Mar 04, 2016 13:56 UTC
  • zababun Aiyuka-Tafarkin shugaban wasiyai 2

shirin zai dubi ne kan tafarkin shugabanmu Aliyu bn Abi Talib (a.s) kan yadda ya dabi'antu da kyawawen dabi'u na Adalci


Masu saurare Assalamu Aleikum barka da sake saduwa da ku a cikin shirin kyawawen Dabi'un Musulinmu wanda ni Aminu Abdu ke gabatar dashi shirin na mu na yau zai yi dubu ne kan tafarkin shugabanmu Amirul mummunin Imam Ali (a.s)dangane da yadda ya tabbatu da kyawawen dabi'un Allah madaukakin sarki na tabbatar da adalci wajen baiwa dukkanin mai hakki hakinsa, mai rauni ko mai karfi. Amma kafin nan bari mu saurari abinda akayi mana tanadi a kan inji.


 


Riwayarmu ta farko za tayi ishara ne kan mumunan aiki da Halid bn walid ya aikata kan Al'ummar Bani Juzaima bayan da Manzon Allah ya tura shi wannan yanki.mun zabo riwayar ne a cikin littafin Al'amli da Ilalul Shara'I'I na baban Malamin nan Sheik Saduk a sanadinsa daga shugabanmu Abi Ja;afar Imam Bakir (a.s) yana ce wa: Manzon Allah (a.s.w.s)ya tura Halid bn Walid zuwa wani yanki mai suna Bani Mustalaq , wannan yanki Kabilar Bani Juzaima ce ke rayuwa a cikinta, ya kasance tsakanin kabilar Halid bn walid(wato Bani Mahzoum) da kabilar bani Juzaima akwai kiyayya a lokaci Jahiliya wato kafin shigowar musulinci.yayin da isa wannan anguwa sai ya tarda wannan kabila tuni  sun amsa kiran Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka.da lokacin salla yayi sai yasa Ladani yayi kiran salla suka yi salla tare da shi,a washa gari lokacin sallar Assuba ya umarci ladan ya kira salla sannan su kayi sallar Assuba tare da shi. Bayan sallar Assuba sai Halid bn Walid ya darma damarar yaki ya yaki wannan Kabila ta bani Huzaima ya kashe wanda ya kashe sannan ya raunata wanda ya raunata. Bayan haka sai wannan kabila ta amshe takardar dake nuna cewa  ta amsa kiran Manzon Rahama sannan  suke je da ita wajen Ma'aikin (s.a.w.a) sai suka bashi Labarin abinda Halid Bn Walid ya aikata, daga jin wannan mumunan abu sai Manzan Allah (s.a.w.s) ya maida gabansa ga Alkibila sannan Yace Ya Ubangijina na baranta ga abinda Halid bn walid ya aikata.


Aka ce sannan sai aka kawo ma Manzaan Allah Ganima daga baitul mal na Musulmi kamar su Zinari da makamantansu.sai Manzan Allah yace ma Ali bn Abi Talib (a.s) Ya Ali kaje waje Bani Juzaima na Bani Mustalaq, ka amintar da  su cewa na barnatu daga aikin halid bn walid sannan sai Manzan Allah (s.a.w.s) ya daga kafarsa mai albarka yace Ya Ali ka sanya duk wani hukunci jahiliya kalkashin diga digunka.


Masu saurare a karshen wannan riwaya da Imam Bakir (a.s) ya ce:Imam Ali (a.s)ya amsa umarnin Manzan Rahama(s.a.w.s) ya je ga kabilal Bani juzaima sannan yayi hukumci a karesu da hukunce-hukuncen ubangiji.bayan ya koma wajen Manzan Allah sai Annabi (s.a.w.s) ya ce masa Ya Ali bani labarin abinda ka aikata?sai Yace Ya Ma'aikin Allah yayin da na isa bayan na tabbatar da abinda ya faru na baiwa ko wani jini diya wato duk wanda aka kashe an ba magadansa diya, sannan na baiwa Dan tahi rabin diya wata Matar da aka kashe idan tana da ciki an baiwa magadanta diya da rabin diya,sannan duk wanda aka bata masa dukiyarsa an mayar masa da makamnciyar dukiyarsa,sai Imam Ali (a.s) yace manzan Allah daga cikin dukiya na basu kwauta ka duk wadanda aka bata ma bahohin Dabobinsu,da kuma sanya tsoro da akayi cikin cukatan Matansu da Yaransu sannan kuma na baiwa wadanda suka sani da wadanda basu sani ba. Har ila yau na raba masu Dukiyata don su yarda da kai ya ma'aikin Allah sai Manzan Allah yace ka basu domin su yarda dani ? Allah ya yarda da ya Ali.kai daga ni ne kuma matsayinka a wajena kamar matsayin Haruna ne a wajen Musa sai dai babu annabi baya na. Haruna ya kasance khalifan Annabi Musa (a.s) sannan bayan Annabi Musa (a.s) Haruna ya zama Annabi amincin Allah ya tabbata a gareisu.


 


Masu saurare riwayarmu ta biyu litattafan Tarihi da dama sun rawaito wannan riwaya amma muku ma mun dauko ta ne daga cikin littafin Algarat na Ibn A'asam Alkufi daga Mukhtar Tammar shima daga Abi Matar Albasry yace:wata rana Amiril mummunin Ali bn Abi Talib ya na ficewa daga wajen masu saida Dabino sai yaga wata Baiwa tana kuka sai ya tambayeta yace mata yakai wannan baiwar Allah minene ya sanya kike kuka? Sai ta ce mai gidane ya aikoni in siya mashi Dabino  sai na siya a wajen wannan mai saida dabinon ,lokacin da na kai masa sai yaki amincewa da shi wato mai gidan nata bai amince da wannan Dabinon ba da wannan baiwar ta siyo sannan ya umarce ta da ta mayar da shi sai wannan baiwa ta ci gaba da cewa yayin da na maido masa ya bani kudi na shima sai yaki amincewa.sai Imam Ali(a.s)yace mai saida Dabino ya kai Bawan Allah wannan mai aiki ce kawai bata da wani iko kan wannan dukiya don haka ka mayar mata da kudinta ka amshi Dabinonka sai wannan Mutuman mai Dabino ya meke tsaye ya mari Imam Ali (a.s) sai Mutane suka yi ca a kansa suka ce masa kai tsonka ko ka san wanda ka mara ? wannan Amiril mummunin ne .sai tsoro ya kama shi ,fuskarsa ta canza ya amshi Dabinansa cikin gaggawa sannan ya mayar ma wannan baiwar Allah kudinta sai Ya Amira mummunin ka ya feini sai Imam Ali(a.s) yace masa abinda zai sa in yafe maka idan ka gyara halayanka wato zai yafe masa amma da sharadin ya gyara halayansa.


 


 


Masu saurare anan za mu dasa aya saboda lokaci na hararrenmu   sai kuma a sati na gaba za ku jimu da wani sabon shiri shirin idan Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada Shirin  a ka saurara ni da na jagoranci ni ke cewa wassalamu aleikum warahamtullahi wa barkatuhu.