Mar 04, 2016 15:46 UTC
  • zababun Aiyuka-Kiyayye Hakin Dabbobi

shirin na yau zai yi bayyani a kan kiyayye hakin dabbobi


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani a kan kiyayye hakin dabbobi, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


***************************Musuc**************************


Masu saurare,daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki ya ke so ga bayinsa, kiyaye hakin dabobbi, a cikin littafin Khisal na Shek Saduk yardar Allah ta tabbata a gare shi, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da aimncin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Dabba nada hakki shiga a kan mai Ita, na farko ya fara bata abinci a yayin da ya sauka daga kanta, ya bata ruwa a yayin da ya bi ta hanyar Ruwan, kada kuma ya bugeta a bisa fuskarta domin tana godiyar Ubangijinta a ita, kada ya zaya a bayanta idan ba saboda Allah ba,kada ya dora mata kayan da su kafi karfinta,kuma kada ku tilasta mata tafiyar da ba za ta iya ba),a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:( ku ji tausayin Dabobbi, kada ku daure su da kaya a kansu, kada kuma ku basu ruwa  ba tare da kun fidda musu Lizzamin dake bakunansu ba,kuma kada ku dora musu kayan da suka fi karfinsu).fadar Imam (a.s) (kada ku daure su da kaya a kansu) yana ishara a kan hadisin  aka ruwaito daga Ma’aikin Allah (s.a.w) yayin da ya ga wata Taguwa a daure, kuma tana dauke da kaya, sai ya ce ina mai wannan Dabba,ku kira shi,ku gayama sa cewa ya shiryawa Khusuma a gobe).


Masu saurare dabi’antuwa da dabi’ar tausasawa Dabbobi kamar amsa kira ne ga umarnin Allah madaukakin sarki na kiyaye hakinsu, kuma cutar da su zai sanya a fuskanci fishin Allah madaukin sarki kamar yadda hadisai da suka gabata suka yi ishara da hakan , a cikin Littafin Wasa’il, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce: (a cikin wuta na ga wata Mata da ta kasance a nan Duniya, ta nada Mage kuma Magen tana ta kartonta a  gabanta da bayanta , saboda a nan Duniya ta daureta ba tare da bata abinci ba, kuma ba ta barta ba ta je ta nemi abinci a doron kasa ba, kuma dana shiga cikin Aljanna na ga wani Mutune , saboda ya kasance yana baiwa karansa ruwa a nan Duniya), har ila yau a cikin wani hadisi da aka ruwaito daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika wata Mata ta kasance cikin Azaba saboda ta daure Mage har ta mutu da ishirwa), a wani hadisi na daban Amiru Mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(kada ku biki dabba kuma kada ku la’anceta domin Allah madaukakin sarki yana La’antar mai la’antar Dabba)


Masu saurare hadisai da dama sun haramta kisan dabbobi haka nan ba tare da wani dalili ba, kuma hakan na daga cikin mafi munin zunubai da ya kamata Mutane su kiyaye, a cikin Littafin wasa’il, an ruwaito wani hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce: (duk wanda ya kashe wani tsuntsu guda cikin wasa ba tare da ya amfana da shi ba, ranar Alkiyama wannan tsuntsu zai kai kararsa wajen Allah ya ce ya Ubangiji wannan Mutune ya kashe ni haka nan kawai ba tare da ya amfanu da Ni ba, kuma bai barni na rayu daga ni’imar doron kasa ba). har ila yau a cikin wani hadisi na daban Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika mafi munin zunubi guda uku ne, kashe dabba hakan nan, taushe hakin Mace da kuma hana wanda aka sanya aiki hakkinsa).


****************************Musuc*****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani a kan mahimancin kyautatawa dabbobi domin shima na daga cikin kyawawen dabi’u da Allah madaukakin sarki yake so, a cikin littafin Munakib, an ruwaito hadisi daga Imam Aliyu bn Husain Zainul Abidin (a.s) yayin da yake yiwa Dansa Imam Bakir (a.s) wasiya kafin shahadarsa ya ce:( hakika na yi aikin hajji so 20 a bisa wannan taguwa tawa,ban taba bugonta ba ko da so guda, idan ta mutu, kuyi rami a bisne ta domin kadda dabbobin daji su ci namanta, hakika Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce babu wani ragumi ko taguwar da aka yi aikin hajji so bakwai a kansa sai Allah madaukakin sarki ya sanya shi daga cikin dabobin Aljanna, kuma ya albarkaci zuriyarsa). A cikin Littafin Kitabul Khara’ij an ruwaito hadisi daga Abdul…..bn Ja’afar yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ce :(wata Rana Ma’aikin Allah (s.a.w) ya shiga gonar wasu daga cikin mutanan Madina wato Ansar ,sai ya tarar da wani rakumi a ciki, da ma yaga Ma’aikin Allah (s.a.w) sai hawaye suka fara zuba daga idanunsa, Ma’aikin Allah ya fara shafa goshinsa har yayi shuru, sannan sai ya tambaya da mai rakumin, wani Matashi daga cikin Ansar ya ce rakumi na ne ya Ma’aikin Allah, sai Annabi ya ce masa, shin ba ka tsoron Allah a kan wannan Dabba da Allah ya mallaka maka ita? Domin yana korafin kana barinsa da yunwa kuma kana wahalar da shi), Ma’aikin Allah (s.a.w) ya kasance yana yawan yiwa sahabansa wasici na su tausayawa dabbobinsu, misali a hadisin da aka ruwaito cikin littafin Alwasa’il daga Sawadata bn Rabi’I ya ce Ma’aikin (s.a.w) ya ce masa( Ya Rabi’I idan ka koma gidanka ka umarcesu su kautata abincin dabbobinsu, kuma ka Umarcesu su dinga yanke farcen su domin kadda su cutar da dabbobinsu a yayin da suke tatsar nono a jikinsu).wannan na daga cikin kyawawun dabi’un Ma’aikin Allah tsarkaka kadda mutune ya bar farcansa yayi tsaho har ya kai ya cutar da dabba a lokacin da yake tatsar nononta.a cikin littafin Almahasin an ruwaito hadisi daga shugabanmu imam Ridha (a.s) ya ce:(wata rana Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka sai wasu Mutane suna wasa da kaza mai rai sun mayar da ita kamar kwallo suna jifa ta ita, sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce su waye wadacan? Allah ya la’ancesu) masu saurare wannan hadisi darasi ne babba a garemu domin cutar da dabba na iya yin sanadiyar Bawa yayi mumunar karshe ko da kuma ya kasance mai yawan Ibada, rashin mu’amala cikin tausayi tare da dabbobi shi zai tabbatar da cewa Ibadar tasa ba ta gaskiya ce ba, A cikin Littafin Alwasa’il, an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce :(wani Lattijo sufi mai yawan ibada daga cikin Bani Isra’ila  ya kasance yana cikin ibada sai ga wasu Matasa guda biyu suna fige gashin wani zakara rayayye, yana kallonsu bai hanasu ba , ya kuma ci gaba da Ibadarsa , sai Allah madaukakin sarki yayi wa kasa wahayi na cewa ana wulakanta Bawansa sai kasa tayi kara, shi kuma wannan Bawa ya kasance daga cikin wadanda La’anar har abada ta sauka a garesu).


***************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.