zababun Aiyuka-Nisantar Makirci Da Yaudara
shirin na yau zai yi bayyani ne na nisantar makirci da yaudara a cikin ko wani hali
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne na nisantar makirci da yaudara a cikin ko wani hali,amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
****************************Musuc****************************
Masu saurare hadisai da dama sun yi galgadi ga ko wani musulmi da ya kaucewa munanan halaya kamar su hiyana, makirci, yaudara da sauransu,Shekh Muhamad bn Ali Assaduk yardar Allah ta tabbata a gareshi a cikin littafinsa Al’amaly ya ruwaito hadisi daga iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka daga kakansu Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:( duk wanda ya kasance musulmi ne ba ya makirci kuma ba ya yaudara, domin na ji mala’ika jibrilu (a.s) ya ce hakika makirci da yaudara siffofi ne na ‘yan wuta, sannan ma’aikin Allah ya ci gaba da cewa ba ya daga cikinmu wanda ya ha’inci musulmu dan uwansa, kuma ba ya daga cikinmu wanda ya yaudari dan uwansa musulmi , hakika Mala’ika jibrilu wanda shine ruhi amincecce ya zo mani da sako daga wajen ubangijin Talikai yana mai cewa :Ya Muhamad na horeka da kyawawen dabi’u domin munanen dabi’u suna tafiya da da alhairan duniya da Lahira, ku saurara duk wanda ya fi kama da ni daga cikinku shine wanda ya fiku kyawawen dabi’u). masu saurare a cikin wannan hadisi mai albarka za mu fahimci cewa hiyana, yaudara , makirci, almundahana da dukiyar Al’umma na daga cikin misdakin munanan dabi’u ma’ana da kuma mu’amala tare bayin Allah kamar yadda kaucewa irin wadannan munanen dabi’u na daga cikin misdakin dabi’antuwa da dabi’un Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka domin haka ne ma hadisai da dama suka bayyana cewa daga cikin bayin Allah wanda dabi’unsa suka fi kusa da na ma’aikin Allah shine wasiyinsa Imam Ali dan Abi Talib amincin Allah ya tabbata a garesu. A cikin Littafin Ikabul A’amal, Shek Saduk ya ruwaito hadisi daga Amiru mumunin (a.s) ya ce:(in ba dan naji ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa makirici, yaudara da Almundana dukkaninsu wuta ce, da na kasance wanda ya fi kowa makirinci daga cikin kabilar Larabawa) wannan magana Imam Ali( a.s) ya fadeta ne a matsayin mayar da martani ga makirci bani Umaiya a yayin da suke kulla masa makirci kuma a zatansu bai gane manufarsu ba,
Masu saurare hadisai da dama sun yi ishara da kyakkyawar bushara ga masu kyawawen dabi’u, a cikin littafin Kafi Sikatul Islam Kulaini ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(musulmi dan uwan musulmi ne, ba ya zaluntarsa, kuma ba ya yaudararsa, ba ya kuma ha’intarsa)har ila yau a wata riwayar Imam (a,s) ya ce :(musulmi Dan Uwan musulmi ne, shine ganinsa, madibinsa, da kuma shiriyarsa, ba ya ha’intarsa, ba ya zaluntarsa,ba ya kuma kulla masa makirci, ba ya karyata shi, ba ya kuma cin amanar sa) , a wata riwayar kuma Imam (a.s) ya ce: (mumuni dan uwan mumuni ne idanunsa ne na gani kuma shine shiriyasa ba ya ha’intarsa ba ya kuma zaluntarsa, ba ya kuma yi masa Almundahana ba ya kuma gwada masa kiyayya)
Daga cikin irin wasiyoyin da Imam (a.s) ya yiwa sahabansa ya ce:( ku girmama sahabanku kuma ku zamanto masu ba su kariya, kadda sashinku su dinga farwa sashinsu, kadda ku cutar da junanku, kadda ku dingawa junanku hassada , na hane Ku da rowa, ku kuma kasance bayin Allah mukhlisai) .
*****************************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi magana ne dangane da mahimancin dabi’antuwa dakyakkyawar dabi’a na kokari wajen biyan bukatun bayin Allah,domin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un da suke kusantar da Bawa zuwa mahalicinsa kuma yana janyo albarkatu masu tarun yawa ga rayuwar Dan Adam tare kuma da sanya soyayya a tsakanin Al’umma.an ruwaito hadisi daga shugaban kyawawen dabi’u wajen biyan bukatun halitun Allah shugabanmu Muhamad Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce: (duk wanda ya biya bukatar mumuni dan uwansa kamar ya bautawa Allah a tsahon rayuwarsa ne) kamar yadda Allah madaukakin sarki yake isarma masu kokari wajen biyan bukatun bayin Allah ko da ba su daga hanuwasu suka roke su ba, shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya biya hajar Dan uwansa mumuni Allah madaukakin sarki zai biya masa irin wannan haja so dubu dari ranar Alkiyama , farkonsa zai sanya su Aljanna). Kamar yadda daga cikin Albarkatun dake tattare da biyan bukatun bawu ,za a biya musu bukatunsu tun a nan duniya.a cikin Littafin Nahjul Balaga, daga cikin wasiyoyin da yayi shahararen sahabinsa Kumail bn Ziyad yardar Allah ta tabbata a gareshi ,Amirir mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Ya Kumail ka umarci ahlinka da suka zamanto masu kokari wajen nemen kyawawen halayen koli, kuma masu biyan bikatun masu kwana,na rantse da wanda ya fadada jinsa ga dukkanin sauti, babu wani mutune da zai sanya wa wata zuciya yarda da kuma farin ciki sai Allah madaukakin sarki ya sanya farinci a cikin zuciyarsa ) masu saurare , maluma sun fassara kaolin Shugaban mumunai na cewa ( su zamanto masu kokari wajen biyan bukatun masu kwana) da cewa ma’ana shie kokari wajen biyan bukatun wadanda ba su da karfi ko kuma wadanda suke da rauni ba tare da sanin su ba kuma ba tare da sun bukaci a yi musu hakan ba.
A bangare guda kuma, wasu hadisan sun yi hani mai tsanani na kin kokari wajen biyan bukatun wanda ya nemi taimako a gareku,musaman mumuni, nuna kasawa ga hakan yana a matsayin hiyana ga Allah madaukakin sarki da manzon sa, a cikin littafin babban malamin hadisin nan shek Barki an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya kasance Sahabinmu ne, dan uwansa mumuni ya nemi taimakonsa, ba tare da ya yi wani kokari ba wajen biyan bukatun sa ba, hakika ya ha’inci Allah da Manzon sa da kuma mumunai baki daya). Har ila yau a cikin wani hadisin na daban Imam (a.s) ya ce:(duk wanda ya fice a kan wata bukata ta dan uwansa ma’ana ya ji kuma yi banza ta ita ba tare da yayi wani kokari wajen maganceta ba, to kamar ya ha’inci Allah da Manzonsa ne) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu iko biyan bukatun ‘yan uwanmu a lokacin da suka gabatar da bukatarsu a garemu domin Karamcin shugaban halittu Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.
***************************Musuc***************************
Masu saurare , ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dakata zai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimaka har shirin ya kammala musaman Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar, nike muku fatan Alheri, wasslama alekum……………….