Mar 04, 2016 15:49 UTC
  • zababun Aiyuka-Mahimancin cika Alkawari

shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin cika Alkawari


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin cika Alkawari amma kafin shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan fafai.


**************************Musuc*********************************


Masu saurare, cika alkawari na daga cikin kyawawen dabi’u da Allah madaukakin sarki ke so ga bayinsa  kuma yake yabawa masu irin wannan hali, wannan shine abinda za mu fahimta a cikin suratu Maryam Aya ta 54 da kuma 55, Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma ka ambaci (labarin) Isma’ila a cikin Littafi (Alkur’ani). Hakika shi  ya zama mai cika alkawari ne, kuma ya kasance Annabi (kuma)Manzo. Kuma ya zamanto yana umartar iyalansa da (tsai da) salla da kuma (ba da) zakka,kuma shi yardajje ne a wurin Ubangijinsa) imam Sadik (a.s) ya bayyana dalilin da ya sanya ake kiran Annabi Isma’ila da lakabin mai cika alkawari, a cikin Littafin Kafi Sikatu Islam Kulaini ya ruwaito wani hadisi daga Imam (a.s) ya ce(an kira Annabi Isma’il (a.s) da Lakabin mai cika alkawari, domin ya baiwa wani Mutune alkawari a wani guri bai zo ba, Annabi Isma’il (a.s) ya jira  shi har tsahon shekara guda a wannan guri, shine Allah madaukakin sarki ya kira shi da mai cika alkawari, sannan wannan Mutune ya zo masa, lokacin da wannan mutune ya zo sai Annabi Isma’il (a.s) ya ce masa na kasance cikin jira dangane da wannan batu wato alkawarin da muka yi), hadisai da dama sun bayyana cewa cika alkawari na daga cikin alamar imani da Allah da kuma Ranar Alkiyama, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da aimincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya yi Imani da Allah da kuma Ranar Lahira ya cika Alkawari idan ya dauka) har ila yau a cikin littafin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) inda yake bayyana mana mumunar makoma na wanda ke karya alkawari, imam (a.s) ya ce alkawarin mumuni ga dan uwansa fakance ne da babu gafara a kansa, duk wanda ya saba, ya san cewa ya fara saba alkawrin Allah ne kuma wannan shine ma’anar fadar Allah madaukakin sarki (Ya Ku wandanda kuka bada gaskiya don me kuke  abin da ba kwa aikatawa? Ya isa abin Ki a wurin Allah ku rika fadin abin da ba kwa aikatawa) suratu Saffi Aya ta 2 da ta 3.a cikin littafin Ilalu Shara’I’I an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce (wata Rana Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yiwa wani Mutune alkawari a cikin dokar daji na sahara, Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce masa ina nan har ka dawo, mutuman bai dawo ba har zafin rana yayi tsanani ga Ma’aikin Allah cikin tsananin rana, sai Sahabansa suka ce masa Ya Ma’aikin Allah da ka koma cikin Inuwa, sai Ma’aikin Allah ya ce da su hakika a nan na yi masa alkawari kuma a nan ne ya dace in tsaya har da dawo,idan kuma bai dawo ba , saba alkawarin zai kasance daga wajensa har tashin Alkiyama)


*************************Musuc***************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani dangane da dabi’ar kunya domin Allah madaukakin sarki na son mutune mai kunya, a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa (hakika Allah yana son Mai kunya, mai hakuri da kuma mai kamun kai) irin wadannan halaye masu kyau na daga cikin halayen da iyalan gidan Ma’ailkin Allah (a.s) ke so, a cikin littafin Kafi an ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika mu muna son wanda ya kasance mai hankali, mai fahimta, mai hakuri, da kuma wanda ya iya tafiya da zama da mutane cikin siyasa, mai tsananin hakuri, mai kuma cika alkawari, hakika Allah madaukakin sarki ya kebe wadannan kyawawen dabi’u ga Annabawansa masu girma, duk wanda ya kasance ya nada irin wadannan dabi’u sai ya godewa Allah, wanda kuma ba shi da su ya gaggauta komawa wajen Allah ya tambayesa ya kuma ya arzuta shi da irin wadannan kyawawen dabi’u, sune, tsoron Allah, dangana, hakuri, godiya, tsananin hakuri, kunya, kauta, karfi, kishi,biyayya, gaskiya da kuma rikon Amana)


Masu saurare, ma’anar kunya shine mutune ya kaucewa duk wani abu da zai yi wanda zai sanya sunansa ya bace ko kuma a dinga bata shi, ana kuma nuna shi saboda ya aikata wannan aiki,wannan dabi’a mai kyau na daga dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so ga bayinsa kamar yadda ma’aikin Allah (s.a.w) ya bayyana a wani hadisi daSalman Muhamadi yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ruwaito, (hakika Allah madaukakin sarki mai kunya ne kuma mai karamci ne, yana jin kunya a yayin da bawan ya daga  hanunsa ya rokesa wani abu  ya hanashi (wato Allah madaukakin sarki yana jin kunya ya hana Bawa a lokacin da ya daga hanuwansa ya roke shi wata bukata) har sai ya sanya wani alheri a cikinsu) har ila yau masu saurare, dabi’antuwa da wannan dabi’a mai kyau na daga cikin gaskiyar imanin Bawa ga Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Ma’anil Akhbar an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa (kunya da Imani suna cikin karni guda, duk lokacin da daya ya gushe sai dayan ya bi bayansa) har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce (babu imani ga wanda ba shi da kunya) har ila yau daga cikin albarkatun dake tattare da irin wadannan dabi’u masu albarka, shafe zunubai, domin su wata hanya ce na tsarkaka daga zunubai da kuma kaurace musu,a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) na cewa (ababe guda hudu, duk wanda ya kasance yana su  kuma ko da ya kasance zunubansa sun kai girman daga wuyansa zuwa diddiginsa za a canza su zuwa kyawawan aiyuka, fadar gaskiya da kuma yin gaskiya a cikin Al’amuransa, kunya, kyawawen dabi’u da kuma godiya) kamar yadda suke kasancewa wasila ne na suturta aibi mai su, a cikin littafin Man La Yahduruhul Fakih an ruwaito hadisi daga shugaban mumunani Aliyu bn Abi Talib (a.s) yayin da yake yiwa Dansa Muhamad Bn Hanafiya wasiya ya ce masa(duk wanda ya sanya rigar kunya ,dukkanin aibinsa zai boye) a karshe masu saurare daga cikin mafi girma na albarkar dake tattare da dabi’ar kunya, rabauta da gidan Aljanna, a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce (kunya na daga cikin imani shi kuma Imani shi ke raka mai shi shiga cikin gidan Aljanna) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon amfani da abinda muka saurara domin darajjar shugaban halittu Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.


***********************Musuc**********************************


Masu saurare a nan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala , ni da na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.