zababun Aiyuka-Neman Gaskiya
shirin na yau zai yi bayyani ne kan neman gaskiya tare da kaskantar da kai a gabanta, ma’ana shine ya kamata ko wani Mutune ya yi iya kokarinsa wajen nemam gaskiya, idan kuma ya gano ta to ya yi biyayya a gareta shin ta yi daidai da ra’ayinsa ko kuma ta sabawa ra’ayinsa,
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan neman gaskiya tare da kaskantar da kai a gabanta, ma’ana shine ya kamata ko wani Mutune ya yi iya kokarinsa wajen nemam gaskiya, idan kuma ya gano ta to ya yi biyayya a gareta shin ta yi daidai da ra’ayinsa ko kuma ta sabawa ra’ayinsa, yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa tare da yi wa masu albishir na kyakkyawan sakamako a nan duniya da Lahira.
**************************Musuc***************************
A cikin littafin Kafi na sikkatu islam kulaini an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) daga cikin irin wasiyoyin da ya yiwa salihin bawan nan Hisham bn hakam ya ce :(Ya Hisham hakika Allah ya yi albishir ga ma’abota hankali da fahimta a cikin littafinsa mai girma sannan sai ya karanto wannan Aya:( to ka yi wa bayina albishir*wadanda suke jin magana sannan su bi mafi kyawunta ,wadannan su ne wadanda Allah ya shiryar,kuma wadannan su ne ma’abota hankula) suratu Zumari Aya ta 17 da kuma ta 18.sannan Imam (a.s) ya ci gaba da cewa Ya hisham hakika Lukmanul hakim (a.s) ya ce wa Dansa Ya kai Dana ka kaskantar da kanka a gaban gaskiya sai ka zamanto mafi hankali daga cikin al’umma). Masu saurare abinda za mu fahimta a wadannan ayoyi masu albarka da kuma kaolin Imam Kazim (a.s) shi ne dabi’antuwa da dabi’ar amincewa da gaskiya daga da kaskantar da kai a gabanta wanda hakan shi zai sanya dan adam ya amfanu da ni’imar hankalinsa, kuma hakan shi zai sanya ya cimma kurinsa na samun kyakkyawan rabo a duniya da lahira.
A cikin littafin Sawabul a’amal an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s): (duk wanda ya kasance mai hankali ya nada Addini, kuma duk wanda yake da addini zai shiga Aljanna), a bangaren guda kin bin gaskiya da kuma kin amincewa da ita yak an jefa mutune cikin kaskancin kabilanci wanda zai kai mutune ga hallaka har ya kaisa ga shiga wuta,a cikin littafin Ikabul A’amal na shek Saduk an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya yi ta’asubanci ko kuma kabilanci Allah madaukakin sarki zai tayar da shi ranar alkiyama tare da larabawan lokacin jahiliya). Har ila yau a cikin kafi an ruwaito daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk mai kabilanci ko kuma wanda ake kabilanci saboda shi kuma bai hana ba , ba shakka ya ajiye ikiyar imanin dake rataye a wuyansa).har ila yau a wata riwayar Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce (duk wanda ya kasance a kwai kwayar zarra na kabilanci a zuciyarsa Allah madaukakin sarki zai tayar da shi ranar alkiyama tare da larabawan lokacin jahiliya).
A cikin Littafin Nahjul Balaga Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(Ya ku Mutane hakika ina yi muku tsoron ababe guda biyu, bin son rai, da kuma dogon guri, domin son rai ya na toshe ganin gaskiya da kuma binta, shi kuma dogon guri yak an sa a manta da Lahira).
***************************Musuc**************************
Masu saurare barkanmu da sake sduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimancin kyakkyawan zaton Bawa ga mahalicinsa wato Allah madaukakin sarki, domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so ga bayinsa, a cikin littafin Almahasin sheik Ahmad bn Abdullah Albarki ya ruwaito hadisi daga shugabanmu imam Sadik (a.s) ya ce:(ranar Alkiyama za a zo da bawan da ya zalinci kansa, sai Allah madaukakin sarki ya ce masa shin ban umarce ka da yin da’a a gareni ba, shin ban hane ka da saba mani ba, sai wannan Bawa ya ce hakika ya ubangiji ka umarceni da na bauta maka kuma ka haneni da na saba maka sai dai na bi son rai na, idan ka yi mani Azaba, ba shakka hakan ya kasance sakamakon zunubaina ne, sai Allah madaukakin sarki ya bada umarni a fice da shi zuwa Wuta, sai wannan Bawa ya ce Ya Ubangiji zatona a kanku bai kasance hakan ba, sai Allah madaukakin sarki ya tambayeshi minene zatonka a gareni? Sai wannan Bawa ya ce ina da kyakkyawan zato a gareka? Sai Allah madaukakin sarki ya bada umarni da a sanya shi Aljanna, sannan sai Allah madaukakin sarki ya ce hakika kyakkyawan zatonka a gareni ya amfanar da kai a wannan Rana ta Alkiyama). A cikin Littafin Uyunul Akhbarir Rida an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:( ku kyautata zato ga Allah domin Allah madaukakin sarki na cewa:ni ina yadda Bawana yake zatona, kuma babu wani zato da bawana zai yi mani sai na Alheri). A cikin Littafin Mahasin wal sawabul A’amal an ruwaito hadisi daga Imam Sadik(a.s) na cewa:(idan Bawa ya yi kyakkyawan zato ga Allah to ba shakka haka nan zai tarar da shi , haka zalika idan ya yi mumunan zato , haka nan zai tarar da shi, sannan sai Imam (a.s) ya karanto fadar Allah madaukakin sarki:(wannan kuwa shi ne zatonko da kuka yi ga ubangijinku da ya hallakar da ku, sai kuka wayi cikin tababbu) surar Fussilat aya ta 23.
Masu saurare sai a biyo mu domin buda zukatanmu da irin nasihohin shugaban halittu Muhamad dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce mun samu a cikin Littafin Amirur mumunin (a.s) cewa wata rana Ma’aikin Allah (a.s) ya kan minbarinsa ya yiwa Al’ummar musulimi wa’azi kamar haka: na rance da wanda babu wani abin bauta sai shi, ba a bawa wani bawa alherin duniya da lahira ba sai don kyakkyawan zatonsa da kuma fatansa ga Allah, kyakkyawan dabi’unsa da kuma kare kansa daga yin batanci ga mumunai. Na rantse da wanda babu abin bauta sai shi,Allah ba zai azabtar da Baw aba bayan ya tuba kuma ya yi nemi gafara, sai don mumunan zatonsa da shi da kuma kasawarsa wajen kyawawen fata ga Allah madaukaki, munanan dabi’unsa da kuma batanci gami da cin naman mumunai, Na rantse da wanda babu abin bauta sai shi, babu wani kyakkyawan zato da bawa mumuni zai yi wa Allah sai ya tarar da Allah n kamar yadda ya kyautata zatonsa, ku saurara hakika Allah mai karamci ne kuma alheri na gareshi ya na jin kunyar ya sabawa Bawansa mumuni da ya kyautata zato a gareshi, ku zamanto masu kyautata zato ga Ubangijinku da kuma kyakkyawan fata a gareshi) masu saurare da fatan Allah madaukakin sarki ya taimake mu mu kasance daga cikin bayinsa masu kyakkyawan zato a gareshi ta hanyar kyawawen tunani domin mu kasance kalkashin rahamarsa da kuma girmar tausayi da kuma kyautatawarsa.
***************Musuc******************************
Masu saurare a nan za mu dakata ganin lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala ni da shirya kuma ya gabatar nike muku fatan alheri wassalama alekum warahamatullahi ta’ala ba barkatuhu.