Mar 04, 2016 15:37 UTC
  • zababun Aiyuka-Soyayya Don Allah

shirin na yau ci gaban shirin da ya gabata ce ma’ana shine soyayya ko kiyyaya ta kasance saboda Allah madaukakin Sarki


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau ci gaban shirin da ya gabata ce ma’ana shine soyayya ko kiyyaya ta kasance saboda Allah madaukakin Sarki, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


***************************Musuc***********************


Masu saurare shirin zai fara da kyakkyawen albishir na girman ladan da Allah madaukakin sarki ya tanardarwa masu son juna saboda  Allah, masoyin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka a cikin wata riwaya da aka ruwaito a cikin Litattafan Mahasin na shek Abu Ja’afar Albarki da Kafi na sikatu islam kulaini Ma’aikin Allah(s.a.w) ya ce:(masu son juna saboda Allah, ranar Alkiyama suna kalkashin  inuwar Al’arshin Ubangiji, fuskokinsu sun fi kankara haske, sun fi kuma rana haske, ko wani Mala’ika yana fatan samun irin  wannan matsayi da suka samu  da kuma dukkanin Annabawa mursalai, sai Mutane su ce su waye wadancan? Sai ace musu sune masu soyayya saboda Allah madaukakin sarki).masu saurare dabi’antuwa da irin wannan hali mai albarka, alama ce ta samun rabauta da soyayyar Allah da kuma alheri mai yawa kamar yadda ya kasance wasilar sanin hakan ,shine  jarrabawar kai , ma’ana mutune ya bincike kansa domin gane hakan, a cikin Littafin Ilalu shara’I’I na shek Saduk an ruwaito hadisi daga shuhaban Imam Muhamad Bakir (a.s) y ace:(idan Kana so ga san cewa a kwai alheri a gareka, sai ka dubu zuciyarka, idan ta kasance tana son ahlin da’a ga Allah wato masu biyayya ga Allah kuma tana kiyayya ga masu sabon Allah to hakika a kwai alheri a gareka kuma Allah yana son ka, idan kuma zuciyarka tana adawa da masu biyayya ga Allah kuma tana son masu sabon Allah to hakika kana tattare da shari kuma Allah yana fishi da kai, domin rai  na tare da masoyinta).


A wani hadisin kuma Imam Bakir (a.s) ya bamu albishirin din cewa Allah madaukakin sarki ya na bayar da Lada ga mai niya mai kyau ko da yayi kuskure wajen tantance wanda ya kamatan a bayyana soyayya a garesun ma’ana wajen nuna soyayya ga masu biyayya ga masoya Allah koda Bawa ya yi kuskure wajen hakan idan yanada niya mai kyau Allah madaukakin sarki zai basa Ladansa.a cikin Littatafan Almahasin da Amaly na shek tusy an ruwaito hadisi daga Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce : (Da Mutune zai so wani mutune saboda Allah, Allah madaukakin sarki zai basa ladansa ko da kuwa wanda aka kwadawa son  ya kasance daga cikin ‘yan wuta a sanin Ubangiji, kazalika da Mutune zai ki wani Mutune saboda Allah ma’ana saboda yana sabon Allah, Allah madaukakin sarki zai bashi Ladan wannan aiki ko da kuwa wanda ya kin yana daga cikin ‘yan Aljanna a ilimin Ubangiji)


Har ila yau a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:( Hakika Soyayya ta kan kasancewa saboda Allah madaukakin sarki da kuma ma’akin sa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ,kazalika ta kan kasancewa saboda Duniya, duk wanda ya so saboda Allah da Ma’aikinsa  Ladansa yana wajen Allah, kuma duk wanda ya so saboda Duniya ba zai samu komai ba ).da fatan Allah madaukakin sarki ya arzutamu da irin wadannan halaye masu albarka soyayyarmu ta kasance saboda Allah, haka zalika kiyayyarmu ta kasance saboda Allah don darajar shugabanmu Annabi Muhamad tare da iyalan gidansa tsarkaka.


****************************Musuc****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shrin zai yi bayyani a kan fadar Alheri ma’ana Bawa ya rike bakinsa da fadar maganar da ba ta dace,duk abinda zai zai fito daga bakin Bawa ya kasance alheri ne ,nassosi da dama sun umarci mumuni da ya kame bakinsa wajen firta Magana matukar ba ta Alheri ce ba, kuma a kwai alheri a cikinta.a cikin suratu Bakara Aya ta 83 Allah madaukakin sarki ya ce:( kuma (ku tuna) lokacin da muka daura alkawari da Bani-isra’ila (kan) kada ku bauta wa kowa sai Allah , kuma ku kautata wa mahaifa da makusanta da marayu da miskinai , kuma ku rika yi wa Mutane kyakkyar Magana, ku tsaida salla ku bada zakka…………) daga cikin misdakin kyakkyawar Magana da Alkur’ani mai tsarki ya Ambato a wannan nassi kamar yadda maluma suka bayyana shine fadar tattausar Magana cikin ladabi ko da ya kasance tare da makiya Allah ne domin yin hakan shi ke shiryar da zukata zuwa ga shiriyar Ubangiji, kamar yadda aka ruwaito a kissar ma’aikan Allah Annabi Musa da dan uwansa Harun amincin Allah ya tabbata a garesu,a cikin Suratu Taha Aya ta 43 da kuma ta 44 Allah madaukakin sarki ya ce:(ku ta fi wurin fur’auna, don ko hakika ya yi tsaurin kai* sannan ku gaya masa Magana mai taushi, ko wata kila zai karbi galgadi ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah)) abin fahimta a wannan Nassi shine kyakkyawar magana nada tasiri mai girma wajen sanya mutune ya tuna da gaskiyar da aka gyayamasa a cikin fitirarsa kuma ya karbeta.masu saurare, shugaban shiriya zababbe amincin ubangijinmu ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu zuwa ga girman ladan da Allah madaukakin sarki ya tanadarwa wadanda suka dabi’antu da irin wadannan dabi’u masu albarka, a wata riwaya da bangarori biyu suka ruwaito wato sunna da shi’a Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce:(tsarkakekkiyar magana da hikima  Sadaka ce) kuma dukkaninmu mun san cewa irin ninkin baninkin Ladan  da Allah madaukakin sarki ya tanadar ga wanda ya bayar da sadaka domin shi Allah mayalwaci ne masani kamar yadda ayoyi da dama suka bayyana a cikin Alkur’ani mai girma.hadisai da dama sun bayyana cewa fadar kyakkyawar magana da kuma alheri shine mafi fifikon  Infaki saboda Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Mahasin, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( na rantse da wanda raina ke hanunsa babu wani Infaki da mutane da su yi da ta fi fadar maganar Alheri) har ila yau wasu hadisan sun bayyana mana irin girmar ladan da mai irin wannan hali zai samu, mafi girmansa shine Rahamar Allah ta iyakancesa kuma ya amintu daga fishin Ubangiji. A cikin Littafin Mahasin an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce :(Allah ya yi rahama ga Bawan da ya fadi Alheri ya kuma amfanu, ko kuma ya yi shuru daga fadar mumunar Magana  ya kuma amintu). Kamar yadda daga cikin albarkatun fadar alheri samun kyakkyawen rabo a Duniya da kuma kyakkyawen Ambato a tsakanin Al’umma.a cikin Littafin Almahasin Amiri mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s)  ya ce:( ku fadi Alheri kuma ku san shi, ku aikata Alheri  ku zamanto daga cikin alhlinsa) da fatan Allah ya arzuta mu da irin wadannan kyawawen dabi’u.


***************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.