Ci Gaba da dabi'ar Kunya
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a cikin shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan dabi'ar kunya ganin mahimancin wannan maudi'I shirin na yau ma zai ci gaba da shi, amma kafin nan bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
**************************Musuc**********************
Masu Saurare shirin na yau zai fara da bayyana ma'anar dabi'ar kunya, da kuma Nau'inta gami da misdakinta wanda hakan zai taimaka mana wajen dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a, Hakika cikin Littafin Misbahu-Shari'a, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) na cewa:(Kunya Haske ne asalinsa shi ne tushen Imani, kuma tafsirinsa shi ne juriya da sabati a kan dukkanin abinda ke gyamar Tauhidi da Sani) wannan ma'ana ta sanin Dabi'antuwa da dabi'ar kunya ya kan wajabta juriya da kuma sabati wajen aikata duk wani abu da yake a matsayin abin ki a wajen Allah madaukakin sarki da kuma yake da alaka da tsarkakekken tauhidi, Sani da kuma Imani ga Allah tabaraka wa ta'ala.Masu saurare a wani hadisi na daban Shugabanmu Imam ja'afaru Sadik (a.s) ya sanar da mu hakikanin hasken dabi'ar Kunya da kuma alakar ta da Imani inda yake cewa:(Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:Kunya na tare da Imani, an kayyade kunya da Imani da kuma Imani da kunya, ma'abocin kunya Alheri ne gaba dayansa kuma wanda ba shi da kunya sharri ne gaba dayansa ko da kuwa yayi bautar Allah ya kuma ji tsoran sa, tako daya cikin kare gudirin Allah ta hanyar Kunya ya fi alheri ga ibadar shekaru 70) baya ga haka Imam (a.s) ya ci gaba da bayyana tasirin rashin kunya dake jefa mutum cikin mumunar dabi'a, wanda hakan zai sanya Mutum fadawa cikin nifaki da kuma samun karfin gwiwa wajen aikata sabo da kafirci, Allah ya kiyaye mu fadawa cikin irin wannan hali.Imam (a.s) ya ci gaba da cewa:(mumunar dabi'a ta kan jefa Mutum cikin Munafici, Sabo da kuma kafirci, Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce idan ba ka kunya to kai aikata abinda kaka dama, ma'ana duk wanda ya rabu da kunya duk abinda ya aikata na alheri ko na sharri za a saka masa a kansa).Masu saurare cikin Hadisin sa Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya Shiriyar da mu zuwa ga hanyar dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a inda ya bayyana cewa tsiron wannan dabi'a shi ne kwarjinin Ubangiji da kuma karkata zuwa neman yardar Allah madaukakin sarki.Imam (a.s) ya ci gaba da cewa:(Karfin Kunya daga bakin ciki da tsoro, kuma Kunya gidan tsoron Allah ne, kunya kuma farkonta shine Kwarjini karshen ta kuma shi ne ganin Karamar Allah, ma'abocin kunya kuma shi ne wanda ya shagaltu da kansa, Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce Idan Allah Ta'ala ya nufi Bawa da alheri sai ya yi masa ilhami da kyawawensa, ya kuma sanya daidaito a idanuwansa, ya kuma sanya shi ya kyami zama da masu adawa da Anbaton Allah) a karshen wannan Hadisi Imam Sadik (a.s) ya bayyana martabar dabi'ar kunya da sababin dake taimakon Mutum zuwa ga wannan dabi'a, tushensa kuma shi ne Soyayyar Allah wanda ke sanya Mutum jin kunyar aikata duk wani aiki da Allah tabaraka wa ta'ala ya ki shi, Imam (a.s) ya ce:(Kunya nau'I biyar ne, Kunyar zunubi, kunyar na rageggen aiki, kunyar karama, kunyar Soyayya, da kuma Kunyar Kwarjini, kuma duk daya daga cikin wadannan ahli ce ga ko wani ahlinta kuma nada martaba).
***************************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,ci gaban shirin zai fara da hadisin Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) wacce aka ruwaito cikin Littafin Uyunul Hikam wal Mawa'iz) Imam (a.s) ya ce:(Kunya ita ce dukkanin Karamci da mafi kyakkyawar Hanya, mafi fifiko na dabi'ar Kunya, kunyarka ga Allah da tushen karamci kunya ne, kuma sakamakonsa Kamun Kai) Masu saurare, cikin wannan Hikima ta Shugaban Mumunai za mu fahimce cewa Kunya ita ce dabi'ar dake samar da jarumta dake taimakon Mutun na fuskantar dukkanin aiyukan alheri da kyawawa gami da kauracewa dukkanin abinda yake abin ki ne a wajen Allah tabaraka wa ta'ala da Mutane. Kamar yadda yake dabi'ar Kunya ya kan sanya Mutum ya zamanto mai kamun kai a dukkanin Al'amuransa daga cikin har da kamun kai na ganinsa, domin haka ne ma Shugaban Masu kadaita Allah Aliyu bn Abi Talib (a.s) cikin Littafin uyunul Hikam wal Mawa'iz ya ce:(Kunya rufe ido ) ma'ana rufe Idanu kan abinda yake ya haramta da kuma wanda aka ki kalonsa) Masu saurare a yayin da dabi'ar Kunya ke kiyaye Mutum da aikata abin ki, haka kuma ta kasance taimako wajen tsarkaka daga zunubai, kuma ta kasance wasila na Tuba da kuma Neman gafarar Ubangiji. A kan haka Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya bayyana cewa:(Kunyar Allah yana shafe zunubai mai yawa, kuma kunyar Allah tabaraka wa ta'ala tana kare Mutum daga Azabar wuta). Har ila yau Masu saurare wasu hadisan na daban kuma suna yi mana albishir da cewa dabi'antuwa da dabi'ar Kunya na daga cikin hanyoyin siffantuwa da siffar mabiya tafarkin iyalan gidan Anbata (a.s), sai ya kasance mai wannan kyakkyawar dabi'a abin koyi ga Mumunai da suke bukatar Shiriya, Hakika Kadi Na'aman Almagriby cikin Sharhul-Alkhbar (وى القاضي النعمان المغربي في كتاب شرح الأخبار) ya ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik daga kakansa Imam Ali(a.s) ya ce:(Hakika Allah nada Bayi daga masoyanmu, ya sanya girma a cikin Zukatansu, da kuma tsoron Allah a cikin Damirinsu, ya kuma daukaka Kunya a tsakanin idanuwansu, ya kuma sanya tunani a zukatansu, suka samu kariya daga Allah daga batan batattu, da kuma karyar mulhidai da kuma shakun marassa tunani, da kuma Guliyi na masu fice gona da iri wadanda suka rabu da Addininsu, suka kuma kasance gungu-gungu, ba sa haduwa da gaskanci, su ne hasken ilimi da kuma fuskar Musulinci, maganar su haske ne, kaurace musu kuma Hasara ne, su ne Hujja daga sahibin Hujja, masu rabo da nasara a kan Hujja ga wanda ya bukaci hujja daga cikin Mutane a wajen Allah madaukakin sarki a kan halitunsa, ku bi su, ku yi musu biyayya, ku yi koyi da su sai ku shiryu).
*************************Musuc******************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.