zababun Aiyuka-Mahimancin Hakuri
shirin na yau zai yi bayyani ne game da mahimancin hakuri a kan gaskiya
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne game da mahimancin hakuri a kan gaskiya,amma kafin nan bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.
***************************Musuc*****************************
Masu hakuri, wadanda suka dabi’antu da wannan halaye masu albarka sune wadanda Allah madaukakin sarki yake yabonsu a cikin Ayoyi da dama na Alkur’ani sannan ya yi musu albishi da soyayyarsa a garesu tare da taimakonsu saboda hakurinsu kamar yadda allah madaukakin sarki ke cewa(kuma ka yi bishara ga Masu Hakuri) (hakika Allah yana tare da masu Hakuri) (kuma Allah yana son Masu Hakuri)
Masu saurare hakika hadisai da dama sun bayyana cewa daya daga cikin misdakin dabi’antuwa da wadannan kyawawen dabi’u masu albalka , hakuri a kan gaskiya, ma’ana yin hakuri dangane da wahalhalun da Bawa zai fuskanta wajen iltizami da yin biyyaya ga Allah gami da wahalhalun kaucewa sabon Allah da kuma yakar zuciya kan abinda take rayawa Bawa na sabon Allah da kuma sha’awance-sha’awance, haka zalika yin hakuri bisa ibtila’I da jarrabawa wacce Mutune ke fuskanta a rayuwarsa ta yau da kulun wacce kuma ta kana ne idan bawa ya ci jarabawar imaninsa ke cikka. A cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga Ma’ailin allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(hakuri guda uku ne,hakuri da Bawa ya fuskanci wata musiba, hakuri wajen yin biyayya ga Allah, hakuri wajen kaucewa sabon Allah,duk wanda yay i hakuri a bisa wata musiba da ta same shi kuma ya mayar da kyakkyawen martani Allah madaukakin sarki zai rubuta masa Laba dari uku, kuma ko wani lada daga cikin fadinsa ya kai tsakanin dake akwai tsakanin sama da Kasa, kuma duk wanda ya yi hakuri bisa bautar Allah, Allah zai rubuta masa dari shida tsakanin ko wani Lada da dan uwansa fadinsa ko kuma girmansa kamar girmar farkon kasa zuwa karshen Al’arshi, kuma duk wanda yayi hakuri wajen kaucewa sabon ubangiji, Allah madaukaki sarki zai rubuta masa Lada dari tara, wani Lada da dan uwansa fadinsa ko kuma girmansa kamar girmar farkon kasa zuwa karshen Al’arshi so biyu)
A cikin littafin Nahjul balaga, an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce hakuri kala biyu ne hakuri kan abinda kake so da hakuri a kan abinda kake ki, hakika masoyin Annabi Muhamadu (s.a.,w) shine wanda yayi biyayya ga Allah ko da ya yi nisa da kusancinsa, kuma makiyin Allah shine mai sabo komin kusancin dangantakarsa da Annabi) har ila yau a wata riwayar da aka ruwaito cikin littafin Kafi:Imam (a.s) ya ce:(hakuri nau’I biyu ne:yin hakuri yayin da bawa ya fuskanci wata musiba hakuri mai kyau, wanda ya fi kyau shine hakuri wajen kaucewa abinda Allah ya haramta ga bawa,kuma ambato nau’I biyu ne anbaton Allah madaukakin sarki a yayin wata musiba wanda ya fishi kuma shine anbaton Allah yayin da Bawa ya fuskanci fadawa cikin sabon Allah, idan ya ambaci Allah a wannan lokaci zai kasance masa garkuwa )har ila yau a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(a lokacin babana Aliyu bn Husain (a.s) ke gadon mutuwa ya rungumeni a bisa kirjinsa sannan ya ce da ni ya kai Dana zan yi maka wasici irin wanda Babana yayi mani yayin da mutuwa ta riskeshi, daga cikin da yayi masi wasici yace ya kai dana ka yi hakuri a bisa gaskiya ko da ta kasance tana da daci), har yanzu masu saurare muna cikin Littafin Kafi inda zamu karanto wani hadisi da aka ruwaito daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(idan ya kasance ranar Kiyama wasu gungu na mutane za su tashi su je kofar Aljanna sai ace masu su waye ku? Sai su ce mune Ahlin hakuri, sai ace da su? Bisa mi ku kayi hakuri, sai suce mun kasance muna hakuri bisa bautaur Ubangiji da kuma kaucewa sabonsa, sai Allah madaukakin sarki ya ce sun yi gaskiya ku shiga Aljanna, Imam ya ce wannan shine kaolin Allah madaukakin sarki (hakika masu Hakuri ne kawai ake cika wa ladansu ba da lissafi ba) suratu Zmari Aya ta 10.
*****************************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne dangane da mahimancin tsantseni, ma’anar tsantseni shine kaucewa duk wani abu da kan iya jefa bawa cikin sabon Allah kamar yadda shugabanmu Imam Ja’afaru sadik (a.s) ya ce:(hakika Mu ba ma Lissafa mutune cikin mumanai har sai ya kasance yana biyayya ga dukkanin Al’amuranmu, ku saurara yin biyayya ga Al’amuranmu shine mumuni ya zamanto mai tsantseni, ku zamanto masu ado da shi Allah ya yi maku rahama) masu tsantseni shine karfin shahsiyar mumuni da kuma Alamar imaninsa kuma shine a matsayin tsani na farko na kalmar tauhidi ma’ana tsarkaka daga duk wani abin bauta idan ba Allah madaukakin sarki ba,a cikin littafin Man La Yahduruhu Fakih shek Saduk yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ruwaito hadisi daga Masoyin Allah Mustapha (s.a.w) daga cikin wasiyoyin da ya yiwa wasiyinsa Imam Ali(a.s) ya ce :(Ya Ali duk wanda ya jewa Allah madaukakin sarki da ababe guda uku na daga cikin fiyayen mutane, duk wanda ya jewa Allah madaukakin sarki da aiyukan da aka wajabta masa shi ya na cikin wadanda suka bautawa Allah,duk wanda yayi tsantseni daga sabon Allah na daga cikin wadanda suka fi tsantseni daga cikin Mutane, kuma duk wanda ya dangana daga abinda Allah ya arzuta shi da shi hakika shi na daga cikin wadanda suka fi kowa Arziki daga cikin Mutane Ya Ali duk wanda bai kasance ba cikin wadanda suka mallaki wadannan ababe guda aiyukansa ba su cika ba, na farko tsantseni da zai kiyaye shi fadawa cikin sabon Allah, na biyu, kyakkyawar mu’amala da mutane sai kuma hakuri da zai bashi damar mayar da martani ga duk wani jahilcin jahilai, Ya Ali rigar musulinci kumya ce,Adonsa shine kamun kai, daukaka da kuma mutuncinsa shine kyakkyawen aiki, gimshikinsa kuma shine tsantsenin aiyukan da su kai Bawa shiga cikin sabon Allah).
Masu saurare dabi’antuwa da dabi’ar tsantseni wajen kusantar aiyukan da za su kai bawa ya sabawa mahalicinsa da kuma abinda Allah madaukakin sarki ba ya so ga bayinsa ya na bayar da sakamako mai kyau da kuma aiyuka na gari.a cikin littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini an ruwito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da yake yiwa daya daga cikin sahabansa wasiya ya ce (ina yi maka wasici da tsoron Allah, tsantseni da kuma Ijtihadi, kuma ka sani babu wani ijtihadi da zai yi amfani matukar babu tsantseni a tare da shi).
Masu saurare tsantseni wajen kusantar sabon Allah na daga cikin alamomi na mabiyar mazhabar iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka, Imam Sadik (a.s):(hakika sahabina ko kuma mabiyina shine wanda ya tsananta tsantseni, da kuma aiki saboda mahalicinsa, da kuma fatan sakamako a gareshi, masu irin wannan siffa sune sahabaina)
A wata riwayar kuma Imam (a.s) ya ce:(ku kasance masu masu kiran mutane zuwa ga Addini ba tare da bakunansu ba , a ga tsantseni,Salla, Ijtihadi ma’ana kwazo da kuma kokari wajen gudanar da ibda da kuma dukkanin Alheri a gareku, wannan shine hakikanin kira zuwa ga Addini.da fatan Allah madaukakin ya bamu damar aiki da wannan kyawawen dabi’u domin sune Adon bayin Allah salihai domin albarkar ma’aikin Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka.
**************************Musuc********************************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dakata sai a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman Aminu Ibrahim Kiyawa ni madugun shirin nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.