Mar 04, 2016 15:23 UTC
  • zababun Aiyuka-Dangana da abin da ke hanunka

shirin na yau zai yi bayyani ne kan nisantuwa da rogo kuma tambaya a wajen Mutane


Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan nisantuwa da rogo kuma tambaya a wajen Mutane , sai a biyo mu domin jin abinda shirin ya kumsa.


************************Musuc*************************


Masu saurare a cikin suratu Bakara Aya ta 273 Allah madaukakin sarki ya ce:(ku fifita ciyarwar) ga fakirai wadanda suka tsare kansu saboda Allah, bas a iya yawatawa cikin Kasa (don neman abinci har) wanda bai sani ba ya rika tsamanin su mawadata ne domin kamewarsu, ba sa naciya wajen rokon Mutane.Abin da kuka ciyar na alheri, hakika Allah ya na sane da shi) a cikin Tafsiru Kummy na Aliyu bn Ibrahim an ruwaito hadisi daga Imam Ma’asum (a.s) ya ce (fakirai sune wadanda ba sa tambayar mutane duk da cewa su nada bukatar abinda za su ciyar da iyalansu sannan sai ya karanto wannan Ayar da ta gabata). A cikin Tafsiru Majma’ul bayyan shek Tabrasi ya ce hakika Allah yana son ganin tasirin ni’imarsa a kan bayinsa, kuma yana gyamar ganin mai kaskantar da kansa  sannan ya na son mai hakuri, mai kamiya daga cikin bayinsa, kuma ya na fishi  ga fasiki mai yawan Alfahasha, mai yawan tambaya da yawan rantsuwa).  Masu saurare hadisai da dama sun umarci mumunai da su kiyayi rogo tambaya daga wajen mutane ko da ma yana cikin larura, Allah madaukakin sarki ya son bawa ya mika bukatunshi kawai wajensa ba wajen mutane ‘yan uwansa ba,a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare iyalan gidansa tsarkaka na cewa :(ku kiyaye rogo ko kuma tambayar Mutane daidai golgodo) har ila yau a cikin littafin Ma’anil Alkhbar na shek Saduk an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (SAW) ya ce:(duk wanda ya budewa kansa Baben Tambaya ko kuma rogo , Allah zai buda masa kofofi saba’in na talauci babu abinda zai iya toshe ko karamarsu daga ciki).maluman Hadisi sun fassara wannan hadisi da cewa duk wanda ba ya nisantar rokon mutane Allah madaukakin sarki ya sanya ya dinga jin talauci a dukkanin al’amuransa har da daga ababen da yake samu da kuma abinda yake so), Imam Bakir (a.s) ya ce :(neman bukatu a wajen mutane yak an kawar da daukakar dan adam da kuma kawar da kunya, kawar da kai da abinda ke hanun Mutane daukaka ce ga mumunai, kwadai kuma shine talaucin yau). shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(na galgadeku da rokon Mutane domin shi kaskanci a duniya kuma   talauci ne kuke gaggauta kira, kuma yana da dogon hisabi a ranar Alkiyama). Har ila yau a wata riwayar kwa da aka ruwaito  cikin littafin Wasa’il Imam (a.s)  ya ce:(Allah ya ji kan Bawan da ya nisantar da kansa kuma nisartar da Jama’a daga rogo ya kuma rike mutuncin daga tambayar Mutane).a bangare guda wani hadisin kuma yayi umarni da a nisanci tambayar makiya Ahlulbait (a.s) a cikin littafin Kafi, Imam Sadik (a.s) ya ce :(hakika mabiyanmu ‘yan shi’a ba sa kodayi  kamar irin kodayin hankaka, kuma ba sa tambayar makiyanmu ko da za su mutu  da yinwa).


***********************Musuc***************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne  kan mahimancin dogoro da kuma tabbaci ga Allah madaukakin sarki.Nasossi da dama sun yi bayyanin cewa Dogora da kuma tabbaci ga Allah shi ke  sanya dan adam ya dandana dadin  imani da  nisantar  kodayin abinda ke hanun Mutane tare  kuma meka al’amuransa zuwa ga Allah madaukakin sarki.ma’anar wannan dabi’a shine dan adam ya kasance a dukkanin al’amuransa da kuma mu’amalarsa wacce ya kayi yau da kula bisa imanin cewa hakika Allah mai tausayi  kuma mai hikma ne dukkanin al’amura gaba daya suna hanun Allah madaukakin sarki kuma shine mai amfanarwa   kuma mai cutuwar  wa, ba ya yi mutune wani abu sai abinda ya kasance maslaha a gareshi. A cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Amiru mumunin Aliyu bn abi talib (a.s)yace :(Bawa ba zai samu dandanon imani ba har sai ya sa san cewa babu wani wanda zai iya cutar da shi mai cutarwa ko amfanarwa shine  Allah madaukakin sarki). Masu  saurare tabi’antuwa da irin wadannan kyawawen dabi’u ya kan samar wa mumuni karfin Zuciya wajen tunkarar wahalhalu na duniya, domin yakininshi  da kuma tabbacinci ga Allah ya kan sanya shi ba ya tsoron kowa idan ba Allah madaukakin sarki ba,a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Abi Basir daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce :(babu wani  abu a duniya face yanada Haddi,sai Abu Basir ya ce na cewa Imam (a.s) fansar kaina a gareka minene hadin dogoro? Sai Imam (a.s) ya ce hadin dogaro shine yakini   ko kuma tabbaci ga Allah madaukakin sarki sai nace masa shi kuma tabbacin ko yakinin ga Allah minene hadin sa? sai Imam (a.s) kada ka ji tsoron komai tare da Allah madaukakin sarki).har ila yau a cikin littafin na kafi an ruwaito hadisi daga imam Sadik (a.s) ya ce:(daga cikin sahihancin tabbaci ga Allah kada musulmi ya yardewa mutane fishin ubangiji, kuma kada ya zarke su kan abinda Allah ya basu, domin shi arziki ,makon mai mako  ba ya kawo sa, haka nan  kashin mai kashi ba ya kawar da shi, da dayanku zai kujewa arzikinsa kamar yadda kuke kujewa Mutane, da ya riske sa  kamar yadda mutuwa za ta riske ku,hakika Allah madaukakin sarki da adalcinsa ya sanya wa zukata hutu a cikin  tabbaci da kum yarda  sannan ya sanya bacin rai da damuwa a cikin shakku da fishi), masu saurare kamar yadda muka saurara a hadisin da ya gabata, dabi’antuwa da kyawawen dabi’u na tabbaci ga Allah da kuma kyakkyawan zato a gareshi yak an sanya mumuni ya samu Raha  da nutsuwa a cikin zuciyarsa kamar yadda Imam Sadik (a.s) ya bayyana, kuma hakan   babban rabo ga shi mumunin. Har ila yau  wannan lamari ya kan sanya aiyukansa su zamanto karbabbu a wajen Allah madaukakin sarki kamar yadda yake samun damar ci gaba da aiyukansa saboda albarkar tabbacin da gareshi tare da Allah madaukakin sarki, a cikin littafin Ilalu Shara’I’I na shek Saduk an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa:( Hakika dawamma kan aiki kadan bisa tabbaci ko kuma yakini ya fi aiki mai yawa wanda babu yakini a cikinsa wajen Allah madaukakin sarki).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon samun wadannan kyawawen dabi’u masu albarka.


**********************Musuc*******************************


Masu saurare a nan za mu dakata ganin lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala ni da shirya kuma ya gabatar nike muku fatan alheri wassalama alekum warahamatullahi ta’ala ba barkatuhu.