Mar 04, 2016 15:40 UTC
  • zababun Aiyuka-Mahimancin Ciyarwa

shirin zai yi bayyani kan mahimancin ciyar da Mutane a musulinci


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin ciyar da Mutane a musulinci, domin mahimancin maudu’in za mu ci gaba da shi, kafin shiga shirin bari mu saurari abinda aka yi tanadi a kan faifai.


*****************************Musuc******************************


Masu saurare kamar yadda mun kawo muku hadisan da suke bayyani kan cewa Allah madaukakin sarki ya na son masu ciyar da Mutane kuma yin hakan na daga cikin dabi’un masu kirma da karamci,wasu hadisai sun bayyana cewa ciyarwa na daga cikin alamar Imani na gaskiya, a cikin Littafin Almahasin an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Imani shine kyawawen dabi’u da ciyarwa). Masu saurare dabi’antuwa da dabi’un ciyar da Mutane na daga cikin hanyoyin da Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin wasilar samun rabauta da gidan Aljanna kuma wannan shine abinda muka fahimta a cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Kafi daga Mu’amar bn Khalag ya ce:(baban hasan Imam RIdha (a.s) ya kasance  idan zai  ci abinci a kan zo masa da wata Tasa a ajiye ta a gurin cin abincinsa sai ya zabi mafi kyawon abinci daga cikin abincin da aka kawo masa zai ya zuba cikin wannan tasa sannan ya baiwa miskinai sannan sai ya karanto wannan Aya mai albarka (To, me ya hana shi kutsawa cikin Akaba*Ba kuwa an sanar da kai mene ne akaba ba?*shi ne ‘yantar da mutune (wato Bawa ko Baiwa)* ko kuma ciyarwa a cikin ma’abociyar yunwa).suratu Baladi daga Aya ta 11 zuwa 14,sannan Imam ya ci gaba da cewa ba ko wani mutune ne ke da ikon ‘yantar da Bawa ba sai Allah madaukakin sarki ya samar masa da wata hanya mai sauki  wacce  za ta yi sanadiyar shiga Aljanna shine ya ciyar da abincin dake hanunsa). Masu saurare ciyarwa bai takaita kawai a kan miskinai ko mabukata ba, ya shafi duuaknin Mutane gaba daya talakawa da masu kudinsu, a cikin Littafin Almahasin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s)ya ce:(babu wani mumuni da zai ciyar da Dan Uwansa Mumuni mabukaci ne ko kuma mai Hali ne sai ya kasance an bashi ladan wanda ya ‘yantar da Bawa daga cikin diyan Isma’el).har ila yau a cikin Litattafan Almahasin na shek Barki da kuma Kafi na Shek Kulaini an ruwaito hadisi daga Husain bn Na’im yace (baban Abdullah Imam Sadik (a.s)ya ce da ni shin kana son ‘yan uwanka  ya kai Husain?(wato ‘yan uwansa na Imani) sai na ce masa  Na’am sai Imam (a.s) ya ce kana taimaki mabukatansu?, sai na ce Na’am sannan ya ce shin kana kiransu gidanka? Sai na ce ba na ma cin abinci sai tare da Mutune biyu ko uku daga cikinsu, sai Imam (a.s) ya ce: falalarsu a kanka ya fi girma daga falarlar da ka samu  a garesu, sai na ce in kiransu gidana, in ciyar da su abincina, in kuma shayar da su, sannan ya kasance sun fi ni falala? Sai imam (a.s) y ace haka abin yake domin idan su suka shiga gidanka, sun shiga da Arziki mai yawa daga Allah kuma ya amfanaika  kai da iyalanka, idan kuma suka fita daga gidanka za su fita da zunubanka gami da na iyalanka) masu saurare wannan hadisi na kwadayar da mu na mu dabi’antu da irin wadannan kyawawen dabi’u masu Albarka domin cin ribar duniya da Lahira da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon aiki da kuma dabi’antuwa da irin wadannan kyawawen dabi’u masu Albarka.


******************************Musuc*******************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimanci kyakyawar mu’amala tare da makwabci domin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki ya yi wasiti a kansa, a cikin suratu Nisa’I Aya ta 36 Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma ku bauta wa Allah kada ku tara komai da shi,kuma ku kautata wa mahaifa, da dangi, da marayu, da miskinai, da makobci na kusa, da makobci na nesa,da abokin tafiya, da abinda hannayenku suka mallaka, (watau bayi) hakika Allah ba ya son wanda ya zamanto mai takama mai fariya) hakika maluman Tafsiri sun bayyana cewa abinda ake nufi da kyautatwa makobci na kusa wanda yafi kusa da gidanka kamar makusancin ka na jinni, kazalika abinda abinda ake nufi da makobci na nesa wanda yake nesa da kai a bangaren jini ko kuma wanda yake nesa da gidanka kuma wannan shine abinda wannan hadisi ke tabbatar da shi,a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce: (makwobci shine duk wanda gidansa ke makwobtaka da kai har gida 40 na shashen damar gidanka da kuma sashen hakun kinsa, da kuma sashen gabansa gami da sahsen bayansa, dukkanin wadannan gidaje na a matsayin makwobtanka suke ), masu saurare hadisai da dama sun bayyana mahimancin hakin makwabtaka tare da yin ta’akidi wajen kiyayesa kamar yadda shugabanmu Imam Aliyu bn Husain Zainul Abidin (a.s) ya bayyana a cikin Littafinsa mai albarka wato Risalatu Hukuk  (amma hakin makwobcinka ka kiyaye shi a yayin da ba shi nan, ka girmama shi a gabansa kuma ka taimakeshi a yayin da aka zalunceshi,ka kadda ka kasance mai kokonto wajen neman aibinsa, idan ka san wani mumunan abu a gareshi ka suturta shi, kuma idan ka san yana daukar nasiharka to ka yi masa nasiha a tsakaninka da shi, kadda ka bar shi a yayin da ya shigac cikin tsanani, ka yafe masa laifin da ya yi maka kuma ka yi kyakyawar mu’amala tare da shi).


Masu saurare daga cikin kololuwar martaba na kyakyawen makobtaka, hakuri a kan tsutarwar da makwobcinka ya yi maka domin riko da wasici da kuma kwadayi wajen Allah madaukakin sarki wanda ya yi wasiya a kan kyautata masa, hakika cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Musa Alkazim (a.s) ya ce: (babu kyakyawar makwobtaka kamar kiyeye cutar da makwabci, kazalika babu kyakyawar makwabtaka kamar yin hakuri bisa cutarwa ta makwabci). Har ila yau a cikin Littafin Kafin an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) ya ce: (wani Mutune ya je wajen Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya kai karar makwabcinsa bisa zutarwar da yake yi masa, sai Ma’aikin Allah ya ce masa yayi hakuri, bayan wani lokaci ya sake komawa ya kai karar makwabcinsa a karo na biyu sai Ma’aikin Allah ya sake bashi hakuri….) a wani hadisi na daban da a ruwaito  cikin Littafin Kafi, Amru bn Akrama ya ce:(na shiga wajen babban Abdallah Imam Sadik (a.s) sai na ce masa makwabcina ya na cutar da ni, sai ya ce : ka jikansa)


Bayan wadannan Lada mai dunbun yawa, kyakyawar makwabtaka na yin sanadiyar karin Arzuki da kuma karin yawan shekaru a nan duniya gami da sake farfado  gidaje kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana (kyakyawar makwabtaka tana raya gidaje kuma tana kara yawan shekaru) a wani hadisin kuwa Imam (a.s) ya ce:( kyakyawar makwabtaka tana kara yawan arzuki), da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu iko na amfani da wadannan hadisai masu albarka.


***************************Musuc***************Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai