Mar 04, 2016 14:17 UTC
  • zababun Aiyuka-Tafarkin Iyalan gidan Annabin Rahama

Shirin zai yi bayyani kan yadda iyalan gidan Annabin Rahama suka dabi'antu da kyawawen Allah madaukakin sarki


Masu saurare Assalama Aleikum barkanku da warhaka barkankanku da sake saduwa da mu a cikin shirin kyawawen  dabi'un musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, hakika Allah madaukakin sarki shine mawadaci wanda kuma baya bukacar taimakon kowa da kowa  kuma ba ya gafala wajen wadatar da bayinsa don haka shirin na mu na yau zaiyi dubu ne ga tafarkin iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka kan yadda suka tabbatu da wannan kyakyawar halaye  amma kafin nan ,bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.


 


Musuc***********************************


 


Masu saurare hadisin mu na farko Sheik Mufid (r.a) ya rawaito cikin littafinsa mai suna Kitabul Irshad daga Abi Abdul…Sadik (a.s)yace:Muhamad bn Munkadir ya kasance yana fada:ban yi tsammanin ba zanga wani Mutune mai falala da karamci kamar Aliyu bn Husaini(a.s)  har saida na hadu da  Dansa Muhamad bn Ali (a.s) yayin da naso inyi masa wa'azi sai yayi mani wa'azi. Sai Mutanan da suke tare da shi  suka ce masa  a kan minene ya yi maka wa'azi? Sai Muhamad bn Munkadir yace:wata rana na fita kewayen Garin Madina a lokacin tsananin zafi sai na ga Muhamad bn Ali cikin Gonarsa yayi aiki matukar aiki har ya gaji zufa na zuba daga jikinsa kamar yadda kuka sani Muhamad bn Ali(a.s) Mutune mai jiki don haka saboda gajiyar da yayi ya jinginu a jikin bayinsa guda biyu sai a cikin raina nace babban lattijo daga cikin lattijawan Kuraishawa a wannan lokaci cikin wannan yanayi yana neman Duniya?ba shakka sai nayi masa wa'azi ko kuma sai nayi masa galgadi sai na ruga zuwa gareishi, bayan nai masa sallama  sai amsa mini zufa na zuba daga jikinsa, sai nace masa Allah ya shiryeku, babban shaihi daga cikin Sheihunnan Kuraishawa a wannan lokaci cikin wannan Yanayi yana naiman Duniya?mi zaka ce da Mutuwa zata zoma kana cikin wannan yanayi?sai Imam (a.s) ya bar bayin da ya jingina da su sannan ya ce:wallahi da Mutuwa za ta saman cikin wannan yanayi to babu shakka ta same ni ne cikin biyayya daga biyayyar Allah madaukaki domin na dogara da kaina ta hanyar wannan Noma kuma ina biyar bukatun Mutane da dama , ka ji tsoron Mutuwa yayin da za ta same ka kana aikata sabo daga cikin sabon Allah madaukaki , don haka ina tsoron mutuwa ta sameni yayin aikata sabon ubagiji. Sai Muhamad bn Munkadir yace ma Imam(a.s) Allah yayi rahama a gareiku na zo da niyar inyi maku wa'azi amma gashi na amfana da wa'azin da kayi mani.


Masu sausare wannan riwaya na karnatar da mu cewa dogaro da kai , wajen neman abinci ta hanyar halal ibada ne, domin a kwai hadisin dake cewa Allah na karkare zunuban bayinsa ta hanyar neman abincin da shi  na halal  ko ga iyalansa.


Riwayarmu ta gaba kwa na magana ne kan irin karamcin da iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka ke yi ga Mutuman da yayi masu kazafi cikin rashin sani. Hafiz Sarwi Alhabli Almazandarani ya rawaito wani Hadisi cikin littafinsa mai suna Almunakif yayin da yake Ambato falalar Imam Sadik(a.s) yace wani Mutune daga Alhazan Madina ya kwanta sai yayi mafalkin cewa an sace masa jikkarsa ta kudi  , yayin da ya tashi sai ya fita daga gurin kwanansa ya hadu da Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yana sallah sai dai wannan bako bai san ko waye Imam ba, wato bai san cewa ba shi  jikan Ma'aikin Allah ne ba, sai  ya tsaya a kusan Imam (a.s) har  saida ya gama sallah sannan yace masa kai ne ka dauki jikkata ta kudi,sai Imam Sadik(a.s) yace masa nawane a cikin jikkar? Sai wannan Mutuman yace Dinarai Dubu. Sai Imam Sadik (a.s) ya kama hanun sa har suka isa Gidansa sannan ya kilga dinare dubu ya bashi. Bayan ya dawo Gidansa  sai ya samu jikkar tasa  ta kudu a inda ya ajjeta sannan ya tabbatar da cewa mafalki ne yaga an daukemasa jikka tasa ta kudi. Sai ya koma wajen Imam Sadik (a.s) yana neman gafara sannan ya medo masa kudansa sai Imam sadik(a.s) ya ki ya amshi wannan kudi sannan yace  Mu duk abinda ya fita daga hanunmu ba ya dawowa. Wanda ya rawaito wannan hadisin yace bayan wannan abu sai wannan Mutune ya tambaya da cewa ko wanene wannan Mutuman da yayi masa wannan karmamci sai aka ce masa ay Imam Ja'afaru Sadik ne (a.s) sai wannan Mutune yace tun da nike a rayuwata ban ta ba aikata babban laifi ba kamar wannan.


 


Musuc*****************************


 


Masu saurare riwayarmu ta gaba kuma ta karshe na ishara ne kan fadar Gaskiya domin fadin gaskiya na daga cikin kyawawen dabi'u musulinci.har ila yau cikin Littafin Almunakib na Hafiz Habli an rawaito hadisi a babi na labaran Khalifofi.


A cikin wannan hadisi ance Haruna Rashid ya kasance yana cewa Imam Musa bn Ja'afar  kazo in mayar maka da Fadak (Fadak wata Garka ce da Khalifofin da suka gabata su ka amshe daga hanun Sayyida Fatumatu Zahra (s.a) diyar Manzan Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka wato Gadonta ne da Manzon Allah ya bar mata aka hanata.Harunar Rachid ya bayyana hakan ne don yaudarar Al'ummar musulmi kan cewa ya kautatawa iyalan gidan Monzon Allah (s.a.w) domin kafin Fadak ay ga Maganar Khalifanci wanda yake hakin iyalan gidan Ma'aikin Allah ne amma baya maganar khalifancin sai ya dauko maganar Fadak) Imam Musa bn Ja'afar yaki amince wa har saida ya nace a kan hakan sai Imam yace masa ba zan amsa ba sai dai idan zaka bani ita tare da dukkanin iyakokinta?sai Haruna rachid yace inane iyakokinta? Sai Imam (a.s) yace masa idan na shata iyakokin ba za ka iya bayar wa ba,harun Rashid sai yace na rance da kakanku ma'aikin Allah (s.a.w) zan ba ku. Imam (a.s)yace iyaka ta farko shine Adan (adan wani yanki ne na kasahsen larabawa yankin da ya shafi irin kasashen Saudi Arabiya) sai fuskar Haruna rachida ta canza, Imam ya ci gaba da cewa iyaka ta biyu Sarmakand (sarmakand yanki ne na karshen hukumar Harunar Rashid a yankin gabas) sai fuskarsa ta rikida . Imam (a.s) ya ci gaba da cewa iyaka ta ukku shine yankin Afirka gabaki daya  sai haruna Rashid ya rude , imam (a.s) yace iyaka ta hudu yanki ruwa wanda ya shafi tsibiri tsibiri tare da Armanistan (shi kwa wannan yanki yanki ne na karshen arewacin hukumar Harunar Rashid) sai  ransa ya bace duk ya rikide sannan yace idan na baka wannan, kenan mu babu abinda zai mana saura. Sai Imam (a.s)yace  dama na fada nace idan na bayyana  maka iyakokinta ba za ka iya bamu ba. Masu saurare a nan Harunar rashida ya so ya yaudari Al'ummar musulmi na cewa ya mayar wa iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka hakinsu sai ya bayyana masa cewa idan har da gaske yake to ya basu hakikanin hakkinsu shine khalifanci . daga wannan lokaci sai khalifan abbasiyawa ya dauki aniyar kashe Imam (a.s) saboda ya bayyana masa Gaskiya haka ya yi da kulle kullen makirci  sai da yaga ya cimma gurinsa wato sai da imam (a.s) yayi shahada ya koma ga Mahilinsa.


 


Musuc****************************************************


 


Masu  saurare anan shirin namu zai dasa aya sai kuma a Mako na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da hada shirin aka saurara ni  madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.