka ce wani Mutum ya Ji wajen Annabin Rahama yay a ce Ya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ka yi mini wasici sai ya ce:(ka ji kunyar Allah kamar yadda ka ke jin kunya Salihin Bawa daga cikin mutananka) Hakika Masu saurare Bawa ya ji cewa dukkanin abinda yake yi Allah madaukakin sarki na kallonsa , kuma na kusa da shi, domin shi Allah ya fi kusa da ko wani Bawansa daga bayinsa da jijiyar sa ta wuya, zai taimakawa Mutum wajen dabi'antuwa da wannan dabi'a, a cikin Littafin Durratul-bahira na Shahidunl-Awal yardar Allah ta tabbata a gare shi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Zainul-abidin (a.s) cikin daya daga cikin wasiyoyin sa na cewa:(Ka kaskantar da kanka ga kudurar Allah ta'ala kuma ku ji kunyar sa madaukakin sarki saboda kusancin ka da shi). Masu saurare, daga cikin albarkar dake tattare da dabi'ar kunyar Allah, shi ne kasancewarsa hanya ta canza mumuna zuwa kyakkyawa domin hakan ya kansa mutum ya bar aikata sabo ya koma zuwa aikata aiyukan alheri da kuma biyayya ga Ubangijinsa. A cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Manzan Allah (s.a.w.a) ya ce:(abu hudu duk wanda ya kasance cikin su ko da kuwa zunubansa sun kasance daga wuyansa zuwa digadigansa Allah madaukakin sarki zai canza su zuwa kyawawa, Gaskiya, Kunya, kyawawen dabi'u da kuma godiya), Masu saurare a bangare guda rashin dabi'antuwa da dabi'ar kunyar Allah yak an jefa Mutun aikata sabo, munanan aiyuka gami da zunubai. Hakika cikin Littafin Amaly na shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa (babu abinda ya rage daga misalan Annabawa face kaulin Mutane: idan ba jin kunya to ka aikata abinda kaka dama).a cikin Littafin Ma'anil-Akhbar an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) wanda yake ishara kan mumunar makoma ga wanda ya juya baya ga dabi'ar kunya watau ga wand aba shi da kunya ko kadan, Manzob Allah (s.a.w.a) ya ce:(idan Bawa ya kasance maras kunya farkon abinda Allah madaukakin sarki zai zare masa shi ne Amana sannan kuma ya zare masa jin kai, sannan kuma ya tubu mesa rikar Addinin musulnci daga wuyansa sai ya kasance Shaidani la'ancecce).
************************Musuc************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye da sashen hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran, ci gaba shirin zai fara da Littafin Tuhuful Ukul inda a cikin sa aka ruwaito wani dogon hadisi da a cikin sa Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya amsa tambayoyin wani Malamin Kirista da ya sanya gamsuwar sa har ma ya yi imani da shi ya kuma musulinta, daga cikin amsar tambayoyin da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya bashi yay i ishara da cewa hakika Hankali na daga cikin mafi so daga cikin halitun Allah, inda ya ce:( sai ya wanzu daga Hankali , Hakuri, daga Hakuri kuma Ilimi, daga Ilimi kuma gaskiya, daga gaskiya kuma Kamewa, daga Kamewa tsoron Allah, daga tsoron Allah kuma Kunya, daga kunya kuma samun Nutsuwa,daga kuma samun Nutsuwa shi ne Dawwama a kan aikin Alheri, daga Dawwama kan aikin alheri shine kin aikin Sharri, daga kuma kin aikin Sharri, yin biyayya ga mai yin gargadi, wadannan Siffofi guda goma na daga Nau'o'I guda goma na alheri, kuma ko wani daga cikin wadannan siffofi guda goma su nada Nau'I guda goma) Masu saurare bayan wannan bayyani sai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyakan gidansa ya ci gaba da bayyana albarkar dake tattare da dabi'ar Kunyar Ubangiji a nan Duniya da Lahira yana mai cewa:(Amma Kunya yana wanzuwa daga gareta Magana mai taushi da kuma tausayi,murakaba ko kuma sanya ido cikin aiyukansa saboda da Allah cikin Sirri ko a bayyane, Amintuwa da kuma kauracewa aikata Sharri, fara'a da kuma hakikanin Nasara, da kuma kyakkyawan fata ga waninsa, wannan shi ne abinda hankali ke cimma ta hanyar Kunya, madalla ga wanda yay a ji tsoron Azabar Allah kafin ya ji nasihar Allah).masu saurare, har ila yau muna cikin wannan Hadisi na Ma'aikin Allah (s.a.w.a) inda a cikin sa aka yi mana bushara da cewa dabi'ar kunya ita ce sanadi na wanzuwar kyawawen dabi'u da dama, kamar yadda kuma ya kasance wata alama ce ta cewa mai wannan Dabi'a zai lazamci aiki da hukunce-hukuncen tsarkakekken hankali, a ci gaban wannan hadisi, Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(tsarkakekken hankali Allah ta'ala yana ilhaminsa ga masu rabu yana kuma haramtawa shakiyai,kuma siffar mai hankali shi ne yin hankuli ga abinda ya jahilta, ya kuma kauda kai ga wanda ya zalince sa, ya kuma yi tawaru'u ga wanda yake kalkashinsa, ya yi musabaka ga wanda yake samansa wajen bauta da neman biyayyar Ubangiji,kuma idan ya bukaci yin Magana sai yayi Nazari, idan ta kasance a kwai alheri cikin ta sai ya fada domin ya rabauta,idan kuma ya fahimci za ta iya janyo wani sharri ko matsala, sai ya kame bakin sa daga fadarta, har ila yau Masu Saurare Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ci gaba da cewa idan wata Fitina ta tunkare shi sai ya nemi tsari ga Allah ya kuma kame fakinsa da hannayansa, idan kuma ya ga wata falala sai ya tarbeta a hanu biyu ya kuma kiyayeta, ba ya rabuwa da kunya, ba ya kuma nuna damuwa ga Al'amura, wadannan su ne siffofi goma da ake gane mai hankali da su) da fatan Allah madaukakin sarki ya arzuta mu da wannan kyakkyawar dabi'a don albarkar riko da tafarkin iyala gidan Ma'aikin Allah tsarkaka.
*****************************Musuc**************************
Masu saurare, a nan za mu dasa Aya , ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da ci gaban shirin, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala musaman ma Aminu Ibrahim Kiyawa ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamullahi ta'ala wa barkatuhu.