Mar 04, 2016 14:29 UTC
  • zababun Aiyuka-Hadiye fishi

shirin zai yi bayyani ne kan mahimancin hadiye fishi


Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin na yau ci gaban shirin da ya gabata ne, inda a ba'amanta ba a makun day a gabata mun kawo muku Ayoyin Alkur'ani da kuma na Ma'aikin Allah gami da na iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da mahimancin hadiye fishi, shirin nay au ma zai dora ne daga inda muka tsaya a baya  sai a biyo mu domin jin abinda shirin nay au ya kumsa amma kafin  nan, bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.


 


Musuc**************************************************


 


A Cikin Littafin Sharhin Nahjul Balaga na Sayyid Sharif Rida (RTA) an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa(babu wata Gorzantaka da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa kamar hadiye fishi yayin da rai ya bace) Sayyid Sharif Rida ya yi ta'aliki a kalkashin wannan hadisi inda yake cewa a wannan hadisi an ambaci Gorzanta mai tasiri gaske, wacce idan Bawa yayi ta zai samu sakamako mai kyau duk da cewa mutune sai ya daure kafin ya iya irin wannan juriya


A Cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s)inda yake cewa Dansa ya Dana babu wani abu wanda ya fi farantawa Ma'aifinka Rai kamar hakuri da kuma hadiye fishi yayin da Rai ya bace).


har ila yau a cikin wannan littafin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa: (babu wata Gorzanta da bawa zai yi kuma ya samu babban sakamako daga wajen Allah madaukakin sarki kamar Hadiye fishi lokacin da rai ya bace a yayin  zuciya ke kokonto ta dauki fansa ko kuma tayi hakuri, a wannan lokaci sai bawa ya yi Gorzantaka ya fifita yin hakuri tare da hadiye fishinsa kuma ya mayar da komai ba komai ba ba shakka wannan zai samu sakamakon mai kyau a wajen mahalicinsa).


hakika hadisai da dama sun yi bayyani dangane da mahimancin  hakuri da kuma hadiye fishi yayin da Rai ya bace sannan kuma ya bayyana irin kyakkyawan sakamako dake tattare da wannan aiki mai albarka kuma hakuri tare da hadiye fishi na sanya mai shi samun izza da buwaya gami da daukaka a tsakanin Mutane a Duniya da kuma samun izza a Lahira, a cikin littafin Tuhful Ukul na Ibn Shu'ubatul Bahrani yardar Allah ta tabbata a gareshi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) na cewa:( abu uku wanda ya kasance ya nada su zai kasance shugaba, na farko mai hadiye fishinsa a yayin da Rai da bace, na biyu yin afuwa da yafiya ga mumunan abu sai kuma na uku sada zumunci ga 'yan uwa da abokanai tare da taimakawa wadanda suka yanke zumuncinsu a gareshi).


 


Musuc**************************************************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a cikin littafin Kafi Sikatu Islam kulaini ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa:(babu wani Bawa da zai hadiye fishinsa yayin da ransa ya bace sai Allah madaukakin sarki ya kara masa Izza a Duniya da Lahira kuma Hakika Allah madaukakin sarki na cewa:(wadanda suke ciyarwa cikin halin yalwa da guntsi ,da masu hadiye fushi, da masu yafewa Mutane, Allah kuwa yana Son masu kyautatawa.)suratu Ali Imran Aya ta 134 bayan kuma ya karanto wannan Aya Sai Imam (a.s) ya ci gaba da cewa kuma sai Allah madukakin sarki ya saka masa da Aljanna a madadin hadiye fishinsa da yayi).


a cikin littafin Mishkatul Anwar na Sheik Tabrasi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yana cewa: (duk Mutuman da aka zalunta kuma aka kaddara zai rama zaluncin da aka yi masa sannan bai rama ba, Allah madaukakin sarki zai canzamasa da Izza a madadin hakurin da yayi na kin ramawa).


aksin wannan riwaya kuma duk wanda ba ya iya hadiye fishinsa a yayin da Ransa ya bace zai fada cikin kaskanci da kuma tsangoma na Makiya. a cikin littafin Kanzul Fawa'id an ruwaito wani bangare na wasiyar Lukmanul Hakim (a.s) da yayiwa Dansa, a cikin wannan Wasiya Lukamanul hakim (a.s) na cewa Ya Dana duk wanda yake son yardar Allah to dole ya sabawa Son Ransa, duk wanda bai sabawa son ransa ba, ba zai hadu da yardar Ubangijinsa ba, kuma duk wanda ya kasa hadiye fishinsa to zai fuskancin muzguna da kuma dariyar makiya).


daga karshe masu saurare bari mu kawo muku wani kauli da Sheik Muhamad Salih Almazandarani a kan hadiye fishi yayin da Rai ya bace,a cikin littafinsa na Sharh Usulul Kafi shek na cewa Hakika Hadiye fishi yayin da Rai ya bace wata falala ce mai karfi da Allah madaukakin sarki ya baiwa bayinsa mumunai kuma na daga cikin girman daukaka na Adamtaka).


 


Musuc**************************************************


 


Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah, a madadin wadanda suka hada shirin musaman ma Injeniyanmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.