zababun Aiyuka-Syayyar abinda Allah ke so
Mar 04, 2016 15:36 UTC
shirin na yau zai yi bayyani ne a kan soyayyar da abinda Allah madaukakin sarki yake so
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne a kan soyayyar da abinda Allah madaukakin sarki yake so, amma kafin mu shiga shirin ga wannan.********************************Musuc****************************
Masu saurare soyayyar abinda Allah madaukakin sarki yake so shike bayyana hakikanin imanin Bawa, kamar yadda sunar Ma’aikin Allah da kuma iyalan gidansa tsarkaka ta yi ishara da hakan, a cikin littatafan Almahasin na Shek Barki da Kafi na Sikatu Islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Fudail bn Yasar y ace: na tambayi shugaban Imam Sadik (a.s) a kan soyayya da kiyayya shin suna daga cikin Imani ?sai yace da ni shin minene Imanin idan ba soyayya ko kiyayya ba, sannan sai ya karanto wannan Aya mai Albarka:(Allah ya kimsa muku son Imani ya kuma kawata shi a cikin zukatanku,ya kuma kimsa muku kin kafirci da fasikanci da sabo. Wadancan su ne shiryayyu) suratu Hujurati Aya ta 7. Masu saurare wannan hadisi , hakikanin Imani shine bayyana soyayya ga ababen dake da cikar imani ga Allah madaukakin sarki kamar cika farilar da Allah ya farantawa bayi da kuma soyayar waliyansa Annabawa da mabiyansu,ita kuma kiyayya ita ce kiyayyar duk wani wata dauta ta sabo da kuma yin bara’a ga makiyan Allah tare kuma da aiki da abinda zai tabbatar da hakan, wannan shine fuska da kuma Alamar Addinin gaskiya. A cikin littafin Mahasin an ruwaito daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yayin da yake amsa tambayar daya daga cikin sahabansa sai y ace:(shin addinin wani abu ne idan ba soyayya ba, shin b aka ji fadar Allah madaukakin sarki ba inda yake cewa:(Ka ce (da su) idan kuka boye abin da ke cikin zukatanku ko kuma ku bayyana shi, Allah Yana sane da shi, kuma Yana sane da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin Kasai,kuma Allah mai iko ne a bisa komai) suratu Ali-imrana Aya ta 31. Iman ya ci gaba da cewa shin ba ji kaolin Allah ga Annabi Muhammad (s.a.w) ba(Allah ya kimsa muku son Imani ya kuma kawata shi a cikin zukatanku) suratu Hujutati Aya ta 7, kuma ba ka ji fadar Allah madaukakin sarki ba (suna son wanda ya yi hijra zuwa garesu) Suratu Hashari Aya ta 9. Sannan Imam (a.s) ya ce ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Addini shine soyayya kuma soyayya shine Addini).
Masu saurare, imani ga Allah da kuma saninsa madaukakin sarki na daga cikin kyawawen dabi’u kuma cimma hakan yana bukatar sanin abinda Allah yake so da kuma abinda waliyansa da kuma masoyansa ke so, da kuma sanin makiyansa domin mu ki su kuma mu yi musu bara’a. shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) a cikin wani hadisi da aka ruwaito a cikin litattafan kafi da Almahasin ya ce:(alamar mumuni uku ne , na farko sanin da Allah,kuma wa yake so kuma wa yake ki) har ila yau Imam (a.s) ya ce:(daga cikin tabbacin Imani ka so don Allah, kuma ka ki don Allah, ka bada don Allah kuma ka hana don Allah) har ila yau a cikin wani hadisi Imam (a.s) ya ce:(duk wanda ya so Allah,kuma ya Ki makiyinsa,zai daukaka a duniya sannan ranar Alkiyama Allah madaukakin sarki zai yafe masa zunubansa ko da yawansu ya kai yawan teku).
*************************Musuc********************************
Masu saurare ci gaban shirin zai yi bayyani a kan soyyaya da kiyayya ta kasance saboda da Allah madaukakin sarki,domin dabi’antuwa da wannan ita ce za ta sanya shi’arinmu da kuma aiyukanmu su kasance a kan abinda Allah madaukakin sarki ke so bisa dukkanin alakarmu da mu’amalarmu a tsakanin Al’umma kuma yin hakan shike karfafa imanin Bawa, shahararen malamin hadisin nan shek Barki ya ruwaito hadisi a cikin littafinsa Almahasin, sikatu Islam Kulaini a cikin Littafinsa Alkafi,shek Saduk a cikin Littafinsa Ma’anil Akhbar dukkaninsu sun ruwiato wani hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) tare da sanadi bamambanta ya ce: ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya tambayi sahabansa cewa wani abu ne ya fi cikar imani? Wasu suka ce Allah da ma’aikinsa ne masana, wasu kuma suka ce Sallah ce, wasu kuma suka ce Zakka, wasu kuma suka Azumi, wasunsu kuwa suka ce Hajji da Umara,wasu kuma suka ce Jihadi, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce dukkanin abinda kuka fada na da nashi matsayi da falala a musulinci amma hakikanin amsar ita ce duk abinda musulmi zai so ya kasance saboda Allah haka zalika duk abinda zai ki ya kasance saboda Allah madaukakin sarki, da kuma soyayyar waliyan Allah tare da yin bara’a ga makiyansa).
Masu saurare,shugaban masu shiriya ya shiryar da mu cewa iltizami da wannan dabi’a mai kyau wasila ce ta samun rabauta da karama na zamantowa daga cikin zababbun Ubangiji madaukakin sarki.a cikin litattafan Kafi da Almahasin, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir(a.s) ya ce Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce:soyayyar mumuni gad an uwansa mumuni saboda Allah na daga cikin girmar imani,kuma duk wanda ya so saboda Allah kuma yaki saboda Allah, ya bayar saboda Allah ya kuma hana saboda Allah wannan ya na daga cikin zababbun Allah madaukakin sarki).maluman hadisi sun fasara ma’anar badawa da hanawa saboda Allah da cewa mumuni ya baiwa wanda Allah umarta a basu daga cikin makusanta, talakawa, miskinai da saurensu kuma ya hanawa wanda Allah ya umarta da a hana musu, ya kasance kautarsa da infaki bisa ma’auni da Allah madaukakin sarki ya yi umarni., dabi’antuwa da wannan dabi’a mai kyau na daga cikin kamalar imani kamar yadda Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya bayyana a cikin riwayoyin biyun da suka gabata.sannan a wata riwayar Imam (a.s) ya ce:(wanda ya so saboda Allah kuma ya ki saboda Allah, ya bada saboda Allah kuma ya hana saboda Allah, shi yana daga cikin wadanda Imaninsu ya kammala).a cikin wani hadisin kuwa Imam(a.s) ya ce:(babu wasu mumunai da za su hudu sai ya kasance daya yafi dan uwansa falala, kuma wanda ya fi falalar shine wanda nunawa dan uwansa tsananin soyayya). Da fatan Allah madaukakin sarki ya sanyamu daga cikin masu so ko kiyayya saboda Allah don girma dakuma Albarkar Zababben Allah Muhamad Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.
***************************Musuc*****************************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.