Mar 04, 2016 15:33 UTC
  • zababun Aiyuka-Zuhudu ko Gudun Duniya

shirin na yau zai yi dubi ne ga Zuhudu ko kuma gudun Duniya


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi dubi ne ga Zuhudu ko kuma gudun Duniya,amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


**************************Musuc***********************************


Masu saurare ma’anar Zuhud ba a ana nufin haramtawa kai ba jin dadin Arzikin da Allah madaukakin sarki ya saukarwa bayinsa ba ne ba kamar yadda wasu ke fada. ma’anar Zuhudi shine ‘yantuwa daga kangin duniya da kuma tsoron talauci ko abinda ke cikin duniya tare kuma da samun Sikka gami da tabbaci daga Allah madaukakin sarki ma’ana Bawa ya samu tabbacin cewa dukkanin ni’imar duniya da Lahira na Allah ne kuma shine mai hanawa da bayarwa, duk abinda Bawa ya samu ya san cewa daga Allah ne haka zalika duk abinda ya rasa.a cikin litattafen Ma’anil Akhbar na Shek Saduk da Kafi na Shek Kulaini da kuma Tahzibul Ahkam na shek Tusy an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce: (ba ma’anar Zuhudi a Duniya ba karin dukiya ko kuma haramtawa kai arzikin Allah madaukakin sarki ya horewa bayinsa na Halal, ma’anar Zuhudu a Duniya shine kadda ya kasance abinda ke hanunka na dukiya ya fi zama tabbaci a gareka da abinda ke wajen Allah madaukakin sarki).hakika dabi’antuwa da wannan hali mai kyau, shine mabudin Alherin Dan Adam a Duniya da Lahira, kamar yadda shugaban Mursalai Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu. A cikin Littafin Amaly na shek Tusy an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce: (hakika farkon Alherin wannan Al’umma Zuhudu da samun tabbaci gami da Yakini , kuma hallakar karshenta, rowa da kuma dogon fata) ma’anar wannan hadisi duk mutuman da ya samu tabbaci da yakini na cewa duk abinda ya mallaka daga Allah ne a aikace ba a baki ba ya samu alheri duniya da Lahira, kuma hallakar Dan Adam ta kan kasancewa ga rowa gami da dogon fata wanda hakan ya kan toshe duk wani aikin Alheri). Masu saurare   Zuhudu da ‘yantar da kai daga daudar Duniya da kuma tsoron talauci ya kan taimakawa Dan Adam wajen aiyaka Alheri da kuma aiyuka na gari.kamar yadda aka ruwaito cikin Littafin Ma’anir Akhbar, shugaban mumunai Aliiyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:( Zuhudu a Duniya shine rage dogon fata, godiyar ko wata irin ni’ima da kuma yin tsantseni kame da abinda Allah madaukakin sarki ya haramta a gareka).har ila yau a cikin littafin Kafi Imam (a.s) ya ce:(hakika daya daga cikin mataimakan kyawawen dabi’u ga Addini, shine Zuhudu a duniya).har ila yau ta hanyar Zuhudu A Duniya mumuni yake dandana dadin Imaninsa da kuma tabbaci ga abinda ke wajen Allah madaukakin sarki, a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(an sanya dukkanin Alheri a gida guda, kuma aka sanya mabudinsa Zuhudu a Duniya),har ila yau  Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(babu mutuman da zai ji dadin Imani a zuciyarsa har sai ya kasance bai damu da daudar duniya ba). sannan Abu Abdullah Sadik (a.s) ya ce:(haramun ne ga zukatanku su dandana  dadin Imani har sai sun kasance masu Zuhudu a nan Duniya), daga cikin kalaman shugabanmu Imam Zainul Abidin (a.s) yayin da yake bayyana mana Alamomin Zuhudu a cikin Alkur’ani mai tsarki a cikin wani Hadisi da aka ruwaito cikin Littafin Kafi na Sikkatu Islam Kulainy Imam (a.s) ya ce:(ku saurara!Hakika ma’anar Zuhudu a cikin Littafin Allah shine, sai ya karanto wannan Aya mai Albarka(Don Kada Ku yi Bakin ciki a bisa abin da ya tsere muku kuma kada ku yi fariya da abin da ya ba ku domin kuwa Allah ba ya son duk wani mai girman kai mai yawan alfahari).


**************************Musuc****************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan mahimancin amfanuwa da ni’imar duniya daidai bukata, domin yin hakan shine mafi kyakkyawar hanya ta ‘yantuwa daga kangin duniya, kuma na daga cikin sunar Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin wata riwaya da aka ruwaito cikin littatafan hadisai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:minene game da Duniya!matsayi na a cikinta kamar mahayi ne, da ya dauke mata itacen dake kanta a lokacin zafi) ma’anar wannan hadisi shine kamar wanda ya yi barcin rana ne a cikin ta sannan ya fice ya bar ta) .abinda ma’aikin Allah ya ke nufi a wannan hadisi ya kamata mumuni mu’amalar sa da duniya ta  kasance kamar Dan bulaguro wanda ya tarar da Itaciya a kan hanyarsa a lokacin tsananin zabi ya kuma amfana da inuwar wannan itaciya , yayi barci kalkashinta na dan wani lokaci sannan ya ci gaba da bulaguransa. A wani hadisin kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya sanar da cewa tsanani a wajen nemen daudar Duniya na daga cikin tarkon shaidan da yake shagaltar da Mutune aikata aiyukan Alheri wadanda ta hanyarsu ce mutune yake gina gidansa na Lahira, hakika Sikatu Islam Kulaini ya ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) na cewa:(tsanani wajen neman daudar Duniya yak an cutar da Lahira) a wata riwayar kuma ya ce :(abinda aka nema kadan kuma ya wadatar ya fi wanda aka nema mai yawa ya kuma shagaltar da abinda ya fi mahimanci).


Daga cikin wasiyar da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yiwa wasiyinsa shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya ce masa (Ya Ali Hakika Duniya kurkukun mumuni ce kuma Aljannar Kafiri ce, Allah madaukakin sarki ya yi wa Duniya wahayin cewa ki yiwa wanda ya yi mani hidma, hidma kuma ki bi wanda ya yi maki hidma, Ya Ali babu wani dan Adam daga cikin mutaman farko da kuma na karshe da ya kasance ya nada kyakkyawan fata da ranar Alkiyama ba, ba a bashi wani abu daga daudar Duniya ba sai kamar matsayin loma guda) abinda ake nufi da kamar loma guda daga cikin ni’imar duniya shine abinda zai isheshi gudanar da rayuwarsa  a duniyar. Acikin Littafin Nahjul Balaga Imam Ali (a.s) ya ce:(Ya Bani Adam duk abinda ka samu fiye da bukatarka ko kuma cikinka ka sani cewa taskar waninka ne) hakika masu saurare dabi’antuwa da dabi’ar wadutuwa da daidai bukata daga ni’imar Duniya ya kan samarwa Mutune konciyar hankali da nutsuwa a rayuwarsa ta duniya kafin aje ga rayuwar Lahira, da fatan Allah madaukakin sarki ya arzutamu da wannan dabi’a mai kyau.


****************************Musuc*********************************


Masu saurare, anan za mu dakata, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Injeniyanmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama aleku wa rahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.