zababun Aiyuka-Kaucewa Gardama
shirin na yau zai yi bayyani ne game da mahimancin kaucewa jayayya da kuma gardama da ba ta da amfani a cikin ko wani hali
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne game da mahimancin kaucewa jayayya da kuma gardama da ba ta da amfani a cikin ko wani hali,amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
****************************Musuc****************************
Hadisai da dama sun yi hani ga yawan jayayya da kuma gardamar da ba ta da amfani musaman ma wacce za ta kai zuwa ga husuma da kuma tashin hankali ko da mutune ya na so ya tabbatar da gaskiyarsa idan jayayyar za ta kai ga tashin hankali to ya kamata Bawa ya kaurace mata domin ya samu rabauta kuma wannan ita ce hanyar samun rabauta na shiga Aljanna,a cikin littafin Kafi , Sikatu Islam Kulaini yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ruwaito wani hadisi wanda sanadinsa yake komawa zuwa Ma’aikin Allah tsira da amincin Alah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(ababe guda uku duk wanda ya riski Allah da su zai shiga daga kofar da yake So:na farko kyakkyawar mu’amala, tsoron Allah yayin bawa ya kebe da kuma lokacin da yake bainar jama’a, sai kuma na uku barin jayayya ko da ya nada gaskiya).masu saurare kaucewa rigima gami da rigingimu na banza na kiyaye imanin Mutune tare kuma da kiyaye zukata daga Ta’asubanci ko wani gami da munafici, a cikin littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Imam Ali (a.s) Ya ce :(na hane ku da jayayya gami da husuma domin su suna bata zukuta tare da sanya mata munafici).har ila yau a cikin littafin Kafin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(nahane ku da yawan fadace-fadace domin yin hakan na shagaltar da zuciya sannan ta gadar mata da nifaki da kuma sanya mata gunci), daga cikin wasicin da ya yi wa daga cikin Sahabansa Imam (a.s) ya ce:(kada ka yi jayayya da mai hakuri da kuma wawa, domin shi mai hakuri duk abinda z aka yi zai kyaleka ka yi ta babatunka ba tare da ya ce maka uffun hark a gaji, shi kuma wawa zai yi ta wahalar da kai har ya cutar da kai).
Masu Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka shine mai gaskiya amincecce Al’ummarsa shine ya yi alkawarin fiyeyyen matsayi a Aljanna ga wanda ya dabi’antu da wadannan kyawawen dabi’u tare kuma da kaucewa yin rigingimu , jayayya gami da fadace-fadace ta ko wani hali.a cikin litattafan Attauhid da kuma Alkhisal na shek Saduk an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:( ni ne shugaba, nay i wa lamuni da gida a cikin mafi girman matsayi a Aljanna, da kuma gida a tsaka-tsakiyar matsayi na gidan Aljanna, da kuma gida a cikin koramun Alajnna ga wanda ya bar jayayya ko da ya kasance ya nada gaskiya, kuma ya bar karya ko da ya kasance cikin wasa ne, kuma ya kyautata dabi’unsa ) duk wanda ya wadannan munanan dabi’u kuma ya kyara dabi’unsa suka koma masu kyau Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce yayi masa Lamunin gidan a wadannan matsayi, da fatan Allah madaukakin sarki ya sanyamu daga cikin wadanda Manzon Allah zai yi musu luminin gidan Aljanna.
****************************Musuc******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai yi bayyani ne dangane da umarni na kaucewa ko kuma nisanta nuna adawa ko kuma kiyayya ga bayin Allah ta ko wani hali matukar ba sun kasance makiyan Allah madaukakin sarki ba wadanda aka umarce mu da muyi mausu bara’a da kaurace musu, amma idan ba su ba to ya kamata muyi kyakkyawar mu’amala da dukkanin halintun Allah da kuma kaucewa kiyayya a garesu.wannan shine umarnin da Allah madaukakin sarki ya yi ga Manzonsa sahibin dabi’u masu girma, Sikatu Islam kulaini a cikin Littafinsa Alkafi ya ruwaito wani Hadisi wanda sanadinsa yake komawa zuwa ga Ma’aikin Allah tsira da aimncin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk lokaci da Mala’ika jibrilu ya zo mini ba ya tafiya sai ya ce mani Ya Muhamad ka kiyaye kiyayya ga Mutane) har ila yau a cikin Littafin Kafi an ruwaito wani hadisin daga Ma’aikin Allah (S.A.W) yana mai cewa: (babu wani wasici da Mala’ika jibrilu yay i mani kamar yadda yayi na kaucewa nuna kiyayya ga Mutane) masu dukkanin wadannan wasici da ake yiwa Ma’aikin Allah (s.w.a) wasici ne ga mutane ta hanyar ma’aikin Allah (s.a.w) domin shi ma’aikin Allah ma’asumi ne ne ba ya aikata wani abu ko firta wata magana sai wacce allah madaukakin sarki ya umarce sa da ita kuma ba ya aikata wani aiki sai wanda allah madaukakin sarki ya umarce shi da shi kuma dukkanin kyawawen dabi’u masu girma na shi ne,dukkani wannan wasici ana yinsa ne ga Mutane domin ma’aikin Allah (s.a.w) yake bayyana mana cewa nisantar kiyayya ta ba gaira ba saba ta na kare mutunci, kaama da kuma izzar mutune a cikin mutanansa domin hakan shi zai kare sa daga duk wani sharri na masu adawa da shi.har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(babu wani zuwa da mala’ika jibrilu zai yi gurina sai yay i mani wa’azi karshen maganarda yayi mani shine na haneka da nuna adawa ga mutane domin yin haka ya kan yaye tsraici sannan kuma ya tafi da izzar Mutune) , a cikin wata riwayar kwa da aka ruwaito a littafin na Kafi, shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya shuka kiyayya zai girbi abinda ya shuka)
Masu saurare wasu hadisan kwa sun bayyana cewa nuna kiyayya ga hallitun Allah yak an zamanto sanadiyar bata Addinin Mutune domin kiyayya ta kan yi sanadiyar sanya son rai wajen mu’amalar mutane da makiyansa, a cikin Littafin Al’amaliy na shek Tusy (R.T.A) an ruwaito hadisi daga Mustapha tsira da aimncin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce :(duk wanda ya yawaita damuwa da bacin rai, jikinta zai tabu , wato zai rashin lafiya, duk ya munana mu’amalarsa zai azabtar da zuciyarsa, duk wanda yake nuna kiyayya ga mutane, mutuncinsa zai zube) har ila yau a cikin wata riwayar ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(mala’ika jibrilu ya kasance yana hana ni nuna kiyaya ga mutane kamar yadda ya haneni da shan gida tare da bautar gumaka) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu iko wajen aiki da wadannan hadisai.
***********************Musuc**********************************
Masu saurare a nan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala , ni da na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.