Hakuri mai Kyau
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyani kan kyakkyawar dabi'ar Hakuri mai kyau, wannan dabi'a mafi girman martaba na kyawawen dabi'u har ma ana kiran sa da Shugaban Imani, kuma Mine ne ke banbanta dabi'ar kyakkyawan Hakuri da kuma dabi'ar Hakuri? Domin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
************************Musuc*******************************
Masu Saurare Hakika Allah madaukakin sarki ya yabi wannan kyakkyawar dabi'a na Hakuri mai kyau bisa harshen daya daga cikin Annabawansa tsarkaka shi ne Annabi Yakubu (a.s), A cikin Alkur'ani mai tsarki Aya ta 83, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ya ce: Ba haka ba ne, Zuciyarku dai ta kawato muku wani abu.Hakuri kawai mai kyau kawai shi ya fi(gare shi).Ina kaunar Allah ya kawo min su gaba daya, Hakika shi ne Masani mai hikima), Hakika Annabin Allah mai girma ya dabi'antu da dabi'ar Hakuri mai kyau bayan da fadakarwar Ubangiji mai tausayi madaukakin sarki, Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya bayyana cewa a yayin da Jabir Ju'ufi yardar Allah ta tabbata a gare shi ya tambaye shi kan Ma'anar Hakuri mai kyau sai ya sanar da shi da daya daga cikin misdakinsa ya kuma nakalto hakurin Annabi Yakubu (a.s), Shekh muhamad bn Hamam Iskafi wanda yay i zamani da Shekh Kuleini yardar Allah ta tabbata a gare su cikin Littafin sa mai suna Altamhis (التمحيص) ya ruwaito hadisi daga Jabir Ya ce na cewa Babban Jabir Imam Bakir (a.s) mi ake nufi da Hakuri mai kyau?Ya ce shi ne Wannan Hakurin da ba a kai kuka wajen wani mutum daga cikin Mutane).Sannan Imam (a.s) ya ci gaba da bayyana hikayar abinda ya faru tare da wannan Annabi (watau Annabi Yakubu a.s) ya kuma sanya ya dabi'antu da dabi'ar Hakuri mai kyau:sai Ya ce:Annabi Ibrahimu ya aiki Ya'akub zuwa wajen malami daga cikin Maliman Lokacinsa dangane da wata Bukata, a yayin da wannan Malami ya gansa sai yay i zaton cewa Annabi Ibrahimu ne sai yay i tsalle ya rungume shi sannan ya ce masa barka da zuwa ya kai Khalilun Rahaman, sai Annanbi Yakubu ya ce masa Ni ba Khalilul Rahaman ba ne, saidai Ni Yakubu dan Ishaka dan Ibrahimu ne, sai Malamin ya ce masa Mi nene yake damunka har nake gani ka yi saukin girma haka? Sai Annabi Yakubu ya ce Damuwa, bacin Rai da kuma rashin Lafiya. Sannan Sai Imam Bakir (a.s) y ace Annabi Yakubu bai fice kofar gidan Malamin nan ba sai da Allah madaukakin sarki yay i masa wahayi yana mai cewa Ya Kai Ya'akub ka kai kara na ne wajen Bayi? Sai Annabi Yakubu (a.s) ya fadi ya yi sujada yana neman Gafara yana cewa Ya Ubangiji b azan kara ba, ba kuma zan sake aikata wannan laifi ba, Sai Allah madaukakin sarki ya yi masa wahayi ya ce masa Hakika na yi maka gafara kadda kuma ka sake aikata irin wannan Laifi.Imam Bakir (a.s) daga wancan Lokaci Annabi Yakubu bai kara kai kukansa ba zuwa wani mahaluki a Duniya har lokacin da wata Rana ya ce:( Ya ce:"Ni fa lallai kawai ina bayyana takaicina ne da bakin cikina zuwa ga Allah, kuma ina sane da abin da ku ba ku sani ba game da Allah) suratu Yusufu Aya ta 86 har ila yau Masu saurare irin wannan kyakkyawan hakuri shi ne ya yi tajjali cikin fadar Shugabarmu Sayyida Zainab (a.s)a yayin fuskantar rundunar Ubaidunllahi bn Ziyad,a yayin da aka tambaye ta mi za ta ce dangane da abinda aka aikatawa Dan Uwanta Imam Husain (a.s) a Karbala'a sai ta amsa da cewa babu abinda abinda na gani face kyau, kuma wannan shi ne mafi kyau na martabar tauhidi da kuma tsarkakarsa.
********************Musuc***********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar Musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai yi bayyani kan kyakkyawar dabi'ar boye damuwa da kuma rashin kai koke ga wani) Hakika Babban Malamin nan Hurrul-Amuly yardar Allah ta tabbata garesa cikin Littafin sa mai suna wasa'ilu Shi'a ya ware babe guda dangane da wannan dabi'a wanda ya bashi suna Mustahabin ne a boye rashin Lafiya ko kuma Damuwa da kuma rashin kai koke wajen wani dangane da hakan watau dangane da ibtil'I na rashin Lafiya ko damuwa da wani Mutum ya hadu da jarabtu da shi, a cikin wannan Babe ya kawo riwayoyi masu da suke bayyani kan Istihbabi na boye damuwa da kuma rashin lafiya gami da rashin kai koke ga Mutane, hadisai da dama sun bayyana cewa karancin yi kuka ko kai koke ga wani bisa wani Ibtila'I na daga cikin kyawawen dabi'u na Mumunai, kamar yadda ya zo cikin Khudubar Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) yayin da yake bayyana siffofin Mumunai wacce aka ruwaito a cikin Littafin Kafi na Sikkatu Islam Kulaini, Imam (a.s) ya ce:(ba ya wulakanta sirri, bay a kuma bayyana sirri, mai yawan jarabtuwa da Musiba, mai karamcin kai koke, idan ya ga Alheri sai ya bayyana, idan kuma ya ga wani Sharri sai ya boye shi, yana suturta aiki yana kuma kiyaye gaibi, yana kuma rage ambaton bala'I, ya kuma yi gafara ga gaskanci) har ila yau Imam (a.s) yayin da ya siffanta Dan Uwansa kuma yana yabonsa kamar yadda ya zo cikin Littafin Nahjul-Balaga ya ce:(kuma ya kasance ba ya kai koke ga wani dangane da wani ciwo face wajen Ubangijnsa), Masu Saurare Dabi'antuwa da dabi'ar boye Ibtila'I da ku rashin kai koke wajen wani yana samar da sakamako na samun sauki ga bala'in da zai saukarwa Bawa da kuma samun kariyar Allah madaukakin sarki daga Bayinsa, Hakika cikin Littafin Jami'ul-Akhbar, an ruwaito wani Hadisi inda a cikin sa Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s)yake yiwa daya daga 'ya'yansa ya ce:(Ya Kai Dana,duk wanda ya boye wani bala'I da ya jarabtu da shi daga wajen Mutane, kuma ya meka koken sa zuwa ga Allah madaukakin sarki, Hakki ne ga Allah da ya yaye masa wannan Bala'i), Kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da wannan kyakkyawar dabi'a, rabauta da gafarar Ubangiji, Hakika Kadi Nu'uman Almagribi ya ruwaito Hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Maras Lafiya na cikin kangin Ubangiji ana shafe masa zunubansa matukar dai bai kai kokensa ba zuwa ga wadanda suke zuwa gaida shi ba), kamar yadda Hadisin Kudusi wanda aka ruwaito cikin Littafin Kafi yay i mana Albishir da cewa Allah madaukakin sarki yana canzawa mai wannan dabi'a Bala'I zuwa ga Ni'ima, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Allah madaukakin sarki ya ce:duk bayan da ya jarabtu da wata rashin lafiya ya kuma boye wannan ibtila'I ga masu zuwa gaishe da shi so Uku, Allah tabaraka wa'ala zai canza masa Naman cikinsa jininsa da kuma fuskarsa zuwa mafi alheri,idan kuma na barshi, na barshi, bas hi kuma da wani zunubi, idan kuma ya mutu, ya koma zuwa ga Rahamata) da fatan Allah tabaraka wa ta'ala ya arzuta mu da wannan kyakkyawar dabi'a dan albarkar riko da wulayar iyalar gidan Anabta tsarkaka.
*************************Musuc******************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.