Mar 04, 2016 13:50 UTC
  • zababun Aiyuka-Tafarkin shugaban wasiyai

shirin zaiyi dubi ne kan tafarkin shugaban wasiyai na Manzan Allah wato Imam Ali(a.s)


Masu saurare Assalamu aleikun barka da sake saduwa da ku a shirin kyawawen Dabi'un Musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, ,shirin namu na yau zaiyi dubi ne kan tafarkin shugaban wasiyai na Manzan Allah wato Imam Ali(a.s)musaman ma kan irin abubuwan da suka faru tsakaninsa da Ma'awyia a yakin Siffin kamar yadda Maluman Tarihi na mazhabobi daban daban suka ruwaito, amma kafin mu shiga cikin shirin  bari mu saurari abinda aka mana tandi a kan inji.


 


Maliman tarihi da dama sun rawaito abubuwa daban daban wadanda  suka wakana tsakanin Imam Ali(a.s) da Mu'ayuwa a yakin Sufain ,a cikin riwayar da suka ruwaito sun bayyana cewa Hakika rundunar Mu'awiya ta rika rundunar Imam Ali(a.s) isa yankin Sifain ,a lokacin da rundunar Mu'awiya ta isa wannan yanki na Sufai sai Mu'awiya ya baiwa rundunarsa umarni su rufe duk wata hanya ta isa wajen koki na ruwa wanda ake kiransa da Ma'ul furat saboda ya hada rundunar Imam Ali(a.s) shan wannan ruwa da nifin mabiya Imam Ali (a.s)su muto a sanadiyar  ishirwa , bayan isarwar Rundunar Imam Ali (a.s) anyi ta muhawara kan cewa Mu'awiya ya bude wata hanya da rundunar Imam Ali(a.s) za su samu suma suyi amfani da runar na furat.sai dai Mu'awiya ya dage a kan cewa ba zai bar su ba, a wannan lokaci  ganin cewa babu wata mafuta sai rundunar Imam Ali (a.s) ta kai farmaki kan rundunar Ma'awiya sannan ta samu nasarar 'yantar da wannan kokin ruwan  na furat, saidai bayan da rundunar Imam Ali (a.s) ta kame hanyoyin zuwa isa ga -ruwan na furat , imam Ali (a.s) ya umarci rundunarsa ta buda wasu hanyoyi wadda rundunar Ma'awiya suma zasu samu su yi amfani da wannan ruwa , wanda ya rawaito wannan riwaya yace a yayin da rundunar Ma'awiya suka hana rundunar Imam Ali (a.s) amfani da ruwan furat ,Sayyidina Ali (a.s)ya kira Sa'asa'atu bn suhan inda ya aikeshi wajen Ma'awiya yace kaje wajen Ma'awiya kace masa Masa wannan mataki da ya dauka na hana mabiyanmu amfani da ruwan furat ba zai masa kau ba, sannan ni ba na son in ya kesu bare da nayi masa kashe ba, har ila yau ka gaya masa cewa hakika ya fara kai hari amma ba mu maida murtani ba domin ba ma so mu yaki shi har sai idan yaki a sasanta ,idan kuma yana bukatar a fafata duk wanda ya samu nasara shi zai yi amfani da ruwan na furat to babu laifi,a yayi da aka shaida ma Mu'awiya sakon Imam Ali(a.s) sai yace kar Allah ya shayar da ni kuma kar Allah ya shayar da zuriyar Aba sufiyar idan har na bari suka sha wannan ruwa sai sun Mutu gaba daya saboda ishirwa. Haka zalika rundunar Imam Ali (a.s) ta kasance ba tare da ta sha wannan  ruwa ba  har saida ta yi kwana guda da yini guda.


 


Imam Ali (a.s) ya hada sahaban sa gaba daya sannan yayi masu jawabi kamar haka. Bayan yayi Bismillah ,yayi Annabi Salati sannan ya ce kusairara Hakika wadancen Mutanan sun fara Zalintarku,sun tarbeku da mumunar kiyayya,sun gayyacesu zuya majalisin yaki yayin da suka hanaku amfani da ruwa,sun bukaci a shayar da takoba jini yayin da suka haramta maku amfani da ruwa sha,Mutuwa cikin Rayuwarku Jarimci ne haka zalika idan kuka samu nasara za ku rayu cikin jarimta.ku sani cewa Mutanan da Mu'awuya ke jagoranta  Mutane ne masu bin san ranso da masu biyayya da cikunansu don yakarku saboda wata manufa ta daban.


 


Masu saurare wanda ya rawaito wannan riwaya daga cikin Rundunar Imam Ali(a.s)kamar yadda Nasr bn Muzahim ya rawaito cikin littafinsa mai suna Waki'atu Sifain ,bayan wannan Jawabi yace  sai Muka tunkari rundunar Mu'awuya har saida Kokin Furat ya dawo hannun mu , sai muka ce muma ba za mu shayar da su ba wato bayan da mabiya Imam Ali (a.s) suka amshe kokin furat daga hannun rundunar Mu'awiya sai suka firta cewa ba za su shayar da rundunar Ma'awiya ruwa ba kamar yadda suka hanasu shan wannan riwa a tsahon kwana guda da yuni guda ba, sai Imam Ali (a.s) ya aika da cewa su debi dai dai bukatarsu sannan suko ma sansaninsu na Yaki domin Allah madaukakin sarki ya basu Nasara kan irin Zalinci da aka yi masu.


A cikin wata riwayar kuma an bayyana cewa yayin da Mutanan Sham wato mabiya Mu'awiya suka killice kokin Furat sun ji dadi sosai kan Nasarar da suka samu , sannan Mu'awiya ya gabatar da jawabi ga mabiya bayansa inda yake yace Yaku Mutanan Sham wannan itace Nasara ta farko da muka samu sannan kadda Allah ya shayar da ni ko kuma zuriyar Aba Sufyan Idan har na bar dakarun Imam Ali(a.s) suka yi amfani da wannan ruwa har sai ishirwa ta kashe su gaba dayansu .sannan  kuma Al'ummar Sham ta gudanar da baban biki kan wannan Nasara da ta samu.sai wani Mutune daga cikin Garin Sham  ana ce masa Mu'ary bn Akbal ya tashi yace ma Mu'awiya  subhanallah da ya kasance kune kuka gabaci Al'ummar Kufa isa wajen wannan koki na furat sannan zaku hana masu shan wannan ruwa.amma na rance da Allah da sune suka gabace ku isa wannan guri da sun barku kun shan wannan ruwa.shin ba ka gani baban laifi ne ku hana Mutanan da ku ka gabata amfani da ruwa ?:alhali a cikinsu a kwai bayi da masu rauni da ma wadanda ba su da wani laifi?wallahi wannan baban jahilci ne, sai Mu'awiya ya kyari wannan bawan Allah ,wanda ya rawaito wannan riwaya yace wannan bawan Allah dan asalin garin Hamdan ya sulale daga rundunar Mu'awiya  ya bi duhun Dare ya koma bangaren rundunar Imam Ali(a.s).


 


Masu saurare a karshen wannan Riwaya Nasir yana cewa bayan da Iman Ali (a.s) da amshe kokin Furat daga hannun Rundunar Mu'awiya sai Sahabansa suka ce masa Ya Amiril mummunin  ka hanu  su amfani da wannan ruwa kamar yadda suka hana mu ,kadda ka shayar da su ko da digo guda ne ,ka kashe su da makamin ishurwa  idan kayi haka to ba mu bukatar yaki da takoba sai  u muto dukkaninsu saboda tsananin Ishurwa.Sai Imam Ali (a.s) A'A wallahi ba zan saka masu ba da irin aikin su ,ku bude masu hanyoyin amfani da wannan koki.ba ma bukatar yin hakan domin Kafin Takobi'unmu ya wadatar da mu wajen aikata hakan.


 


Masu saurare daga cikin Dabi'un Imam Ali (a.s) kan makiynsa Nasr Bn Muzahim ya rawaito riyawa cikin littafinsa Waki'atu Safain Ibn As yace ma Mu'awiya yaya ka ke gani idan Iman Ali(a.s) ya hanaku amfani da ruwan Furat kamar yadda kuka hanasu a jiya?shin zaka ya keshi ka amshe wannan Koki kamar yadda ya amshe daga hannunka jiya?sai Mu'awiya yace:kabar tada abinda ya fice, minene zatonta dangane da Ali ?sai Ibn As Yace hakika ba zai hanu ba amfani da wannan ruwa kamar yadda kuka hana shi.


 


Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka dibawa shirin  ya kawo karshe sai kuma a sati na gaba za ku jimu da ci gaban shirin idan Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada Shirin  a ka saurara ni da na jagoranci ni ke cewa wassalamu aleikum warahamtullahi wa barkatuhu.