Mar 04, 2016 14:26 UTC
  • zababun Aiyuka-rashin karayar mumuni

shirin zai bayyani kan yadda Allah madaukakin sarki yake tare Bawa daidai yadda ya dauke shi


Masu saurare Assalama aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin kyawawen dabi'un musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, hakika Allah madaukakin sarki baya karya guwar wanda ya kyautata zato a gareishi kamar yadda Hadisai da dama tare da Addu'o'in Ahlulbait(a.s) suka karantar da mu.ba shakka cikin shahararren Hadisi kudsi ,Allah madaukakin sarki na cewa inanan inda bawana yayi zatona.sannan kuma wani hadisin na cewa duk wanda ya baitawa Allah madaukakin sarki da abinda ya fi so to babu shakka daga kyakyawaen zatonsa ne da shi. Haka zalika idan muka dubi tafarkin waliyan Allah musaman ma Annabawa da iyalan gidan Ma'aikin Allah  tsarkaka suma sun tabbatu da wannan kyawawen Dabi'u amma kafin mu zunduma cikin shirin ga wannan.  


 


Musuc***************************************


 


Masu saurare riwayarmu ta farko za tayi dubi ne kan tafarkin shugaban mummunai Imam Ali (a.s), a cikin littafi mai suna Munakibul Imam Ali (a.s) Muhamd bn Suleimane Alkufi ya rawaito hadisi daga Bakri dan Abdul…Mazni yana cewa wata rana Imam (a.s) ya kira wani Bawa daga cikin bayinsa sai yaki amsawa, yayin da ya fito sai ya same shi a kofar Gida sai ya tambayesa minene ya hana shi amsa kiran nasa? Shin  baka ji kiran da naimaka? Sai wannan bawa yace hakika naji saidai kasala ta kamani ne ba amsa kiran naku ba kuma ba shakka na yi imanin cewa ba za kuyi muni uguba ba, sai Imam Ali (a.s) yace Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya ni daga cikin wadanda bayinsa ke kyakyawan zato a gareishi don haka kaje na intar da kai saboda Allah maduakakin sarki.


Masu saurare riwayarmu ta gaba za tayi dubi ne kan tafarkin  jikan imam Ali(a.s) wato shugabanmu Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin (a.s) cikin riwayar da sheik Mufid (r.a)  ya rawaito a littafinsa mai suna Kitabul Amaly inda riwayar ke cewa wata baiwa daga cikin Bayin Imam (a.s) ta kasance tana zubawa Imam (a.s) ruwan alwalla  shi kuma yana Alwallah sai abin ruwan ya kubce daga hanunta ya fada a fiskar Imam (a.s) har ya samu rauni sai Aliyu bn Husain (a.s) ya daga fiskarsa ya galleta sai wannan baiwa tace Allah madaukakin sarki yana cewa  "وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ wato da masu hadiye fishi sai Imam (a.s) yace mata Hakika na hadiye fishina sai Baiwar ta ci gaba da cewa وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ".wato da masu yafiya ga Mutane  sai Imam (a.s) yace hakika na yafe maki har ila yau baiwar tace وَاللّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ"wato Allah yana son masu kyautatawa ,Imam (a.s) yace mata ta tafi ya intar da ita.


 A bangare guda kuma mun san cewa babu shakka Allah madaukakin sarki ba ya kama bayinsa a kan laifin da suka  aikata bisa kuskure wanda hakan ke tabbatar mana da Adalcin ubangijinmu gami da karamcinsa , riwayarmu ta gaba shugabanmu Imam Zainul Abidin (a.s) ya tabbatar mana da irin wannan karamci , a cikin littafin Matalibi Su'ul babe na yabon iyalan Gidan Ma'aikin Allah tsarkaka a riwayar da sheik Muhamad bn Talha (r.a)wanda ke nuna karamcin shugabanmu Imam Zainul Abidin (a.s) inda a cikin wannan riwaya aka ce wata rana  Imam (a.s) ya samu baki sai daya daga cikin khadiman sa ya gaggauta zuwa gasa Nama a Tanda  saboda wannan baki, yayin da ya dauko wannan Nama  a abinda ake gasa Nama  a Tanda yana gaggawa don ya kaiwa Bakin Imam(a.s) sai madaukin Naman ya kubce  daga hanunsa sannan ya fada Kan Dan Imam Aliyu bn Husain(a.s)  sandiyar hakan sai ya rasu ,bayan haka Imam(a.s) yacewa wannan khadimi yayin da yake karkarwa don tsaro ,kaje na intar da kai domin ka aikata hakane don kuskure ba don san ranka ba.sai Iman ya dauki Dansa yayi masa suttura.


 


Musuc****************************************


 


Hakika Allah madaukakin sarki ba ya banbata bayinsa sai ta hanyar tsoron Allah da kuma kyawawen aiyuka wanda kuma hakan ya sha bambam idan muka dubi rayuwar Mutanan yanzu wanda karamci ko fifiko ya ginu a kan Dukiyar Mutune  ko kuma asalinsa ma'ana idan kaga Mutane na girma maka a yau imam ko kanada Dukiya ko kuma kai Dan wani ne.Allah madaukakin sarki na girmama  bayinsa ne sakamakon tsaron Allah ko kuma kyawawen aiyukansu haka zalika Allah ya hana aikata zalinci ko min kankantarsa domin baya shiryen da Azzalimai kuma yayi hani da a  taimakonsu.idan muka dubi irin wannan kyawawen dabi'u za muga  cewa sun tabbatu  ga waliyansa  musaman iyalan gidan Manzon Rahama tsarkaka. Babban misdakin wadannan kyawawen Dabi'u za mu koya a tafarkin shugabnmu Imam Bakir (a.s) a matsayin na mai Nasiha a riwayar da Sheik Kashi ya rawaito cikin Littafinsa mai suna Kitabu Rijal daga Ukaba bn Bashir Al'asadi yana cewa: na shiga wajen babban Ja'afar Imam Bakir (a.s) sai nace masa ya Dan Ma'aikin Allah ni inada matsayin mai girma tsakanin Al'ummata kuma Al'ummar ta mu ta nada shugaba ko kuma wanda yake wakiltar ta a masaurauta sai ya mutu, bayan mutuwar tasa sai Al'ummar ta mu ke son maye gurbinsa  da ni wato ya zamanto shine wakilinsu a wajen sarki sai ya tambaye Imam (a.s) ra'ayinsa shin ya amince da wannan mukami ko kuma a'a sai Abu Ja'afar (a.s) yace masa: idan kana fatan jin ra'ayinmu ne a kan hakan , to da farko dai kasan cewa Allah madaukakin sarki yana daukaka  imanin wanda Mutane suka kiransa wanda ba kowa ba idan ya kasance Mumuni,sannan kuma dagawa ta kafirci na karuwa ne ga wanda Mutane ke ganinsa babba ko mai matsayi a cikinsu idan ya kasance kafiri, kasani cewa babu wani wanda yafi wani a wajen Allah madaukakin in ba da tsoron Allah ba,amma firicinka na cewa na cewa Al'ummarku ta nada shugaba ko wakili wanda yake wakiltarta a masarauta sai ya mutu kuma suna so su zabe ka domin ka maye gurbinsa  a masarauta, idan baka son Aljanna ko kana kiyayya da ita to ka yarda da bukatar Al'ummarka, ka zamanto dan koren ja'irin sarki sannan kuma mai yuyuwa ba bu wani amfani da zaka iya samu ko da na  duniya ne.


 


Musuc******************************************************


 


Masu saurare muna rokon Allah madaukakin sarki da ya arzitamu da biyayya tare da yin koyi  ga waliyan bayinsa makusanta musaman ma iyalan gidan Manzon Rahama tsarkaka.kuma a nan shirin namu zai dasa aya sai kuma a wata fitowa idan Allah ya yarda ,a madadin wanda ya hada sautin a ka saurare ni jagoran shirin nake muku fatan Alkhairi wassalama aleikum warahamatullahi wa barka tuhu