Mar 04, 2016 14:13 UTC
  • zababun Aiyuka-Aiki tare da manufa

shirin zai bayyani kan mahimancin gudanar da aiyuka tare da manufa


Masu saurare Assalamu Aleikum barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin kyawawen Dabi'un musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi , daga cikin Siffofin Allah madaukakin sarki a kwai cewa Allah madaukakin sarki baya wani aiki ba tare da manufa ba kamar yadda yake cewa a cikin Alkur'aninsa mai girma ban halaci Mutune da Aljan ba sai don su baitamin , idan muka duba cikin rayuwar Annabawansa tare da waliyansa makusanta za muga cewa suma sun suffanto da irin wadannan siffofi kyawawa ma'ana za kaga duk aiyukan da suka yana da manufa babu wasa a cikinsa.amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.


 


Musuc*************************************************************


 


Masu saurare aiki tare da manufa shine hakikanin hikima, kamar yadda aka ruwaito cikin Tafsirul majma'ul bayan dga Aliyu bn Asbat yana cewa wata rana na shiga Garin Madina kan hanyata ta zuwa kasar Masar sai na shiga wajen baban Ja'afar Muhamad bn Ali Arrida (a.s) a wancan lokacin Imam(a.s) nada kimanin shekaru hamsin  a Duniya sai na kasance ina tunanin kan yadda zan siffanta shi ga Mutananmu  idan na isa Masar wato ganin cewa yana da yawan shekaru,sai Imam (a.s) ya kalleni sannan yace maniYa Ali Hakika Allah madaukakin Sarki ya sanya Imamanci ko khalifanici  kamar yadda ya sanya a annabci sai Imam (a.s) ya karanto wannan ayoyi guda biyu ta farko itace ولما بلغ أشده واستوى آتيناه حكما وعلما" wato lokacin kuma da yakai karfinsa ya kuma kammala ,sai muka bashi hukunci da ilimi.sannan kuma  ya kara karanto wannan Aya  kamar haka واتيناه الحكم صبيا"، kuma muka bashi annabci tun yana karami . wato idan aka  hada wadannan Ayoyi guda biyu  wato Imam (a.s) yana nifin cewa kamar yadda Allah madaukakin sarki ke bayar da hukunci ga Dan shekaru 40 haka zalika yake bayarwa ga yaro dan karami ko kuma jariri.


Masu saurare wadannan kyawawen siffofi na Allah madaukakin sarki tare da Annabawansa sun tabbatu a tafarkin Imamai na iyalan Gidan Ma'aikin Allah tsarkaka tun farkon rayuwarsu, misali Imam Hasan Askari (a.s) ya shahara wajen kyawawen Dabi'u irin na Kakansa Ma'aikin Allah Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka wajen kyautarsa,nutsuwarsa,karamcnisa, kamin  kansa da saurensu ,haka zalika tun yana Dan karami yayi fice ga  sarakai da Maliman lokacinsa, a cikin litattafan Duraru Asnaf,Nurul Absar da Sawa'ikul muhrika an rawaito wani hadisi yana cewa  wata rana Bahlul ya ga Imam Hasan Askari (a.s)yana kuka ,lokacin  kuma yana yaro dan kankane , a yayin da sauren yaran suke wasa  a kusa das hi. sai Bahlul yayi tsammanin cewa Imam Hasan Askari (a.s) yana kuka ne sanadiyar ko yaran nan sun amshe masa abin wasansa sai yace wa Imam Hasan (a.s) shin kana so in siyamaka abin wasa? Sai Imam Yace masa ba a halicemu ba don wasa sai Bahlul yace to don mi aka haliccemu ? sai Imam (a.s) yace masa don neman ilimi da Ibada sai Bahlul yace daga ina ka samu wannan? Sai Imam (a.s) yace daga Fadar Allah madaukakin sarki  "أفحسبتم أنما خلقناكم عبثا، وأنكم إلينا لا ترجعون" ga fassarar Ayar (Allah ya ce da su ) ko kuna tsammani ne cewa mun halicce ku ne da wasa kuma ku ba za a dawo da ku gare Mu ba.


 


Musuc***********************************************


 


Masu saurare daga cikin amfanin gudanar da  aiyuka tare manufa da kuma nisantar wassani shine Mutune ya tsarkake halayansa daga almubanziranci ko kuma banzatarwa domin  irin yauni da Dan Adam yake jin cewa yana da shi  .wannan shine irin wasiyar da Imaman na iyalan gidan Ma'aikin Allah ke yi.misali idan muka dubi riwayar da sheik kulaini ya rawaito cikin littafinsa mai suna Alkafi daga Yasir hadimin Imam Rida (a.s) yana cewa wata rana wasu bayi guda biyu daga cikin bayin Imam Rida (a.s) sun kasance suna cin Touffa sai suka gutsiri kadan daga ciki, sannan  suka yi jifa da sauren  sai Imam Rida (a.s) yace masu Subhanallah idan kun wadatu da shi  to a kwai masu bukatarsa , idan  ku ba kwa ci, to  ku ciyar da mabukata.


 


Masu saurare daga cikin Dabi'un Allah madaukakin sarki bada mafuka ga wanda ya nemi mafukar a gareishi ko da ya kasance mai aikata sabo ne , hakika wadannan kyawawen dabi'u sun tabbatu ga iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka , idan muka dubi irin taimako da Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin (a.s) yayi ga bani umaiwa yayin da suka nemi mafuka a gareishi bayan sun aikata mumunan aiki ga Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsakaka a waki'ar karbalah, imam ya baiwa iyalan Marwan mafuka kamar yadda ya bukata yayin da Al'ummar Garin Madina suka yi bori a gareisu, a wata waki'a da ake kiranta واقعة الطف الدامية ko kuma waki'atul hur,maliman tarihi sun rubuta cewa bayan mumunan aikin da yazid dan mu'awiya ya aikata a Karbala'a na kashe iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka musaman ma shugaban samarin Aljanna Imam Husain (a.s), Mutanan  Garin Madina sun yi wani bori  ga shugabanin Bani Umaiya dake wannan Gari mai tsarki inda suka kai hari da nufin kashe Gwamnan bani Umaiya da manyan 'yan siyasarsu wadanda suke shugabanci a Garin Madina sai suka gudu,amma  kafin su gudun sun  nemi gurin da za su bar Matansu da 'ya'yansu  sai Imam Zainul Abidin (a.s) ya karbesu ya ciyar da su ya shayar da su kamar iyalansa ya basu kariya har saida ya tabbatar suna cikin aminci.shahararen malamin Tarihi nan sheik Tabri ya rawaito hadisi a cikin shahararren littafinsa na tarihi wato Tarihul Tabri  inda a cikin Hadisin aka ce Hakika Aliyu bn Husaini(a.s) ya baiwa iyalan Marwan bn Hakan mafuka yayin da  za su gudu daga Garin Madina zuwa Sham saboda borin Mutanan Madina a gareisu.Tabri ya rawaito hadisi daga Muhamad bn Sa'ad shima daga Muhamad bnUmar yana cewa yayin da Mutanan Madina suka fidda Usman bn Muhamad (wato shine Gwamnan Bani Umaiya a wancen lokaci )daga Garin Madina sai Marwan bn Hakam ya bukaci Ibn Umar ya baiwa iyaliansa mafuka sai Ibn  Umar yaki amincewa sai yaje wajen Imam Aliyu bn Husain (a.s) ya bukaci ya baiwa Iyalansa mafuka sai Imam (a.s) ya amince da bukatar tasa ya ciyar da su ya shayar da su kamar yadda yake ciyar da iyalansa ya basu mafuka har saida ya tabbatar da cewa suna cikin aminci.


 


Musu**************************************


 


Masu anan shirin namu zai dasa aya sai kuma a Mako na gaba idan  Allah ya kaimu za a jimu dauke da wani sabon shiri a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da hada shirin aka saurara ni  madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.