zababun Aiyuka-kyawawen halaye
shirin zai dubi ne kan wasu riwayoyi na iyalan gidan manzon Rahama tsarkaka da suke bayyani kan kyawawen halaye
Masu saurare Assalamu Aleikum Barka da sake saduwa da ku a cikin shirin kyawawen Dabi'un musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi.shirin na mu na yau zai yi dubu ne kan wasu riyayoyi daga tafarkin shugabaninnu shugabanin shiriya iyalan gidan Manzan Rahama tsarkaka guda biyu,Imam Ali Alhadi (a.s) da kuma Imam Sadik (a.s) inda wadannan riwayoyi za su yi magana kan wasu daga cikin kyawawen Dabi'un musulnci kamar sakamako da abin yafi kyau da kuma kyakyawar Nasiha ga bayin Allah amma kafin nan bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan inji.
Masu saurare riwayarmu na farko , mafi yawan littatafai wannan lokacin masu inganci sun nakalto wannan riwaya, haka zalika baban marja'in iddinin musulinci nan Ayatull…wahid khurasani ya nakalto ta a cikin Farkon littafinsa na Risalul Amaliya mai suna Minhaju Salihin, ita dai wannan riwaya an samota ne daga mai gadin Muttawaki , shidai wannan Maigadi ya kasance yana aiki ne a fadar milki na khalifan Abbasiya wato Mutawakkil, wannan bawan Allah wanda aikinsa shine buda kofa a fadar milki Mutawakil sunansa Zurafa ya ce wata rana Mutawakil ya bukaci Aliyu bn Muhamad bn Rida (a.s) ya fito a wata Rana wadda ake kiranta Ranar Aminci wato Yaumul Salam,Yaumul Salam Rana ce wadda ake kai gaisuwa ga Khalifofin Abbassiyawa ko kuma rana ce ta tunawa da khalifancin Abbasiyawa, a wannan rana dukkanin mabiya khalifancin Abbasiyawa suna fitowa suna zuwa fada su meika gaisuwarsu ga khalifa sannan ana fita daga cikin gari zuwa wajen gari wanda khalifan ya ayyana, Mutawakkil yayi haka ne na nifin tsutar da Imam Ali Alhadi(a.s)sai wazirinsa ya ce masa karda kayi haka domin yin haka ba kau, sannan zai bata maka suna , sai Mutawakil yace dole ne sai na aikata hakan zuciya zata yi sanyi domin na yi niya, sai wazirin nasa yace to tunda haka ne ka bari har sai dukkanin shugabanin kabilu da masu fada aji sun ci gaba, in yaso kaima sai ka fito saboda kadda Al'umma su gane ka yi haka ne da niyar cutar da Imama Hadi(a.s) shi kadai.sai Mutawakil ya amince da shawarar da wazirinsa ya bashi.
Daga nashi waje Imam Hadi (a.s)ya fito yana tafiya har sai da yakai wani guri mai suna Dehliz zufa na zuba daga fuskarsa domin lokacin zafi ne , Zurafa mai gadin Mutawakin yace sai na hadu da Imam Hadi (a.s), da ka gansa akwai alamar gajiya a gunsa , na zaunar dashi sannan na shafe masa zufar dake zuba daga fiskarsa sannan nace masa wallahi Dan kawunka yayi haka ne kawai na niyar tsutar da kai, tsewar Imam dan kawun Muttawakili ne saboda silsilar Mutawakin tana koma ne ga Abbas Dan kawun Manzan Rahama shi kuma Imam jikan Manzan Rahama saboda haka aka kira Mutawakil Dan Kawun Imam Hadi (a.s), sai Zurafa ya ci gaba da cewa ya Imam kadda ka rike Dan uwanka a zuciya sai Imam (a.s) yace ya kai Zurafat ku ji dadi kwanaki uku a gidanjenku wannan wa'adi wanda babu karya a cikinsa.sai Zurafat yace: na kasance inada malami Dan Shi'a sannan na kasance ina yawan yi masa wasa ina kiransa da Rafidi sai mu hadu a gida na bayan sallar isha lokacin nan na bashi labarin abinda Imam Hadi (a.s)ya gaya mini sai yace mini shin da gaske kake ka ji wannan daga Imam Hadi (a.s)?sai nace masa babu shakka haka naji daga bakin Imaminku .sai yace ma ni wajibi ne a kanya in kaya maka Gasakiya ga wata Nasiha da zan baka idan har wannan magana da ka fada ka ji ta daga Bakin Imam (a.s) ka kwashe duk abinda ka mallaka daga Gidan Milki na Muttawakil domin bayan kwanaki 3 Mutawakil zai Mutu ko kuma a kashe shi, sai na ji haushi gami da wannan magana har ma na farfadi maganganu, sannan na koreshi daga Gida na sai ya ta fiyarshi, bayan na kasance ni kadai na yi tunani, nace ai bai kamata ba inyi fishi ,idan abinda ya fada min ya kasance Gaskiya to kaka bani da watta hujja kuma idan abinda ya gaya min ba gaskiya bane ba sai in meda kayana babu wanda ya san abinda ake ciki, sai na tafi fadar milki ta Muttawakil na fitar da dukkanin kayyayakin da na mallaka a gidansa na kaisu wajejen 'yan uwa wadanda na yarda das u suka ajje min ban bar komai ba sai tabarmar da nike konci,bayan kwanaki 3 wato a dare na 3 wayewar na 4 sai aka kashe Muttawakil , na tsira ni da dukiya ta ,bayan haka sai na zama Dan Shi'a na kasance tare da Imam Hadi(a.s) na zamnto daga cikin masu yimasa Hidma sannan na roke shi yayi mani Addu'a inza manto daga cikin mafiyan na Gaskiya masu riko da Wilayar Ahlulbait (a.s).
daga kasan wannan riwaya Ayyatull…Khurasani ya bayyana cewa sannanan abu duk abinda wannan Bawan Allah ya samu na aminci Duniya da Lahira sanadiyar Albarkar hidmar da ya yiwa Imam (a.s) na shafe masa zufar fuskarsa ce.
Masu saurare riwayarmu ta gaba tana magana ne kan tafarkin shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik(a.s) inda take ishara kan wasu kyawawen Dabi'u guda 2 na farko kauta da kuma kyakyawar Nasiha.
Sheik Keshi ya rawaito riwaya a cikin littafinsa mai suna Kitabul rijal daga Mufadal bn Kais na cewa na shiga wajen Abi Abdullah Imam Ja'afaru Sadik (a.s) sai na meka kukana dangane da wasu Matsaloli na bukace shi yayi mani Addu'a sai ya umarci bawarsa ta kawo jikar da Abu Ja'afar da kawo masu .sai yace mani ga ka dauki wanna jikka akwai Dinare 40 kaje ka biya bukatunka da su.sai na ce masa ya Dan Ma'aikin Allah ba wannan ya kawoni ban a zone don neman Addu'arku Sai Imam (a.s) yace masa na sani amma ka dauki wannan sannan karda ka gayama Mutane halin dake ciki kai dai tayi masu Alkheiri.
Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka dibawa shirin ya kawo karshe sai kuma a sati na gaba za ku jimu da ci gaban shirin idan Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada Shirin a ka saurara ni da na jagoranci ni ke cewa wassalamu aleikum warahamtullahi wa barkatuhu.