zababun Aiyuka-Sunar Allah wajen yiwa Bayinsa Jinkiri
shirin zai yi bayyani dangane da sunar Allah ga byinsa wajen yi masu jinkiri domin ya basu damar gyara aiyukansu
Masu saurare Assalama Aleikum barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin kyawawen Dabi'un Musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,daga cikin siffofin Allah madaukin sarki akwai jinkiri ga bayinsa don basu dama gyara kusruren da suka aikata, hakika Allah madaukakin sarki yayi Alkawalin cewa sai ya tabbatar da Addininsa a doran kasar baki daya ,sannan kuma yayi wa bayinsa Salihai alkawalin gadar masu Gasarsa ,saidai wajen tabbatar da hakan, Allah madaukakin sarki ba ya gaggawa , saboda ya baiwa gungu gungu masu ganin cewa suna iya cikekken milki ba tare da kuskure ba gudanar da na su milkin,daga karshe ya sanya Hukumarsa ta adalci ta mallaki Duniya gaba daya wanda kuma babu wata hukuma da ta iya gudanar da miliki cikin Adalci da masalahar Al'umma kuma ta mallaki duniya gabaki daya in bat a Allah madaukakin sarki ba.masu saurare irin wadannan kyawawen Dabi'u na yin jingiri wajen meda martani sun tabbatu ga iyalan gidan Manzan Rahama tsarkaka musamman ma wajen Mu'amalarsu da sauren Al'umma.amma kafin mu shiga shirin ba ri mu saurari a binda a kayi mana tanadi a kan faifai.
************************MUsuc**************************
Masu saurare shirin na mu na yau zai dubi ne kan tafarkin shugabanmu Imam Bakir(a.s) a cikin riwayar da Abi bakar Hadrami ya rawaito inda yake cewa : yayin da aka kai Imam Bakir(a.s) birnin Sham wajen Hisham bn Abdulmalik Imam Bakir (a.s)ya kasance a kofar Majalisin Hisham bn Abdulmalik kafin a bada umarnin shugowarsa ,sai Hisham bn Abdulmalik yacewa fadawansa tare da na hannun damarsa daga cikin kabilar Bani Umaiya. A lokacin da kuka na muzanta Muhamad bn Ali to kuma ku muzanta shi daya bayan daya.sannan ya bada izini a shigo da Imam(a.s). A yayin da Abu Ja'afar (a.s) ya shigo sai ya daga hanunsa yayi sallama ga Mutanan gurin baki daya yace Masu Assalama Aleikum.sannan ya samu guri ya zauna , ganin haka sai bacin rai ya kara turnike Hisham bn Abdulmalik saboda Imam bai je wajensa ba yayi masa Gaisuwa ta musaman a matsayin khalifa sannan kuma ya zauna ba tare da ya nemi izininsa ba,sai ya juya wajen Imam (a.s) ya fara sukan lamirinsa tare da muzguna masa yana cewa ya Muhamd bn Ali har yanzu ka san cewa a kwai me rike da sandar Musulmi yana nifin kansa wato ya nufin shine Imami ko khalifa na wancen lokaci , ya fadi magangannu masu yawa na muzgunawa Imam(a.s).
Bayan yayi shuru sai Mutanan dake zaune a fadarsa suka fara kalaman batanci tare da sukan lamirin Imam (a.s) daya bayan daya ,har na karshen ya gama ba tare da ya katse masu maganarsu ba kuma bai ce masu komai ba , bayan sun gama sukansu da cin zarafi sai Imam (a.s) ya tashi sannan yace masu yaku Mutane ina za kujeson ko kuma ina ake son zuwa da ku, daga garemu ne Allah ya shiryar da na farkonku, kuma daga garemu ne za'a kamala shiryar da na karshenku, idan kuna tsammanin kuna da milki mai gaggawa to mu kuma muna da milki mai jinkiri kuma babu wani milki bayan namu milkin domin muke da kyakyawar makoma , Allah madaukakin sarki yana cewa kyakyawar makoma ta masu tsoran Allah ne.
musuc
masu saurare haka ta wannan hanya Imam(a.s) ya bayyanawa hukumar umawiya cewa babu wata Daula inba ta iyalan gidan manzan Allah ba kuma itace daular karshe wadda zata wanzar da adalci a dororn kasar baki daya wato anan Imam Bakir (a.s) yana nifin daular jikansa Imam Mahdi(a.s), bayan wannan bayanai na Imam Bakir(a.s) sai aka bada umarni a kaishi Gidan kaso.a ci gaban wannan riwaya ta Abi Bakar Hadrami an bayyana cewa sai aka yi umarni a fice da shi Gidan Kaso, a lokacin da aka kaishi sai ya ci gaba da da'awarsa kafin wani lokaci dukkanin 'yan gidan kason sun zama mabiya tafarkin mazhabar Ahlulbait (a.s), da ganin haka sai shugaban Gidan kason ya ruga zuwa wajen Hashim yace masa:ya shugaban mummunai ba shakka ina fargabar cewa an kusa a rabaka da Al'ummar Garin Sham sannan ya bashi labarin abinda ke faruwa a Gidan Kaso.wato irin abinda Imam Bakir (a.s) ya aikata a gidan Kason ,wanda ya rawaito riwayar sai yace sai aka bada umarni a mayar da shi Garin Madina shi da sahabansa sannan kuma aka umarci dukkanin 'yan kasuwa kadda su sayar masu da komai a hanyarsu ta komawa Madina sai suka kasamce ba su ci komai har zuwa kwanaki 3,bayan sun isa Garin Madayyana sai aka rufe kofar Garin ,a wannan lokaci sahaban Imam (a.s) sai suka meka kukansu wajen Imam(a.s) saboda tsananin yunwa da ishurwa sai Imam(a.s) ya hau babban dutsi na wannan Gari, domin yayiwa 'yan Garin Madayyana jawabi sai ya daga muryarsa don kowa da kowa ya ji yace yak u Mutanan wannan Gari . nine Bakiyatullah wanda Allah yake nifi a cikin Alkur'ani mai Girma بقية الله خير لكم إن كنتم مؤمنين وما أنا عليكم بحفيظ". Wato abin da zai wanzu a gare ku na alheri a wurin Allah shi ya fi muku in kun kasance muminai.ni kuma ba mai gadin ku ba ne''.
Wanda ya rawaito wannan hadisi ya ci gaba da cewa a cikin Al'ummar Garin Madayyana a kwai wani Lattijo mai yawan shekaru sai ya tashi ya tattara Al'ummar Garin sannan yace masu ya ku Al'ummar wannan Gari, wallahi wannan kira irin da'awar Annabi Shu'aibu(a.s) ce, don haka idan baku bude kasuwanninku ba ga wannan Bawan Allah to Azaba na iya sabka a gareiku imam daga samanku ko kuma daga kasan digadiganku, don haka ko da ya kasance za ku karyatani a abubuwan da suka gabata , to a wannan karo ku Gasgantani sannan kuma ku yi biyayya a gareini domin nib a wani bane illa mai Galgadi ne a gareiku.daga jin wannan Magana sai suka gaggauta bude kasuwaninsu ga Imam Abi Ja'afar (a.s) tare da sahabansa.sai wannan labarin na lattijo ya isa wajen Hisham bn Abdulmalik, dan jin haka sai ran Hisham ya kara baci sannan ya tura cikin gaggawa aka kawo masa wannan Lattijo , wanda ya rawaito wannan hadisi yace babu wani wanda ya san yadda Hisham bn Abdulmalik yayi da wannan Lattijo.
Musuc
Masu saurare ganin cewa lokaci na hararrenmu a nan za mu dasa aya, sai kuma a Mako na gaba idan Allah ya kaimu za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da hada shirin aka saurara ni madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.