Mar 04, 2016 15:42 UTC
  • zababun Aiyuka-Kyakkayar mu'amala da abokin Tafiya

shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kyakyawar mu’amala tare da abokin tahiya domin shima na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kyakyawar mu’amala tare da abokin tahiya domin shima na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so , amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


**********************************Musuc**************************


Masu saurare kyakyawar mu’amala tare da abokin tahiya daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so, kamar yadda shugaban Halittu Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yi ishara da hakan , a cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Man La Yahduruhul Fakih na shekh Saduk:(babu wasu Mutane guda biyu da za su yi tafiya tare sai ya kasance daya ya fi dayan lada da kuma samun soyayyar ubangijin wanda yafi kuma shine , wanda ya fi tausayin sahibinsa daga cikin su).masu saurare irin wadannan dabi’u sune wadanda Allah madaukakin sarki ya yi mana wasici a cikin Littafinsa mai tsarki. Hakika maluman tafsiri sun bayyana cewa abokin bulaguro shine misdakin (والصاحب بالجنب) wato da abokin tafiya wanda aka Ambato a cikin suratu Nisa’I Aya ta 36 daga cikin gungun da Allah madaukakin sarki ya yi wasiti na a kyautata musu bayan da ya yi umarni na a bauta masa shi kadai ba tare da abokin tarayya ba, har ila yau daga cikin misdakin dabi’antuwa da irin wadannan kyawawen dabi’u shugabanmu Sayidi sadikin (a.s) ya shiryar da mu cikin littafinsa mai Albarka da ake kira da Risalatu Hukuk yayin da yake cewa : (amma hakin Abokinka ka kasance tare da shi cikin daukaka gami da yin masa adalci, ka girama shi kamar yadda yake girmamaka, kada ka gyale shi ya zarce ka wajen girmama juna, idan ya ci gabanka ka sakamasa,  ka kasance masa Rahama kadda ka kasance Azaba a gareshi……………) har ila yau daga cikin misdakin  kyakyawar abotaka, hadisin da Alama Tabrasi ya ruwaito cikin Littafin Makarimul Akhlaq inda a cikinsa aka ce Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya kasance daga  cikin wani bulaguro da yayi tare da sahbansa, ya umarce su da suke yanke wata tunkiya sai daga cikin sahabansa wani ya ce ni zan yankata, wani kuma  yace ni zan fede ta, wani kuma yace ni zan yayyankata wani kuma ya ce ni zan dafa ta, sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce ni kuma zan tattaro itace, sai sahaban suka ce masa ya Ma’aikin Allah ka bari mu mun isar maka, sai ya ce hakika na san kun isar muni amma Allah madaukakin yana kin bawan da yake tare da sahabansa ya kuma kadaita daga cikin su (ma’ana ya babbanta kansa da su), Ma’aikin Allah (s.a.w) ya tashi ya tattaro musu itace da za su dafa wannan dabba). A cikin wata riwayar ta daban , wacce Sikatu Islam Kulaini ya ruwaito a cikin Littafinsa na Kafi ta yi ishara da cewa kyakkyawar mu’amala tare da abokin bulaguro ta kan zamanto sanadiyar shiriyarsa  da Addinin Allah madaukakin sarki, hakika an samo hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya kasance da wani Mutune daga cikin Ahlilkitabi a yayin wani bulaguronsa, sai wannan Mutune ya ce masa ya kai Bawan Allah ina zaka? Sai Amiru mumunin ya ce zan tafi garin Kufa ne, lokacin da suka isa mararraba wato daidai lokacin da hanya za ta rabasu sai Imam Ali (a.s) ya yi wa  wannan Mutune rakiya , sai Mutuman nan ya ce masa shin ba Kufa zaka ba? Sai Imam (a.s) Eh! Sai Mutuman nan yace masa to ay kabar hanyarka? Sai Imam(a.s) ya ce  masa hakika na sani, sai Mutuman ya ce to mi ya sanya ko biyo ni  bayan kasan hakan? Sai Imam ya ce masa wannan na daga cikin cikar kyakyawar mu’amala tare da abokin tafiya ,idan mutune zai rabu da abokin tafiyarsa yayi masa rakiya tare da fatan Alheri, kuma haka Annabinmu (s.a.w) ya umarcemu…… sai wannan Mutune  ya ce babu Laifi kabi wanda ya bika da aiyukan Alheri , kuma na shaida maka cewa hakika na gamsu daAddininka, Imam Sadik (a.s) ya ce sai wannan Ahlilkitab ya bi Amiri mumunin (a.s)suka isa garin KUfa  bayan kuma yayi masa bayyani, sai ya musulinta).


*****************************Musuc******************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi bayyani a kan nisantuwa daga yiwa Mutane hasada,ma’ana, kyashi da kuma yin hasada a kan wata ni’ima da Allah madaukakin sarki ya horewa wasu daga cikin bawinsa tare da fatan kushewar hakan, a cikin littafin Tuhuful Ukul na shekh Jalil bn Shu’ub Albahrani, an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Musa Alkazim (a.s) yayin da yake yiwa daya daga cikin sahabansa salihin bawannan Hisham bn Hakam wasiya ya ce: (Ya Hisham babban abinda ya fi kusanta Bawa ga Ubangijinsa shine sanin sa,Salla, yin biyayya ga Ma’aifa, barin hasada, jiji da kai da kuma Alfahari), masu saurare nisantar hasada na daga cikin ababen da suke kiyaye Imani da kuma zaunar da shi a cikin zukata kamar yadda shugaban halittu Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu, a cikin Littafin Kurbul Isnad an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce: (hakika Ma’aikin Allah (s.a.w) ya bayyana cewa  kada ku yi hasada domin ita hasada tana cin Imani kamar yadda wuta ke cin busasun itace).a cikin wata  khuduba da Manzon Allah (s.a.w) ya yi a ranar Qadir ya ce:( Ya Ku Mutane, hakika Iblis shine ya fitar da kakanku Annabi Adam (a.s) daga Aljanna saboda Hasada, kada ku yi hasada ta bata muku aiyukanku, domin Annabi Adam (a.s) an fitar da shi zuwa doron kasar saboda laifi guda daya shine hasadar da aka yi masa har ta kai  ya ci  itaciya alhali yana daga cikin zababbun Allah, to yaya zai kasance ta ku alhali ku ku ne).


A cikin Littafin Alwasa'il an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) inda yake Ambato mumunan sakamako na mai yin hasada wajen bata aiyuka na gari, Imam (a.s) ya ce:( hakika Ma'aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka wata Rana yace wa Sahabansa hakika Allah madaukakin sarki ya fitar muku da abinda ya  cutar  Al’ummar da suka gabace ku,shine Hasada domin ita hasada tana shafe Addinin Mutune,).da fatan Allah madaukakin sarki ya tsarkake zukatanmu daga Hasada saboda shugaban halittu Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.


****************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.