zababun Aiyuka-Mahimancin hadiye fishi
Shirin zai yi bayyani dangane da mahimancin hadiye fishi tare da irin kyawawen sakamokon dake tattare da shi
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka da suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayyani dangane da mahimancin hadiye fishi tare da irin kyawawen sakamokon dake tattare da shi, domin mahimancin wannan maudu'in shirin na Yau ma zai ci gaba daga inda muka tsaya a shirin da ya gabata, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.
Musuc**************************************************
Masu saurare shirin na yau zai farada kaolin Allama Sayyid Ali Khan Almadani Alshirazi a cikin littafinsa mai suna Riyadu Salikin Fi Sharhi Sahifatu Sayidu Sajidin) yayin da yake sharhi kan isharar da Imam Sajjad (a.s) yayi na nemam wannan kyakkyawar dabi'a daga Allah madaukakin sarki , Sayyid Ali Khan yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ce ma'anar hadiye fishi shine idan Mutune yayi fishi, to ya danne fishinsa a ransa ba tare da ya firta wata magana ba wacce ke nuna ya ya fishi. ko kuma ya aikata wani abu wanda ke nuna fishinsa a zahiri ko ya bayyana fishin a fuskarsa ko makamancin haka, wannan shi ake kira da hadiye fishi kuma wannan kyakkyawar dabi'a na daga cikin dabi'u kyawawa wanda Allah madaukakin sarki yayi ishara da su a cikin Alkur'aninsa mai tsarki kamar haka:( wadanda suke ciyarwa cikin halin yalwa da guntsi ,da masu hadiye fushi, da masu yafewa Mutane, Allah kuwa yana Son masu kyautatawa.) suratu Ali Imran Aya 134 sayyid ya ci gaba da cewa bayan wannan aya hadisai da dama sun ishara a kan wannan kyakkyawar dabi'ar.
hakika masu saurare wanda Allah madaukaki ya bashi ikon yafiya gami da hadiye fishinsa yayin da aka yi masa wani laifi, zai gudanar da rayuwarsa cikin konciyar hankali wacce ta nisanta da bacin rai gami fishi da kuma daukan fansa, a cikin littafin Mishkatu Anwar na shek Tabrasi an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(wanda ya fi kowa hankali daga cikin Mutane,shine wanda ya fi kowa isa siyasa wajen tafiya da al'umma kuma wanda ya fi daurin kai daga Mutane wanda ya fi su hadiye fishinsa yayin da rai ya bace).
har ila yau hadiye fishi yayin da Rai ya bace ya kan sanya Mutune ya kai ga samun daya daga cikin rukunan kamalar Imani, a cikin Littafin Almahasin na shek Barki an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(ababe guda uku duk wanda ya kasance yanada su Imaninsa ya kammala, na farko wanda idan ya amince da wani abu to ba zai yarda ya sanya yardar nan tashi cikin bata ba, na biyu wanda idan yayi fishi to ba zai yarda fishin nan nashi ya fitar da shi daga tafarkin gaskiya ba, na uku kuma wanda idan yayi rashi baya daukan na waninsa).
Musuc**************************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da Hadisin shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) inda a cikinsa yake siffanta hakikanin mumuni.a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) na cewa:(mumuni shine wanda yake aiki da damar da Allah madaukaki sarki ya bashi, mai hadiye fishi yayin da rai da bace, kuma mai kyawawen dabi'u).
A cikin littafin Khisal na shek Saduk an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) na cewa:( ababe guda uku duk wanda ya kasance yanada su Imaninsa ya kammala wanda yayi hakuri bisa zalunci kuma ya hadiye fishinsa yayin da rai ya bace kuma ya meda komai ba komai ya yafe ya kuma yi gafara, zai kasance daga cikin wadanda za su shiga Aljanna ba tare da hisabi ba,kuma su hadu da ceton Allah yayin da suke cikin matsatsi da yalwa).
Hakika shek Saduk yardar Allah tabbata a gareshi ya ruwaito wasiyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ga shugaban wasiyai da mumunai Aliyu bn abi talib (a.s) a cikin Littafinsa mai suna Man La Yahduruhul Fakih, Ma'aikin Allah na cewa:(Ya Ali zan yi maka wata wasiya sai ka kiyayeta kuma idan har ka kiyaye ba shaka ba zaka gushe daga Alheri ba, Ya Ali duk wanda ya hadiye fishinsa yayin da yake da ikon ramawa kuma ya yafe, hakika Allah madaukakin sarki zai saka masa da aminci ranar Alkiyama kuma zai dandana masa dadin Imaninsa)
har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) na cewa:(duk wanda ya hadiye fishinsa a yayin da yake da ikon ramawa kuma ya yafe Allah madaukakin sarki zai kiyaye zuciyarsa daga duk wani sabo kuma a bashi cikekken aminci da kuma imani ranar alkiyama).
Daga karshe masu saurare bari mu karanto wannan hadisi na shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) wanda sikatul Islam kulaini ya ruwaito a cikin Littafinsa mai suna Alkafi inda a cikin sa Imam (a.s) ke cewa:(duk wanda ya hadiye fishinsa yayin da aka bata masa rai kuma yaga dama ya yafe domin yanada iko ramawa , Allah madaukakin sarki zai sanya masa yardarsa a zuciyarsa kuma ya bashi babban sakamako ranar Alkiyama).
Musuc**************************************************
Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah, a madadin wadanda suka hada shirin har ya kammala musaman ma Injeniyanmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.