Mar 04, 2016 15:39 UTC
  • zababun Aiyuka-Fada kan Sani

shirin na yau zai yi bayyani kan fadar Magana a kan sani ma’ana kada mutune ya firta wata Magana matukar ba ya nada sani ba ne a kanta da kuma tabbaci a kan sahihancinta ba domin hakan na daga cikin misdakin kyawawen dabi’un musulinc


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan fadar Magana a kan sani ma’ana kada mutune ya firta wata Magana matukar ba ya nada sani ba ne  a kanta da kuma  tabbaci  a kan sahihancinta  ba  domin hakan na daga cikin misdakin kyawawen dabi’un musulinci, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


****************************Musuc*****************************


Masu saurare musulinci bai yarda mutune ya fadi wani abu a kan hashashe ba, idan zai fadi wata Magana, ya kamata ya tabbatar da sahihancinsa da kuma matsayinta  a hukuncin Addinin Islama, kada kuma ya danganta wata Magana da Addini matukar bai tabbatar da cewa Addinin ce, a cikin suratu Isra’I Aya ta 36 Allah madaukakin sarki ya ce:(kada kuma ku dinga bibiyar abin da ba ka da ilimi a kansa, hakika Ji da gani da kuma tunani duk wadannan sun zama abin tambaya a gare shi game da su) ,babu shakka a cikin dukkanin abinda Allah madaukakin sarki ya arzuta bawansa da shi na ji, gani,  da saurensu dukkaninsu domin ya cimma ilimin wadatacce kada ya firta wata Magana sai a kan sani. Masu saurare hadisai da dama sun umarci mumuni da ya dabi’antu da irin wadannan kyawawen dabi’u, abinda ya sani mai yawa ne ko kadan, dukkanin abinda zai fada ya fade a kan sani, a cikin littafin Mahasin Shek Abu Ja’afar Barki ya ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce: (na haneku da ababe guda biyu, yiwa Mutane fatawa da ra’ayi, fadar abinda ba ku sani a kansa), a cikin Littafin Uyunul Akhbar na shek Saduk an ruwaito hadisi daga Imam Aliyu bn Musa Arridah (a.s) ya ce: (duk wanda ya yi wa Mutane Fatawa da ra’ayinsa Mala’ikan dake cikin sammai da kasai sun cine masa)


Wasu hadisan kuwa sun yi galgadin cewa duk wanda ya fadi abinda bai sani ba kuma wani ya yi aiki da maganarsa za a dora masa zunuban duk wadanda suka yi aiki da abinda ya fada.Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(duk wanda ya yi wata fatawa ba tare da ilimi ba, da kuma shiriya daga Allah ba, Mala’ikan Rahama da na Azaba za su tsine masa kuma za a labta masa zunuban dukkanin wadanda suka yi aiki da wannan fatawar ta sa)


Masu saurare a cikin wata riwayar shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya karantar da mu yin ihtiyati wajen iltizami da irin wadannan kyawawen dabi’u, a wani hadisi da shek Abu Ja’afar Barki ya ruwaito, yayin da yake wa sahabansa wasiya Imam (a.s) y ace:(idan aka tambayi daya daga cikinsu bisa wani abu da bai sani ba, to ya ce bai sani ba, kada  ya ce Allah ne masani, domin yin hakan zai sanya kokonto a cikin zuciyar sahibinsa, kuma idan wanda aka tambaya ya ce bai sani ba, to kada wanda ya tambayi ya tuhume shia kan gaskiyar da ya fada ).malumam hadisi sun yi sharhi kan maganar Imam (a.s) na cewa kada ya ce Allah ne masani domin shi wanda ya tambayar na iya fahimtar cewa wanda ya tambayar ya sani kuma Allah ne mafi sani da shi  domin saboda kada wannan shakku ya shiga cikin zuciyarsa abinda ya fi Alheri shine ya ce bai sani ba kamar yadda Imam (a.s) ya bayyana. Har ila yau kamar yadda imam (a.s) ya ce kada matanbayi ya tuhumi wanda ya tambaya saboda ya ce bai sani ba, abinda ya kamata ya kimamashi saboda ya sabawa son ransa kuma ya fada masa gaskiya.


**************************Musuc***********************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan mahimancin ciyarwa ko kuma muce ciyar da Mutane domin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa,Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(aiyuka guda uku da Allah madaukakin sarki ya fi so , na farko musulmi ya ciyar  dan uwansa musulmi, na biyu ya fitar da shi daga cikin wani kangi da ya shika , sai kuma na uku ya biya masa bashi idan ana bin sa)


Hakika Allah madaukakin sarki ya yabawa iyalan gidan Masoyinsa Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka saboda yadda suka aiwatar da wannan kyakkyawar dabi’ar a cikin kisar cika alkawarin da suka dauka na Nazr ko kuma mu ce bakance bayan da Imam Husain (a.s) ya samu lafiya, inda suka yi Azumin kwanaki uku ba tare da sun ci wani abinci ba face ruwa kamar yaddar kisar ta zo a cikin Alkur’ani mai girma, a cikin Suratu Insan Aya ta 8 da kuma ta 9 Allah madaukakin sarki ya ce:(Suna kuma Ciyar da abinci tare da suna son sa,ga miskini da maraya da kuma ribatacce a yaki* (suna cewa) Mu Kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah,ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinku),Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s)  a cikin wata riwaya da aka ruwaito cikin Littafin Kafi Ya ce: (Mu Iyalan gidan Ma’aikin Allah an umarcemu da mu ciyar da abinda ke hanunmu kuma mu yi salla a lokacin da Mutane suke barci) hakika masu saurare wannan it ace  alamar bayin Allah na gaskiya kamar yadda shugaban shiriya Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( mafi Alheri daga cikinku wanda ya ciyar da abinda ke hanunsa kuma ya bayyana sallama ya kuma yi salla a yayin mutane ke barci) kitabu khisal na shek saduk.


Masu saurare a wani hadisin kuwa an bayyana cewa dabi’antuwa da wannan dabi’a mai kyau zai zamanto sanadiyar shiriya , hakika sikatu islam Kulaini a cikin Littafinsa Alkafi ya ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s)  ya ce an zowa ma’aikin Allah (S.A.W) da firsunoninn yaki sai mala’ika Jibrilu (a.s) ya zo da Labarin halayen daya daga cikinsu ,Imam Sadik (a.s) ya ce:  sai Mala’ika Jibrilu (a.s) ya ce   Ya Muhamad Ubangijinka yana gaishe da kai kuma yana cewa wannan dan kason ya kasance mai ciyar da abin hanunsa yana kuma girmama baki, yana hakuri a kan wadanda suke aiki a kalkashinsa , kuma yana biya ma wadanda ake bin su bashi ba su kuma da halin biya. Sai Ma’aikin Allah (S.A.W) ya sanarwa wannan Mutune abinda Mala’ika Jibrilu ya fada a kansa kuma ya ce masa hakika na ‘yantar da kai. Sai wannan Mutune ya ce shin Ubangijinka ya na son wannan dabi’u, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya amsa masa da cewa Na’am  sai Mutuman nan ya ce na shaida babu wani abin bauta sai Allah kuma na shaida kai ma’aikin Allah ne, ) a karshe masu saurare bari mu karanto wani hadisi daga Imam Sadik (a.s) inda yake bayyana girman ladan ga mai irin wannan hali mai kyau,Imam (a.s) y ace:(duk wanda ya ciyar da wani Mutune har ya koshi babu wani da ya san irin girman Ladan da za a bashi ko mala’ikai makusanta, ko kuma Annabawa ma’aika sai Allah Ubangijin Talikai, hakika daga cikin ababen da suke wajabta shiga Aljannada kuma gafarar Ubangiji shine ciyarwa ma’ana  ciyar da Abinci)


***************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.