zababun Aiyuka-Tafarkin shugabanin shiriya
shirin zai yi dubi ne kan tafarkin shugabanin shiriya iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Masu saurare Assalama Aleikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin kyawawen Dabi'un Musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi .shirin na mu na Yau ci gaba ne a shirin da ya gabata kan tafarkin shugaban Mummunai Imam Ali (a.s) saidai a yau bayan irin wasiku da wasiyoyi da Imam (a.s) ke aikewa wakilansa a Gariruwa daban daban muna dauke da wasu hadisai kan tafarkin jikokinsa tsarkaka guda biyu wato Imam Ja'afar bn Muhamad Alkazim da kuma Dansa Imam Ali bn Musa Arrida (a.s) wanda dukkaninsu ke Magana kan irin tausayi da Allah madaukakin sarki ke yiwa bayinsa amma kafin nan bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan inji.
Daga cikin irin wasiyoyi da Shugaban Mumunai Imam Ali (a.s) ke yiwa wakilansa a yayin da ya nada su a gariruwa daban daban na Musulinci ga wasiyar da yaiywa Abdullah bn Abas yayin da ya nada shi a matsayin wali na Garin Basara sai Imam Yace masa Ka zamanto mai walwala da shinfidar fuska a tsakanin Al'ummarka mai rahama da adalci wajen hukunci ga Al'umma sannan ka kiyayi yin fishi domin shi fishi wani makami ne daga makaman shaidani.
Har ila yau daga cikin irin wasiku da shugabanmu Imam Ali (a.s) ke aikewa wakilansa yana cewa bayan yayiwa Annabi salati : haki ne a kan ko wani magabaci na kadda ya cansa finsa a kan mutanan da yake gabata kan irin Falala da Allah madaukakin sarki ya bashi sannan ya zamanto mai adalci wajen raba dukiyar da Allah madaukakin sarki yayi umarni a raba tsakanin bayinsa kadda ya zamanto mai fifiko ga 'yan uwansa , abukaninsa ko kuma zuriyarsa sannan ya zamanto mai adalci kan yadda zaiyi amfani da dukiyar Baitul mal.ku saurara hakinku ne a kaina da kadda na boye maku ko wani irin sirri na milki in ba batutuwan da suka shafi yaki ba,sannan kuma in shawarce ku a dukan lamura ba tare da bata lokaci idan har ba hukuncin Allah madaukain sarki ba ne ba,sannan dukkaninku a waje na guda ne, babu wani babbanci ganin irin wannan Mu'amala da Alllah subhanahu wa ta'ala ya umarceni inyi da ku babar ninima ce a gareku kuma wajibi ne ku Godemasa a kan hakan sannan kuma wajibi ne a gareku ku yi mani biyayya. Har ila yau masu saurare irin wadannan kyawawen Dabi'u na Allah madaukakin sarki sun tabbatu a wajen shugabanmu shugaban Mummunai Imam Ali(a.s) wajen Mu'amalarsa da Mutunan wadanda ba Musulmi ba a yayin da suka kai Karen shugabansu kan yanayin da yake Mu'amala da su.sai Imam Ali(a.s) ya rubuta wasika zuwa ga walinsa na wannan gari inda a cikin wannan Wassika yake cewa da dama daga cikin Mutananka suna kokawa da kai kan yadda kade Mu'amala da su cikin fishi da bacin rai tare da muzguna masu da kuma kaskantar da su , sai naga bai kamata ba kayi irin wannan Mu'amala da su saboda Addininsu,sannan bai kamata ka muzguna masu saboda irin Alkawalin da muka kulla da su.ka za manto mai sassauci da tausayi wanda hakan zai kore irin kankin da suka shiga sannan kayi Mu'amala mai kyau tare da su a cikin tausayi.har ila yau ka zamanto mai wasa da dariya tare da su don kusanto ga Addinin Allah.wannan shine abinda muke bukata daga gareka idan Allah ya yarda.
Masu saurare irin wadannan kyawawen Dabi'un Allah madaukakin sarki na tausayi ga bayinsa sun tabbatu ga jikokin Manzon Allah da Imam Ali (a.s) wato Imam Kazim da Imam Rida (a.s)wadanda baban manufar hakan shine nisanta daga cutar da wani ko kuma wasu bayin Allah. A cikin Littafin Kurbul Isnad an rawaito riwaya daga Humairi tare da sanadinsa wanda ke komawa zuwa Mufadal bn Kais inda yake cewa naji baban Hasan na farko wato yana nifin Imam Kazim (a.s) yayi ranzuwa kan cewa ba zai yi magana ba da Muhamad bn Abdullahi Al'Alkat har abada saboda shi Muhamad din na Anfani da Mu'amalarshi tare da Imam Kazim yana kirkira karya sannan ya danganta ta da Imam Kazim (a.s) a daliln haka, ya batar da Al'umma da dama saboda Mutane suna kama zancensa ganin yanda yake kai kawo wajen Imam Kazim (a.s) tare da yadda Imam (a.s) ke kaimasa Ziyara wanda hakan a hakikanin Gaskiya na cutar da kansa da kuma Al'umma mabiya tafarkin Mazhabar iyalan gidan Monzon Rahama tsarkaka,sai Mufadal Bn Kais wanda ya rawaito wannan riwaya yace a raina sai nace shin yanzu wannan shine umarni da Imam ke mana na yin biyayya tare da zumunti?yanzu kuma gashi yayi ranzuwa kan cewa ba zaiyi magana da Dan kawunsa ba har abada? sai Imam Kazim (a.s) ya kallesa sannan yace masa wannan hanya itace zata toshe cutar da Mutane da kuma cutar da kansa saboda idan Mutane suka fahinci cewa bana yi masa magana to kaka ba za su kama zancensa ba sannan shima zai kama bakinsa daga anbatona sai hakan ya zamanto Alkhairi a gareishi da ma Al'umma gaba daya.
A cikin littafin mai suna Uyunu Ahkbaru Rida (a.s)
an rawaito Hadisi daga Umair bn Buraid yana cewa na kasance wajen baban Hasan
Imam Aliyu bn Musa (a.s) sai aka anbaci sunan Muhamd bn Ja'afar shima saboda
irin mummunar Mu'amalarsa da imam (a.s) kan yadda yake kirkira karya yana
danganta ta da Imam sai Imam (a.s) yace nayiwa kaina alkwali ba zan