Feb 26, 2017 04:52 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, a Shirin da ya gabata mun yi fara bayyani kan kyakkyawar dabi'ar Rashin kai koke wajen wani a yayin da Bawa ya jarabtu da wani ibtila'I, domin mahimancin wannan maudi'I, shirin na Yau ma zai ci gaba da shi, amma kafin nan bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

******************************Musuc**************************

Masu saurare, Shirin zai fara da bisharar Anabta wacce ta kumshi wannan hadisi da aka ruwaito cikin Littafin Khisal na Shekh Saduk, da yake bayyani kan wannan kyakkyawar dabi'a dake daukaka sahibinta zuwa samun matsayi na kasancewa da Annabi Ibrahimu Khalilullah (a.s), Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Duk wanda ya yi rashin lafiya yini guda da dare daya bai kai kokensa ba ga mai taimakonsa, Allah zai tayar da shi ranar Alkiyama tare da Khalilinsa Ibrahimu Khalilul Rahaman har sai ya tsallake siradi kamar walkiya), Masu saurare, daga cikin albarkar dake tattare da wannan dabi'a, samun rabauta da gidan Aljanna, a cikin Littafin Almahasin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:( ku Saurara! Shin kuna so in baku labarin halaye biyar da suka na biyayya kuma biyayya tana kira zuwa ga Aljanna? Sai aka ce Na'am, sai Imam (a.s) ya Ambato su kuma mafi fifiko daga cikin su boye Musiba ), kamar yadda Hadisai iyalan gidan Anabta (a.s) suke yi mana albishir da girman lada na wanda ya dabi'antu da wannan kyakkyawar dabi'a da kuma misdakin aiki da ita.Hakika cikin Littafin Kafi an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s)ya ce:(Duk wanda ya jarabtu da rashin lafiya na yini guda ya kuma karbe sa da karba na gari ya kuma cika godiyar ga Allah tabaraka wa ta'ala ya kasance kamar wanda ya yi ibadar shekara 60.sai wanda ya ruwaito hadisin ya tambayi Imam (a.s) ta yaya zai karbi rashin lafiyar da karba mai kyau? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa ya kasance a kanta kadda kuma ya fadawa kowa kan halin da yake ciki, idan ya wayi gari ya godewa Ubangiji bisa halin da ya kasance). Masu Saurare, Wasu Hadisan kuma sun shiryar da mu zuwa kebance Mumuni wajen fada masa halin da Mutum de ciki na rashin lafiya, da kuma tsawatarwa mai tsanani kan ke koke wajen Mukhalif, Shugaban Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya kai kokensa wajen Mumuni kamar ya kai kokensa wajen Allah madaukakin sarki ne, kuma duk wanda ya kai kokensa wajen Mukhalif, watau kafiri ko Mushriki kamar ya kai karar Allah madaukakin sarki ne), Har ila yau cikin littafin musadikatul-Ikhwan na shekh Saduk, an ruwaito wani hadisi wanda yay i Karin bayyani dangane da hikimar dake cikin hadisin da ya gabata, inda a cikin sa Imam Sadik(a.s) yake fadawa daya daga cikin Sahabansa:(idan wani bala'I ya sauko maka, kadda ka kai kokenka ga kowa daga cikin Kafirai ko mushrikai, saidai ka Ambato ta zuwa ga sashen 'yan uwanka domin ba za talautu daga abubuwa guda hudu ba, ko ya wadatar da kai da Dukiya, ko kuma ya taimake ka wajen tunkarar matsalar da kuma magance ta, ko kuma ya yi maka Addu'a, ko kuma ya baka shawarwari masu amfani).

*************************Musuc********************************

Masu Saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai yi bayyani kan kyakkyawar dabi'ar kwadayi ga gyarar Mutane da kuma kare abinda zai cutar da su, domin hakan na cikin kyawawen dabi'un musulinci, a cikin Alkur'ani mai girma  Suratu Tauba  Aya ta 128, Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika Manzo daga cikinku ya zo muku, abin da zai cuce ku yana damunsa, mai kwadayin shiriyarku,mai tausayawa kuma mai jin kai ga Muminai) Masu saurare wannan Aya mai albarka ta tattabar da cewa kwadayin gyara da kuma shiriyar Mutane na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci da hakika cikin Littafin Ma'anil Akhbar na Shekh Saduk, an ruwaito Hadisi daga kuma dabi'an Annabin Rahama (s.a.w.a) kuma hadisai da dama sun bayyana cewa dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a na a matsayon koyi da Annabin Rahama (s.a.w.a) da kuma samun gafara gami da saukar Albarka maras yankewa daga Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Mukni'at yayin da Ambato aiyukan ranar Juma'a,  Shekh Mufid yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ce:(Ka karanta karshen Aya ta suratu Taubat watau(Hakika Manzo daga cikinku ya zo muku, abin da zai cuce ku yana damunsa, mai kwadayin shiriyarku,mai tausayawa kuma mai jin kai ga Muminai ) sannan kuma ya ce Hakika an ruwaito Hadisi daga Abi Abdallah Imam Sadik (a.s) ya ce (wanda ya Karanta wannan Aya bayan ya kamala sallar Juma'a kafin ya tashi daga inda yake za ta kasance masa kaffara daga wannan Juma'a zuwa wata Juma'a).masu Saurare, daga cikin misdakin gaskiyar wannan kyakkyawar dabi'a yiwa Mutane Nasiha da Ikhlasi kamar yadda Allama Turaihi cikin Littafinsa Majma'ul Bahrain  ya bayyana,kuma wannan dabi'a na tabbatuwa  a yayin da Mumuni zai 'yantu kuma yayi iya kokarinsa wajen kare Mutane daga cutuwa da kuma Janyo alheri gare su, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a dan albarkar riko da kuma koyi da shugaban Mursalai wanda aka aiko shi Rahama ga talikai da kuma iyalan gidansa tsarkaka, amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya.

*************************Musuc******************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.