zababun Aiyuka-Girmama Dan Adam
Shirin zai yi bayyani kan mahimancin girmama Mutum a matsayin na Dan Adam kamar yadda Allah madaukakin sarki ya giramama shi
Masu saurare Asslama aleikum barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin kyawawen Dabi'un musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabar da shi ,shirin na mu na yau zai yi dubu ne kan Girmama Mutune a matsayinsa na Dan Adam kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa hakika munyi karamci ga bani Adama wannan kyawawen Dabu'u sun tabbatu ga iyalan gidan Manzon rahama tsarkaka wajen mu'amalarsu da Al'umma amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.
Musuc********************************
Sikatul Islam Kulaini ya rawaito hadisi cikin Littafinsa mai suna Alkafi daga Abdullahi bn Salat daga wani Mutune daga cikin Mutanan birnin Balakh yace na kasance da Imam Rida (a.s) a bulaguransa zuwa garin khurasan lokacin cin abinci sai Imam(a.s) ya kira dukkanin bayinsa bakake da farare bak daya domin su ci abincin a kwano guda sai na ce masa haba Imam da dai za'a fiddawa wadannan bayi kwanonsu daban? Sai Imam (a.s) yace mani inyi shuru wata irin magane ce nike fada ne? ubangiji madaukakin sarki daya, uwa daya ,uba daya kuma makomar Mutue da sakaryarsa na tattare ne da aikata. Masu saurare abinda Imam(a.s) yake nifi a wannan hadisi shine mu dukkanmu ubangijinmu guda ne kuma mun fito ne daga uwa guda uba guda wato daga Annabi Adam da Hawwa amincin Allah ya tabbata a gareisu sannan kuma karshen aikin da Mutune ya aikata shi zai tarar a wajen Allah.haka zalika masu saurare idan muke duba tafarkin shugabanmu Imam Rida (a.s) za mu ga cewa ya shahara wajen girmama Dan Adam da kuma mutuntashi sannan ya nisanto da aiyukan Jahiliya wanda ya gido a kan dukiya ko asali wanda kuma haka ya sabawa koyarwar musulnci wadda ta ginu a kan tsoron Allah da kyawawen aiyuka. A cikin littafin Alkafi na sheik Kulaini an rawaito hadisi daga Yasir da Nadir Hadiman Imam Rida (a.s) inda suka ce: Abu Hasan (a.s) yace mana ko da na kasance a tsaye a kanku bawai kiranku kawai ba matukar kuna cin Abinci to kadda ku tashi har sai kun gama, mai yuyuwa an taba kiran wasunmu yayin da suke cin abinci aka ce suna cin abinci sai aka ce akyalesu har sai sun gama.har ila yau an samo hadisi daga Nadir Hadimin Imam Rida (a.s) yana cewa idan dayanmu na cin abince ba ya wata Hidima ga Imam (a.s) har sai ya gama.har ila yau Nadir ya ci gaba da cewa Imam Rida (a.s) ya kasance yana dora Jauzinajatu a bisa 'yar uwarta sannan sai ya bani (Jauzinajatu wani nau'I ne na abinci).
Musuc**********************************************
Masu saurare daga cikin kyawawen dabi'un musulinci nuna soyayya ga salihan bayi tare da nuna kiyayya ga makiyansu , hakika Alkur'ani mai kirma ya Ambato Ayoyi da dama wadanda suke ishara kan soyayyar Allah ga bayinsa Salihai.irin wadannan Dabi'u sun tabbatu ga iyalan Manzon Rahama tsarkaka kamar yadda wannan hadisi da sheik kulaini ya rawaito daga Sulaiman bn Ja'afar Ja'afari inda yake cewa na shiga wajen Babban hasan Rida (a.s) sai na tarar a gabansa a kwai dabino mai dama sannan kuma yana cinsa da gaske sai yace mani Ya Suleimane rugo muci wannan Dabino sai na iso wajensa muke cin wannan Dabino tare , sannan sai nace masa ya baban hasan gani nike yadda kake cin wannan Dabino da alamun kana sonsa sosai sai Imam (a.s) yace masa na'am hakika ina sha'awar cin Dabino. Sai nace masa ko mi yasa yake sha'awasar cin Dabino?sai Imam(a.s) yace mani domin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa ya kasance ma'abucin Dabino ne,haka shugaban mumunai Aliyu bn abi talib(a.s) da kuma Hasan(a.s) da babban Abdullah Husain(a.s) da shugaban masu Ibada Zainul Abidin (a.s) da kuma Babban Ja'afar Imam Bakir (a.s) da kuma Babban Ja'afar Imam Bakir (a.s) da kuma Babban Abdullah Imam Sadik (a.s) haka zalika Babana Imam Kazim (a.s) dukkanisu ma'abuta dabino ne kuma nima ma'abucin Dabinone sosai haka zalika mabiyanmu suna son Dabino sosai domin an halarcesu ne daga Tabonmu,makiyanmu ya kai Suleimane masoya maye ne domin an haliccesu ne daga tacaccen harshen wuta.
Masu saurare idan muka dubi wasu Ayoyi na Alkur'ani mai kirma tare da hadisan ma'aikin Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka za muga cewa soyayyar Allah ga Bayinsasalihai na tabbatuwa ne wajen daukaka matsayinsu tare da sanya su cikin mafi girma a Aljanna da kuma saurensu amma abinda ya shafi 'yan Adam za muga cewa farin ciki yayain da suka farin ciki taya sub akin ciki yayin da suke cikin damuwa nab akin ciki da saurensu.
Music************************************************
Masu anan shirin namu na yau zai dasa aya sai kuma a Mako na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da hada shirin aka saurara ni madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.