Jan 28, 2017 05:03 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirye shiryen da suka gabata mu yi bayyani kan kyakkyawar dabi'ar kunya kuma da hanyar wannan dabi'a ce Allah madaukakin  sarki ke kare Mutum daga  fadawa cikin sabon sa, Shirin na Yau ma zai ci gaba da dabi'ar kunyar  musaman ma wajen mu'amala da Mutane, kafin shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

****************************Musuc***********************

Masu saurare, Shirin zai fara da hadisin Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) inda ya siffanta  wannan dabi'a da hasken Imani, Hakika cikin Littafin Uyunul-Akhbar, an ruwaito hadisi daga Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:( Imani itaciya ce tushensa shi ne Yakini ko kuma mu ce tabbaci, reshen sa kuma tsoron Allah, hasken sa kuma shi ne  Kunya, 'ya'yan ta kuma su ne karamci). Hakika dabi'ar kunya wajen mu'amala da Mutane na daga cikin hanyoyin da suke kare  soyayya da kyakkyawar alaka a tsakanin Al'umma da zamantakewa, A cikin Littafin Tuhuful-Ukul cikin wasiyoyin da Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya yiwa Sahabansa ya ce:(kadda ka kawar da kunya dake tsakaninka da Dan uwanka, ka kara karfafa ta domin kawar da kunya na a matsayin kawar da soyayya, kuma karfafa ta shi ne karfafa soyayyar dake tsakanin ku). Masu Saurare, Hakika Masoyin Allah kuma mai shiryarwa zababben shi  amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu cewa dabi'antuwa da dabi'ar kunya ya na taimakawa Mutum wajen dabi'antuwa da kyawawen dabi'u masu girma. A cikin Littafin Raudatu wa'izin an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(Kunya ba ta kasance ga wani abu face ado, Alfahasha kuma ba ta kasance ga wani abu face muni, Hakika Ko wani Addini ya nada halitta, halittar musulinci kuma tufafinsa shi ne Kunya).Babban malamin nan Shekh Ridha cikin Littafin Majazatu-Nabawiya المجازات النبويه ya nakalto Kaulin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na cewa:(Kunya ita ce tsarin Imani) kalkashin wannan hadisin shekhin Malamin ya yi ta'aliki  dangane da wannan Isti'ara da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) cikin wannan hadisi da ya gabata ya na nufin dukkanin imani da ban gaskiya domin Mutum mai yawan kunya, kunyar tasa ta kan hana shi abkawa cikin sabo , idan kuma kunyarsa ta rage Imanin sa sai waste).har ila yau Masu saurare wasu Nassosi na daban sun bayyana mana  cewa dabi'antuwa da dabi'ar kunya shi ne suturta aiyukan Mutane  da hakan zai kasance taimako ne gare shi wajen tsarkaka, a cikin Littafin Man La Yahduruhul-Fakih , Shekh Saduk ya ruwaito Hadisi daga Shugaban masu kunya da Imani Mustapha tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka zuwa ga wasiyinsa Imam Ali(a.s) ya ce:( Ya Ali Suturar musulinci shi ne kunya, adonsa kuma shi ne cikka alwari, mutuncinsa kuma shine kyawawen aiyuka, gimshikinsa kuma shi ne tsoron Allah, kuma ko wani abu ya nada tushe, tushen musulinci kuma shi ne soyayyarmu Ahlulbait).a wani hadisin na daban kuma an bayyana cewa rashin dabi'antuwa da kyakkyawar dabi'ar kunya yana yin sanadiyar bayyanar aibin Mutum da kuma karuwar aikata sabo gami da yaye hijabin Imami daga gare shi, a cikin Litattafan Tuhuful-Ukul da Al-Ikhtisas na shekh Mufid, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na cewa:(duk wanda ya yi jifa da suturar kunya ba shi da wani abu na boyewa).

**************************Musuc*******************************

Masu Saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,Hakika cikin Littafin Uyunul-Hikam wal-mawa'iz, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu, Shugaban Masu kadaita Allah, Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(karshen Kunya, Mumuni ya ji kunyar kansa, ka kautata kunya kuma ka fara kyautata daga kan ka, hakika kuma Kunya da kamewa na daga cikin abinda ke aifar da imanin Bawa, hakika kunya dabi'un 'yantattu ne, kuma tafarkin masu biyayya) Masu saurare Kunya , imma ta kasance ta Allah sai Bawa ya kauracewa abinda Allah yake ki, ko kuma kuyar Mutane wajen kauracewa abinba suka ganinsa maras kyau, ko kuma kunyar kai ta hanyar kauracewa abinda zai sanya Mutum ya ji kunya idan ya aikata abu, dukkanin wadannan nau'I na kunya na daga cikin kyawawen dabi'u masu girma, kuma suna samarwa mumuni mahimanci da mafi yawan Albarka, wannan shi ne abinda Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya shiryar da mu cikin Hadisin da aka ruwaito a  Littafin Kafi na Sikkatu Islam Kulaini, Imam (a.s) ya ce:(Kyawawen aiyuka guda goma, idan zaka iya su kasance gare ka to su kasance domin su ,suna iya kasance ga Mutum, ba su kasance ga Dansa ba, watau saboda ana samun su ne ta hanyar kokari ba wai ta hanyar gado, suna kasance ga Da, ba su kasance ga ma'aifinsa ba,su kuma kasance ga Bawa ba su kasance ga Ubangidansa ba, sai aka ce Ya Dan Ma'aikin Allah wasu  kyawawen dabi'u wadannan? Sai Imam (a.s) ya ce: gaskanta rashin damuwa watau kauracewa kodayin abinda ke hanun Mutane, gaskiyar harshe, watau gaskiyar Magana, cika Amana, sada zumunci, girmama Bako,ciyar da matambayi watau mai bara, sakawa ma'aikata watau biyansu a kan lokaci da kuma kyakkyawan biya,kiyaye hakin makobci da kuma kiyaye hakin aboki, watau ya kasance mai basu kariya cikin kyautatawa kuma dukkanin wadannan dabi'u shugaban su shi ne kunya).Masu Saurare dabi'antuwa da dabi'ar Kunya da dukkanin misdakinta da ya gabata shine amsa kirar Alkur'ani mai tsarki ta hanyar koyi da sahibin mai dabi'u masu girma da kuma koyi da dukkanin kyakkyawa na Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, Hakika Kunya ta kasance dabi'arsa, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru sadik (a.s) cikin wata Khuduba mai tsaho da ya yi inda a cikin ta ya ambato halayen Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka, daga cikin bayanin da ya yi yana mai cewa (duk da irin girman sabon su da munanan aiyukan su (watau Larabawa) saboda Hakurinsa tausayi da rahamarsa ,hakan ba hana Ubangijinmu ba  tayar da fiyeyyen halitta da kuma mafi so da kauna daga cikin Annabawansa da kuma mafi karamci Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka zuwa gare su ba, saboda kyawawen dabi'un sa kunya ba ta taba rabuwa da shi ba, kuma halayensa shi ne karamci……..) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yin biyayya da fiyayyen halinttu da kuma koyi da dabi'unsa dan albarkar riko da wulayar iyalan gidansa tsarkaka.

*************************Musuc******************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.