Mar 04, 2016 15:34 UTC
  • zababun Aiyuka-Mahimancin Jhadi

shirin na yau zai yi dubi ne kan jihadi da kokari wajen tsarkake zukata


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi dubi ne kan jihadi da kokari wajen tsarkake zukata, amma kafin mu shiga cikin shiri bari mu saurari abinda aka yima tanadi a kan faifai.


*******************Musuc********************************


Jihadi Nafs da kuma tsarkake zukata na daga cikin dabi’un masu kyakkyawan  rabo, wadanda suka rabauta da yardar Allah madaukakin sarki, abinda ake nufi da tsarkake zukata shine Bawa ya tsarkake zuciyarsa wajen aikata aiyukan Alheri da kuma nafilfilu, da kuma tsarkaketa daga duk wani aiki na sabo wanda zai gurbata masa hasken imaninsa, A cikin Alkur’ani mai tsarki Allah madaukakin sarki na cewa:(da kuma Rai da abin da ya daidaita shi. sa’an nan ya sanar da shi fajircinsa da shiryuwarsa. Hakika wanda ya tsarkake shi ya rabauta. Hakika kuma wanda ya turbude shi da (laifi) ya tabe) suratush Shams daga Aya ta 7 zuwa 9.


Tsarkakar zukata shine wanda Ma’aikin Allah tsira da amincin su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya siffanta shi da Jihadil Akbar wato babban jihadi a cikin mashhurin hadisin nan, wanda Littatafan hadisi da dama kuma masu inganci suka ruwaito kamar Littafin Ma’anil Akhbar da sauransu wanda kuma sanadin hadisan ke komawa zuwa ga shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) y ace:(hakika Ma’aikin Allah (s.a.w) ya tura sahabansa zuwa yaki, bayan sun dawo sai ya taryesu da cewa marhabin da wadanda suka dawo daga karamin jihadi, kuma abinda ya rage musu shine babban jihadi, dukkanin sahaban sai suka yi mamaki da wannan jumla, sai aka ya ma’aikin Allah wannene jihadil Akbar wato babban jihadi? Sai Ma’aikin Allah ya ce jihadi Nafs wato yakar zuciya, sannan ya kara da cewa Hakika mafi fifikon jihadi shine wanda ya yaki zuciyarsa daga abinda ta raya masa na sabo sannan ya tsarkake ta daga duk wata gurbata na zunubai kuma ya raya ta da yin nafilfilu).


Masu saurare daga cikin misdakin jihadin Nafs kiyaye ta a yayin da take kokarin fita daga da’irar riko da hukunce hukuncen Shari’a wanda ta hanyarsu ne ake samun maslahar duniya da kuma rabauta a ranar Lahira, a cikin Littafin Sawabul A’amal Shek Saduk ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) y ace:( duk wanda ya mallaki zuciyarsa a yayin da ta karkata, kuma a yayin da ta sabunta,  kuma a yayin da ta bukaci wani abu, da yayin da ta yi fishu da kuma yayin da ta yarda,Allah madaukakin sarki zai haramtawa wuta jikinsa), har ila yau shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya shiryar da mu cewa daga cikin misdakin jihadin Nafs shine ka sabawa zuciyarka aikata kyawawen aiyuka da kuma kyawawen dabi’u wadanda za su yi maka jagora zuwa ga samun rabauta a duniya da Lahira, A cikin Littafin Kafi na shek Kulaini an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) yayin da yake yiwa daya daga cikin sahabansa Nasiha yana mai cewa:(hakika ka kasance Likitan kanka da kanka , domin ka nemo matsalar dake fuskantarka da kanka , wanda hakan shi zai baka damar sanin maganin da za ka warkar da kanka, za ka ga yadda tashinka zai kasance a karan kanka, ma’ana yadda zaka gudanar da rayuwarka) ma’anar wannan hadisi duk wanda Allah madaukakin sarki ya bashi sani na Addini to an bashi sanin cuwa da kuma maganinta ma’ana abinda zai cutar da zuciyarsa da kuma maganin warakarta ya rage garesa yadda zai tafiyar da rayuwarsa, idan ya bukaci tsarkaka zai tsarkaka, kazalika idan ya zabi gurbatar rayuwa  zai zamanto kurbacecce wanda kwara dabba ma da shi.


Har ila yau a cikin Littafin Man La Yahduruhul Fakih Imam (a.s) ya ce:( ka sanya zuciyarsa a matsayin makiyi wanda zaka yaka, kuma ka sanya dukiya a matsayin Amanar da za ka mayar da ita), a wata riwayar kwa yayi ishara da cewa ya kamata Mutune ya yi dogaro da iliminsa wajen tsarkake zuciya, ma’ana ya yi aiki da iliminsa na Addini saboda yin aiki da ilimi shine zai sanya Bawa ya samu galaba daga kaidin Shaidan Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya kasance ba shi da mai yi masa wa’azi a cikin zuciyarsa,bas hi da mai shiryar da shi, to makiyinsa na iya galaba a kansa,  kuma wannan makiyi shine Nafsul Ammaratu bi su’I wato zukiyar ta karkata wajen sabon ubangiji da kuma shaidan a cikinsa) da fatan Allah madaukakin sarki ya sa mu yi galaba da wannan makiya tare kuma da yin aiki da ilimin da muke da shi na Addini daidai gwalgwado.


****************************Musuc*****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan sadaukarwa wajen neman yardar Allah a kan son zuciya,masu saurare Alkur’ani mai tsarki ya bayyana son zuciya ya fi bautar gumaka hadari saboda shi son zuciya  jagora ne wanda zai kai mai yinsa zuwa bata da kuma wata  kai tsaye , A cikin Suratu Jasiyat Aya ta 23 Allah madaukakin sarki y ace:(shin yanzu ba ka ganin wanda ya riki Ubangijinsa, son ransa,Allah kuma ya batar da shi a kan sani ya kuma rufe jinsa da kuma zuciyarsa, kuma ya sanya rufi a ganinsa,to waye zai shiryar da shi bayan Allah!Me ya sa ba kwa wa’azanta ne ) a cikin suratu Nazi ati Aya ta 40 da kuma ta 41 Allah madaukakin sarki y ace:(Duk wanda kuma ya ji tsoron tsayawa gaban Ubangijinsa, ya kuma hana zuciya bin abinda take so. To hakika Aljanna ita ce makoma) a cikin littafin Man La Yahduruhul Fakih an ruwaito hadisi daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce:(duk wanda wata Alfahsha ta tunkaresa sai ya kauce mata saboda tsoron Allah, Allah madaukakin sarki ya haramtawa masa shiga wuta, kuma zai bashi abinda yayi masa alkawari cikin Littafinsa mai tsarki, sannan sai ya karanto wannan Aya mai Albarka(wanda kuma ya ji tsoron tsayiwa (gaban) Ubangijinsa, yana da Aljanna guda biyu) suratu Rahamani Aya ta 46, ku saurara duk wanda aka bashi zabi tsakanin Duniya da Lahira kuma ya zabi Duniya a kan Lahira, zai hadu da Allah madaukakin sarki ba shi da wani kyakkyawan abu da zai yi masa garkuwa na shiga wuta, kuma duk wanda ya zabi Lahira ya kuma bar duniya Allah zai yarda da shi kuma ya gafarta masa ya kuma daidaita masa aiyukansa), masu saurare dabi’antuwa da halayen sadaukarwa yardar Allah a kan son zuciya, ya kan sanya Bawa ya samu hasken Allah madaukakin sarki kuma ya samu sabati gami da juriya a nan duniya da Lahira kuma ya zamanto daga cikin makusantan Allah madaukakin sarki.a cikin littafin Almahasin na shek Barki an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:(Allah madaukakin sarki ya ce: hakika wanda yay i  sallah domin kaskantar da kai saboda girmana kuma ya hanu da bin sha’awar zuciyarsa saboda da ni, kuma yake aibatona a ranaikunsa, ba ya girmar kai ga hallitu na, yana kuma ciyar da mabukaci, ya suturtar da wand aba shi da shi, ya kuma jikan wanda wani bala’I ya same shi,kuma ya girmama matafiyi, wannan,haskensa  zai haskaka kamar hasken Rana,).


************************Musuc***************************


Masu saurare anan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shiri da yardar Al..