Mar 04, 2016 15:44 UTC
  • zababun Aiyuka-Nisantar Hasadda

a shirin zai yi bayyani kan mahimancin kiyaye kai da kuma tsarkaka daga hasadda da kyashi a kan wata ni’ima da Allah madaukakin sarki ya horewa wani bawansa tare da fatanwannan tushewarta


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin kiyaye kai da kuma tsarkaka daga hasadda da kyashi a kan wata ni’ima da Allah madaukakin sarki ya horewa wani bawansa tare da fatanwannan tushewarta , domin mahimancin wannan maudi’I za mu dora daga inda muka dakata a makun da ya gabata, amma mu shiga cikin shirin ga wannan.


**********************Musuc*********************************


Masu saurare, tsarkaka daga dabi’ar hasada na daga cikin wasicin Allah madaukakin sarki ga Annabawansa masu girma amincin Allah su tabbata a garesu, kamar yadda shugabanmu Mustafa Al-Amin tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana a cikin wata riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Alwasa’il:(Allah madaukakin sarki ya cewa Musa bn Imran (a.s) ya kai dan Imran, kada ka yiwa Mutane Hasada a kan abinda muka basu na falala, kuma kada ka meka hanunka a kan su, kadda kuma kabi son ranka, domin mai hasada ya na fishi da Ni’imata, kuma mai kokarin tushe rabon da na rabawa bayina ne,wanda ya kasance hakan (ma’ana mai irin wannan hali), ba na tare da shi, kuma shi maba ya tare da Ni) maluman hadisai sun yi ta’aliki a karshen wannan hadisi inda suka rubuta cewa ma’anar fadar Allah(wanda ya kasance hakan ba na tare da shi, kuma shi ma ba ya tare da Ni) wanda ya jarabtu da ibtila’in hasada ya nisantu daga kyawawen dabi’un Allah madaukakin sarki. Tsarkake zukata daga yin hasada shine samun tsira da kuma waraka daga rashin lafiyar zukata da ma jiki baki daya, a cikin Littafin Alwasa’il Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya bayyana cewa:(babu abinda hasada ke janyowa illa cutarwa da fishi,tana raunana zukata, kuma tana sanya cuta a cikin jiki, mafi sharin abinda ke cutar da zukiyar Dan Adam ita ce Hasada), kamar yadda Hasada kuma ke bata aiyuka kyawawa, tana makautar da zukata, ta jefa mai yinta ya kafircewa ni’imar Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Misbahu Shari’a, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Mai hasada yana cutar da kansa kafin ya cutar da wanda yake yiwa hasadar, kamar Iblis ne da ya gadawa kansa La’ana kafin ya gadarwa Annabi Adam(a.s) kaucewa, shiriya, da kuma fita daga gurin tabbacin Alkawari da zabi, ka kasance wanda ake yiwa hasada ba mai hasada ba,domin ma’aunin mai hasada har abada haloko ne dangane da wanda ake yiwa hasada, kuma kan san cewa Arziki rabebbe ne, asalin hasada kuma tana makautar da zukata,da kuma kafircewa falalar Allah)


Daga cikin misdakin hasada, da ya kamata bawa Bawa ya tsarkaka da ita, yin inkari ga matsayin da kuma falalar da Allah madaukakin sarki ya baiwa waliyai da kuwa wasu zababbun mumunai, kamar yadda shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya bayyana a cikin wani hadisi da aka ruwaito cikin Littafin Kafi (ku ji tsoron Allah kada kuma ku yi hasada ga shashinku, hakika Annabi Isa Dan Maryamu (a.s) ya kasance daga cikin dokokinsa yana zuwa gari gari,a cikin wata fita da yayi yana tare da wani Mutune daga cikin sahabansa mai suna Kusair  wanda kuma ya kasance yana yawan bin Annabi Isa (a.s), a yayin da suka isa wani teku, sai Annabi Isa (a.s) ya ce bismillahi tare da sahihancin yakini daga gareshi sannan ya bi ta bisan ruwa ya fice, shima sahabin nasa sai ya ce bismillahi tare da yakini daga gareshi sannan shima ya bi ta ruwan ya fara tafiya a bisa ruwan sai yayi mamaki sannan yayi tunanin cewa tafiyar da yake yi a bisa ruwan karamarsa ce ba wai karamar Annabi Isa ba,sai Yace ga Annabi Isa Ruhullah yana tafiya a bisa Ruwa kuma Ni ma ina tafiya a bisa ruwa, to minene fifikonsa a kaina? Wato da mi ya fini, Imam Sadik(a.s) ya ce  yana fadar haka sai ya nutse, sai Annabi Isa (a.s) ya cece shi, sannan yace masa minene ka fada Ya Kusair?sai ya ce cewa na yi ga Annabi Isa Ruhullah yana tafiya a bisa Ruwa kuma Ni ma ina tafiya a bisa ruwa sai wani girman kai da Al’ajabi ya shiga cikin zuciya ta har na ce minene babbancinmu da kai. Annabi Isa (a.s) ya ce  Ya Kusai!hakika ka kai kanka inda Allah bai kaika ba,don haka ka tuba zuwa ga Allah a kan abinda ka fada,sai wannan Bawa ya tuba ga Allah ya kuma koma matsayinsa da Allah ya ajiye sa, Imam Sadik(a.s) ya ce ku ji tsoron Allah kada ku dinga yiwa junanku hasada).


****************************Musuc*******************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin za mu yi bayyani kan yadda wasu gungu na Mutane da suke murna a yayin da suka ga waninsu ya ci gaba ko kuma Allah madaukakin sarki ya arzutashi da wani abun alheri, wannan shine akasin Hasada, mumuni na kwarai inda ya gana Allah madaukakin sarki ya arzuta Dan uwansa da abun alheri zai yi godiya tare da neman allah ya albarkaci ya kuma karamasa ,shima kuma daga bangarensa zai yi Addu’a Allah ya hore masa daga falalarsa.,wannan halaye na daga Alamar sahihancin Imani kamar yadda shugabanmu Iman Sadik (a.s) ya bayyana a cikin wani hadisi da aka ruwaito cikin Kafi na sikatu islam Kulaini (hakika mumuni yana murna da abinda ya samu dan uwansa na Alheri kuma baya hasada, shi kuma mai hasada ba ya murna)  kuma domin haka ne ma yin murna a kan ni’imar da Allah ya baiwa wasu, na daga cikin halayen shugabanin salihai daga shahidai, kamar yadda shahararen hadisin nan na shugabanmu Iman Sajjad zainul Abidin (a.s) yayin da yake bayyani kan makamin Abil Fadlil Abbas(a.s) a riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Amaly na shek Saduk (hakika Abas nada matsayi , da dukkanin shahidai za su murna da shi a ranar Alkiyama) har ila yau wannan hali mai kyau na daga cikin halayen salihai daga cikin bayin Allah kamar yadda shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya bayyana cikin wani hadisi mai tsaho da aka ruwaito cikin littafin kamilu Ziyarat yayin da yake bayyana falalar kakansa Imam Husain (a.s) a cikin wani bangare na riwayar yana cewa:(babu wani matsayinsa da ya gushe tun bayan da aka kashe shi kuma duk wani masallaci daga cikin mala’iku, Aljannu da kuma Mutane yana yi masa, kuma babu wani abu a doron kasa face yana murna da wanda ya ziyarcesa,kuma yana fatan ganin Alheri a yayin da ya ziyarci kabarinsa (a.s)).masu saurare bayyana Murna bisa Alherin da wani ya samu na daga cikin halayen da Allah madaukakin sarki yake so,domin haka dabi’antuwa da wannan dabi’a mai kyau na kusantar da Bawa wajen Allah Tabaraka wa Ta’ala, Muhamad bn Mahmoud Ayyashi ya ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Iman Sadik (a.s)ya ce: (yayin da Annabi Musa dan Imrana (a.s) yana munajati da Ubangijinsa sai ya ga wani Mutune kalkashin inuwar Al’arshin Ubangiji, sai ya ce Ya Ubangiji wanene wannan da ka sanya kalkashin inuwar Al’arshinka? Sai madaukakin sarki ya ce Ya Musa wannan na daga cikin mutanan da ba sa yiwa Mutane hasada  a kan abinda Allah ya basu daga falalarsa) da fatan Allah ya sa mu dace da irin wadannan kyawawen dabi’u.


****************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.