Mar 04, 2016 14:06 UTC
  • zababun Aiyuka-Tafarkin Iyalan gidan Manzon Allah (A.s)

shirin zai yi dubi ne ga wasu wasiyoyi na iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka da Allah ya basu izinin ceto da taimakon bayinsa


Masu saurare Assalamu Aleikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin kyawawen Dabiyun Musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, da dama daga cikin ayoyin Allah madaukakin sarki na yin suka kan aikata Zalinci da Azzalimai har ma da yin La'anta a gareisu wanda hakan na daga cikin Sunar  Allah wajen tushe taimakon Zalinci da Azzalimai tare da kokarin tusa farin ciki a zukatan Mummunai.masu saurare shirin namu na yau zaiyi dubi kan tafarkin Imam Kazim (a.s) wajen tabbatuwarsa da irin wadannan kyawawen Dabi'u.amma kafin nan bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan inji.


 


***************MUSIC*****************


 


Masu saurare riwayarmu ta farko Sikkatul Islam Kulaini ya rawaito cikin littanfinsa mai suna Alkafi daga Ziyad bn Abi Salma inda yace wata rana na shiga wajen baban Hasan Imam Musa Alkazim (a.s) sai yace mani Ya Ziyad shin da gaske ne kana aiki kalkashin hukumar zalinci? Sai na ce masa Hakane, sai ya tambayane ko minene dalilin yin hakan? Sai na ce masa ni Mutune ne mai Iyali sannan bani da wata dukiya wadda zan iya ciyar da su.sai naga ya datse da ni cewa  duk aikin da na samu koda kalakshin hukumar Azzalimai ne in karba. sai Imam Yace mani Ya ZIyad ko da zan fado daga sama inyi kucin kucin, shi ya fiyemin da inyi aiki tare da su  ko kuma in kasance ina tare da su a bisa mazuni  guda daya wato Imam yana nifin Hukumar Zalinci sai Imam ya ci gaba da cewa kasan ko mi yasa?sai Zayad yace bansaniba? Sai Imam (a.s) Yace:sai dai don warware matsalar Mummunai,ko taimakon wadanda aka zalinta ko kuma biyan bashinsu, domin karamar azaba da Allah madaukakin sarki zaiyiwa Mutanan da suke aiki tare da hukumar zalinci ko kuma taimaka masu itace a lullube su da wuta har sai angama dukkanin hisabin Halittu gaba daya.Ya Ziyad idan har ka karbi wani mukami daga hukumar zalinci to ka kautatawa 'yan uwanka daya bayan daya wato Imam yananifin 'yan uwansa na addini sannan Imam ya ci gaba da cewa idan kayi hakan Allah na tare da kai. Ya Ziyad idan har ka tuna karfin ikon  da kare ka a kan Mutane to ka tuna karfin ikon da Allah madaukakin sarki gareishi a kanka a ranar gobe.


Masu saurarenmu abinda wannan hadisin ke bayyana mana shine bai halitta ga Mummuni yayi aiki tare da Azzalimai ko kuma karkashin Azzalimai saidai idan zai iya taimakon Mummunai ko kuma zai iya tushe wani zalinci da Azzaliman keyi don haka duk mummunin dake da rauni a hukumar Azzalimai wato bai sawa bai hanawa to kasance tare da wadannan Azzalimai bas hi da wata fa'ida.


 


A cikin Littafi mai suna Kada'ul hukukul mummunin na Abi Ali bn Tahir Assury an rawaito hadisi daga wani Mutune dan Garin Rai yana cewa:Yahaya bn Khalid ya barmana wani Littafi da nifin mu mayar da shi a wajen mamallakinsa  sai Aliyu Bakaya ya bukaci in bashi wannan Littafi  domin yayi da'awar cewa nasa ne sai na ji tsoron cewa idan na hana masa zan fada  cikin sabo , sai aka ce mani  kadda in bashi domin yana da'awar nasa ne amma ba na shi ne ba,sai na ji tsoron cewa idan na hana shi sannan kuma ya tabbata cewa na sa ne  to kaka na abka cikin  sabo, sai na nemi shawarar Mutane daga karshe sai suka bani shawarar cewa in  mayar da Al'amarin wajen ubangiji, sai na dauki niyar zuwa hajji don in meka kukana wajen ubangiji, lokacin da naje hajji sai muka hadu da shugabanmu Imam Musa bn Ja'afar Alkazim  (a.s) sai na meka kukakana a gareishi,bayan Imam ya saurareni sai  ya bayi amsawa a rubuce kamar :bismillahi Rahamani rahim kasani cewa a kwai wata Inuwa kalkashin Al'arshin Ubangiji wadda ba mai shigarta sai wanda ke taimakon Dan Uwansa,mai kokarin ganin ya magance matsalar Dan uwansa ,sannan kuma mai sanya farin ciki a cikin 'yan uwansa musulmi, kuma wannan Dan Uwankane Musulmi wassalam.


 


 


*************MUSIC*****


 


Bayan na dawo Gida daga aikin hajji sai na je gidan wannan bawan Allah don bashi Littafinsa , sai na fita cikin dare saboda sirri a yayin da na isa na nemi izinin shiga daga gareishi inda na  ce masa Ma'aiki daga wajen Imam Musa bn Ja'afar Alkazim (a.s) sai ya fito cikin gaggawa ya bude mani kofa, sannan ya sunbaceni,ya rungumeni a kirjinsa hakan ya kasance yana yi duk lokaci da na bashi Labarin Imam Kazim (a.s) sai na bashi labarina tare da haduwata  da Imam Kazim (a.s) sannan na koda masa wassikar da Imam Kazim (a.s) ya bani ta amsar tambayata, sai  ya dauki wannan wasika ya sunbace ta sannan yaji dadi sosai , har ila yau na bashi littafinsa dake gurina sai ya  bada umarni da a kawo masa dukiyarsa da kayan sawarsa ga baki daya, ya fara rabawa kashi kashi, a bangaren gudi kuwa  dinare,dinare, dirhami,dirhami , sannan a bangaren kayan sai ya rabasu gida biyu sai ya dauki kashi guda na kudin da kayen ya maikamini sannan ya tambaye ni shin ko naji dadi da wannan kyauta:? Sai nace Eh wallahi. Bayan hakan akwai wasu kayayyakin da yakasa rabasu gida biyu sai ya dauko su ya kara mani sannan ya  sake tambayata ko ya sanya farin ciki a zuciyata ? sai na ce masa Eh wallahi.haka farin ciki ya lullube zuciyata. A lokacin da na bukaci in tafi Gida sai ya kira dan aiki ya dauki mani kayana haka muka rabu da shi cikin annashuwa da fara'a.


Lokacin da na dawo gida sai nace ba zan iya  sakawa wannan Bawan Allah ba saidai kawai in sake komawa aikin  hajji kamar yadda da je a baya don neman taimakon Allah wajen warware wannan matsala in rokamasa Allah ya bashi gidan Aljanna kan wannan Alkhairin da ya mini. Lokacin da na tafi aikin Hajji sai muka sake haduwa da Imam Kazim (a.s) sai na bashi dukkanin Labarin day a faru da ni tare da wannan bawan Allah, sai naga fuskar Imam (a.s) ta cika a fara'a sai Nace Ya shugaba na shin kaji dadi na wannan Labari? Sai Yace:ey wallahi hakika na yin farin ciki da hakan kuma abinda wannan Bawan Allah yayi ya sanya shugaban  farin ciki ga Mummunai  anan Imam na nufin shugaban Mummunai da Imam Ali(a.s) Imam Kazim (a.s) ya ci gaba da cewa wallahi wannan aiki kakana Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi ya yarda da shi haka zalika babu shakka Allah madaukaki ma ya yarda da wannan aiki


 


 


***********MUSIC***********


 


Masu saurare riwayarmu ta karshe har ila yau an rawaito ta ne a cikin littafin Kada'ul mummunin na Abi Ali bn Tahir inda aka ce Aliyu bn Yaktin ya nemi izinin barin Aikin da yake yi a hukumar Azzalimai daga Imam Kazim (a.s) ganin yadda yake kare hakin Mummunai da yadda yake hana a gudanar da zalinci sai Imam (a.s) ya ki bashi wannan dama inda yace masa kadda kayi murabus domin kai kadai ne mai kore mana kewa a wannan Milki sannan kuma kai abin alfari ne ga 'yan uwanka mummunai ,mai yuyuwa Allah ya sanya kai ne sanadiyar  rushrwar wannan hukuma ta zalinci. Ya Ali ka sani cewa kaffarar aiyukanku shine taimako ga 'yan uwanku,ya Ali kayi min  alkawlin Abu guda ni kuma zan baka tabbacin abubuwa guda ukku, kayi min alkalin cewa ba za ka juya baya ba  ga masoyanmu duk lokacin da wata bukatarsu ta taso zaka iya kokarinka na ganin cewa ka maganceta sannan ka kirmama su, ni kuma zan baka tabbacin cewa idan har ka aikata hakan na farko ba zaka shiga gidan Kaso ba har Abada, na biyu kafin Takoba ba zai huda jikin ba har abada,na uku talauci ba zai shiga gidanda ba har Abada. Ya Ali duk wanda ya sanya farin cikin a zukatan Mummunai to babu shakka kamar ya faranta Ran Ma'aikin Allah ne da kuma mu imam yana nifin mu a nan A'imomi guda 12 daga iyalan gidan Ma'aiki  tsarkaka sannan kuma babu shakka sai samu samako mai yawa daga Allah madaukakin sarki.


 


Masu saurare Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshen don haka a nan zamu dasa Aya sai kuma a Maku mai zuwa idan Allah ya kaimu a madadin Aminu Ibrahim Kiyawa da ya hada shirin aka saurara ni jagoran shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.