zababun Aiyuka-Mahimancin murmushi da sakin fuska
shirin na yau zai yi bayyani dangane da sakin fuska gami da murmushi ma’amanar hakan kuwa shine duk lokacin da mutune ya ga Dan uwansa ya tarbe sa cikin fara’a da murmushi wanda hakan shike daukaka ma’anar adamtaka kuma shi zai baiwa mutane damar yin mu’amala cikin nashadi da Annashuwa kuma duk wanda ya kasance mai irin dabi’u Allah madaukakin sarki zai girama shi da rabo mai yawa
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani dangane da sakin fuska gami da murmushi ma’amanar hakan kuwa shine duk lokacin da mutune ya ga Dan uwansa ya tarbe sa cikin fara’a da murmushi wanda hakan shike daukaka ma’anar adamtaka kuma shi zai baiwa mutane damar yin mu’amala cikin nashadi da Annashuwa kuma duk wanda ya kasance mai irin dabi’u Allah madaukakin sarki zai girama shi da rabo mai yawa. Kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda a kayi mata tanadi a kan faifai.
***************************Musuc***************************
Masu saurare hadisai da dama sun yi bayyani cewa kyakkyawar mu’ala tare da jama’a na daga cikin kyawawen dabi’u da Allah madaukakin sarki ya umarci bayinsa da aikatawa , a cikin Littafin Masadikatu Ikhwan, Shek saduk ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Musa bn Ja’afar Aridah (a.s) ya ce:(duk wanda ya sha ruwa a cikin modar da Dan uwansa ya sha ruwa ko kuma duk wanda ya sha sauren dan’uwansa domin kaskantar da kai da kuma tawadu’I, Allah madaukakin sarki zai sanya shi gidan Aljanna, kuma duk wanda ya yiwa Dan Uwansa mumuni murmushi Allah zai rubuta masa kyakkyawa, kuma duk wanda Allah madaukakin sarki ya rubutawa kyakkyawa, ba zai azabtar da shi ba) har ila yau a cikin wannan littafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Muhamad Bakir(a.s) ya ce:( sanya murmushi a fuskar dan uwanka mumuni , sadaka ne ,kuma hakan canza cutarwa ne da kyakkyawa, ba a bauta Allah kuma da komai ba da ya fi so kamar sanya farinciki a cikin zukatan mumuni), masu sarare daga cikin misdakin dabi’antuwa da wannan dabi’a mai kyau, rashin bayyana bacin rai da damuwa a lokacin mu’amala da marassa lafiya da kuma juriyar wahalhalun da bawa zai fuskanta wajen mu’amala da mutane gami da sakin fuska da kuma fara’a a yayin mu’amala da su, hadisai da dama sun bayyana cewa yin hakan sadaka ce mai albarka, a cikin litattafan Sawabul A’amal da kuma man La Yahduruhul fakih, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(sauraren baibai ma’ana wand aba ya jin kadan ba tare da bayyana cutuwa ba, sadaka ce mai girma), kamar yadda riko da halayen sakin fuska da fara’a tare da Mutane na daga cikin hanyoyin dake kai Mutune zuwa gidan Aljanna da kuma samun rabo na yardar Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka (kyautatawa da kuma sakin fuska suna samar da soyayya kuma suna yin sanadiyar shiga gidan Aljanna, shi kuma rowa gami da murtsuke fuska na nisantar da bawa ga Allah madaukakin sarki kuma suna yin sanadiyar shiga wuta). Masu saurare duk wanda ya kasance mai irin wadannan halaye zai samu kusanci da Ubangijinsa kuma yayi aiki da wasiyar shugaban Halittu Muhamad dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s)ya ce:(wani Mutune ya je wajen Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce Ya Ma’aikin Allah ka yi mani wasici, daga cikin ababen da yi masa wasici a kansa ya ce duk lokacin da zaka tarbi dan uwanka ka tarbe shi cikin murmishi, sakin fuska da walwala), masu daga cikin albarkar dake tattare da dabi’ar walwala tare da sakin fuska, yana kore kiyayya gami da kyashi,sannan yana wanzar da soyayya a tsakanin Al’umma, a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce(kyakkyawar mu’mala , sakin fuska gami da walwala na kore kiyayya, hasada gami da kyashi a tsakanin Al’umma) da fatan Allah madaukakin sarki ya kiyaye mu da irin wadannan munanan dabi’u.
**************************Musuc******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani dangane sassauti a yayin mu’amala da Mutane domin shi ma na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so ga bayinsa a cikin littafin Amaly na shekh Tusy an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce(mumuni yanada saukin kai, ya kan gudanar da mu’amalarsa cikin sauki kuma yanada kyawawen dabi’u, shi kuma kafiri yanada tsanani, mu’amalarsa ta kan kasancewa cikin tsauri kuma yana munanan dabi’u), masu saurare, sausauci wajen mu’amala da Mutane adon imani ne, a cikin Littafin Amaly, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam sadik (a.s) ya ce (adon Imani, sanin ilimin Addini, sanin ilimin Addini, hakuri, adon hakuri, tausayi, adon tausayi, tattausar magana, adon tattausar magana,sassauci), dabi’antuwa da dabi’ar sassauci wajen mu’amala tare da Mutane na daga cikin hanyoyin dake tsiratar da Bawa shiga wuta da kuma samun babban rabo na gidan Aljanna, a cikin Littafin sawabul a’amal shekh saduk ya ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce wa sahabansa(ku saurara! Ku na son in baku labarin abinda zai kiyaye ku da shiga cikin wuta a ranar gobe? Sai suka ce Na’am ya Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce tattausar magana da kuma sassauci a yayin mu’amala da Mutane), hakika daga cikin misdaki da kuma tabbacin wannan dabi’a mai albarka, kyawawen dabi’u a yayin mu’amala da halittun Allah, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito wani hadisi, inda a cikinsa wani Mutune ya tambayi Imam Sadik (a.s) dangane da iyakar kyawawen dabi’u, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa (ka zamanto mai tausayi da sassauci ga wanda ke kalkashinka da kuma na kusa da kai, ka kyautata kalamanka, ka kuma tarbi dan uwanda da fara’a cikin mulmushi), a wani Hadisin kuwa, Imam Sadik (a.s) ya ce :(ababe guda uku duk wanda ya zo da daya daga cikinsu, Allah ya wajabta masa gidan Aljanna,ciyar ga mabukata,bayyana fara’a ga dukkanin Mutane, yin adalci ga kai).
Masu saurare daga cikin misdakin wannan dabi’a mai albarka, sassauci da kuma kyakkyawan bayyani cikin mu’amala tare da Mutane a bangaren kasuwanci, kuma wannan na daga cikin dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so kuma ya albarkanci arzikin da wanda ya yi iltizami da shi, kuma ya yi masa gafara,a cikin Littafin Attahzib na shekh Tusy, an ruwaito hadisi daga Imam sadik (a.s) ya ce Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce : (Allah yayi albarka ga kasuwanci da aka yi cikin sauki, da kuma siyayyar da aka cikin sauki,zartar da hukunci da kuma shara’ar da aka yi cikin sauki).a cikin Littafin Man La Yahduruhul fakih,an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(hakika Allah madaukakin sarki ya ce yana son Bawan da zai kasance siyayyarsa da sayarwarsa cikin sauki,zartar da hukunci da kuma shara’arsa cikin sauki). Har ila yau a cikin Littafin Alkhisal an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(Allah ya yi gafara ga Mutunan da suka gabace ku, siye da sayarwarsu cikin sauki, kazalika gudanar da hukuncinsu cikin sauki) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu damar amfani da abinda muka saurara.
****************************Musuc*****************************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.