zababun Aiyuka-Mahimancin Hakuri dangane da 'yan adawa
shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin hakuri bisa halin masu adawa da ni’imar Allah kamar masu hasada da saurensu
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin hakuri bisa halin masu adawa da ni’imar Allah kamar masu hasada da saurensu, amma kafin shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan fafai.
**************************Musuc*********************************
Masu saurare, dabi’antuwa da wannan dabi’a na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah ya sanya yarda da kuma ta’arsa madaukakin sarki, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga sheikh Kaini rahamar Allah ta tabbata a gareshi, daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce:(ka yi hakuri a kan halayen masu kiyayya da ni’imar Allah domin har abada ba z aka iya hana mai sabo ba yin sabo ba kuma wannan wata dama ce da zaka bautawa Allah ta fiyeyar hanya).kamar yadda dabi’antuwa da wannan dabi’a mai girma na daga cikin hanyoyin cikar aiki wato mumuni ya cimma albarkar aikinsa na kwarai,kuma wannan shine abinda shugaban Halittu Muhamad Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya shiryar da mu a cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Kafi:(ababe guda uku duk wanda ba ya da su aiyukansa ba za su cika ba,na farko tsoron Allah da zai hana shi fadawa cikin sabon Allah, na biyu, halayen da zai mu’amala mai kyau tare da Mutane, na uku kuma shine hakurin da zai kalubalanci zahilcin jahilai) masu saurare, hakuri kan halayen masu kiyayya da ni’imar Allah da kuma cutarwarsu na daga cikin hanyoyin da suke karfafa imanin mumuni, da kuma samun tabbaci ga Allah adali mai hikima da kuma cewa wa’adin da Alkur’ani mai girma yayi na cewa Allah madaukakin sarki zai kare wadanda suka yi imani ,kuma zai basu nasara a nan duniya barantana ma a ranar shaida wato ranar Alkiyama, a cikin littafin Man La Yahduruhul fakih, an ruwaito hadisi daga shugaban Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) yayin da yake yiwa Dansa Muhamad bn Hanifa wasiya yace masa:(ka sani aiki da hanhali bayan imani da Allah madaukakin sarki shine mu’amala da mutane cikin siyasa, babu alheri gawanda ba ya mu’amala mai kyau ga wanda babu makafa ayi rayuwa da shi har lokacin da Allah ya sanya mafuta, hakika na samu mafi yawan masu mu’amala da mutane kashi daya cikin ma’auninsu kyautatawa ce kuma kashin daya cikin uku na daban gafala ne) abinda Imam (a.s) yake nufi da kashi daya cikin uku kyautatawa ce kuma kashi daya cikin ukun gafala ce shine mu’amala cikin siyasa tare da wassani,kyautata mutane da alheri tare da gafala wajen cutar da su.
Masu saurare bari mu karanto wani hadisi da yake bayyani kan sakamakon hakuri a kan halayen masu kiyayya ga ni’imar Allah da kuma cutarwarsu tun a nan duniya kafin aje ga Ranar Kiyama, hakika a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yana cewa:(hakika ‘yancecce,’yancecce ne a dukkanin Al’amuransa,hakika duk tsananin da ya shiga martaninsa hakuri, ko da wahalhalu da dama sun taru a garesa ba za su karya masa gwiwa ba,koda sun shiga cikin kanki,kurkuku ko kuma sun fuskanci karfi da danniya, za su canza wannan kanki da sauki,kamar yadda Annabi Yusuf Sidik (a.s), ‘yancinsa da aka canza masa da istibdadi, karfi da kuma katangewar kurkuru bai cutar da shi ba, haka zalika, dufun rijiya da kadaitar cikinta bai cutar da shi ba,babu abinda ke kabansa kamar tunanin ubangijinsa, sai Allah madaukakin sarki ya sanya shugaba bayan ya kasance Bawa, sannan kuma ya tayar da shi a matsayin ma’aikin ya ji kan Al’umma daga fadawa cikin bala’in fari da karamcin abinci.kuma kun san cewa bayan hakuri sai Alkheri, domin haka ku kasance masu hakuri kuma tilastawa kanku yin hakuri sai ku samu rabo mai girma).
****************************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi bayyani a kan halin kame baki ko kuma yin shuru idan ba fadar Alkheri ba,domin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki ke so ga bayinsa, hadisa da dama sun bayyani dangane da mahimancin wannan maudu’I, a cikin littafin Kafi, sikatu islam kulaini ya rauwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce: (ma’aikin Allah amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce wa wani mutune shin ka na son in sanar da kai wani umarni da zai sanya Allah madaukakin sarki ya sanya ka cikin Aljanna saboda shi,sai ya ce Ay Ya Ma’aikin Allah, sai Manzon Allah ya ce ka baiwa mutane abinda Allah ya arzuta ka da shi, sai mutuman ya ce Ya Ma’aikin Allah idan kuma na kasance ni nafi bukatuwa da abinda zan bayar din? Sai Ma’aikin Allah yace mas aka taimaki wanda aka zalunta, sai wannan mutune ya ce Ya Ma’aikin Allah idan ya kasance na fi wand azan taimakar rauni kuma fa?sai Ma’aikin Allah ya ce ka yi nasiha ga wanda yake bukata, sai wannan mutune ya ce ya Ma’aikin Allah idan na kasance na fi bukatuwa da nasihar kuma ina karamcin ilimi to yaya zanyi?sai Ma’aikin Allah ya ce masa ka rike bakinka ma’ana ka yi shuru, idan ba fadar Alkheri ba, abinda ya fi sauki daga cikin wannan ababe zai j aka zuwa gidan Aljanna).domin haka masu saurare yin shuru idan ba a fadar alheri ban a daga cikin kyawawen halayen dake yin jagora zuwa shiga Aljanna kamar yadda kuma ya ka kasancewa sanadiyar samun soyayyar mutane, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce:(daga cikin alamomin fikhu, ilimi, hakuri, da kuma kame baki ko kuma yin shiru idan ba fadar gaskiya, hakika kame baki babe ne daga cikin baben hikima, hakuri ya na samar da soyayya, kuma shi dalili ne na ko wani alheri) masu saurare, dabi’antuwa da dabi’ar kame baki ado ne ga mutune kuma sutura ce a gareshi kamar yadda shugabanmu Imam Sadik(a.s) yayi da shi a hadisin da aka ruwaito cikin littafin Man La Yahduruhul Fakih na shekh Saduk, Imam (a.s) ya ce:(shuru ko kuma kame baki taska mai girma, adon hakuri ne kuma suturar jahili ce) kamar yadda wannan hali mai kyau hanyar kariya ce ga cutuwa, a cikin Littafin Sawabul A’amal an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce (wani zamani zai zowa mutane, lafiya za ta kasance kashi goma, tare daga ciki ja bayan mutane ko kuma nisantuwar su daga aaiyukansu da Allah bai yarda da su ba,dayan kuma shine yin shuku ko kuma kame baki daga fadar wani abu idan ban a alheri ba ne ba) har ila yau a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadasi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(ka kame bakin ka domin yin hakan sadaka ce da ka yiwa kanka, Baw aba ya sanin hakikanin Imani har sai harshensa yay i fishi) har ila yau a cikin wannan littafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce: (ba zai kushe ana rutawa bawa mumuni kyakyawa ba matukar ya kame bakinsa, da zarar yay i magana za a rubuta masa kyakkyawa ko kuma mumuna, ma’ana za a rubuta masa Lada ko zunubi, ya danganta da abinda ya fada na alheri ne ko na sahari. Da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon kame bakunanmu matukar ba alheri ba ne zai futo daga cikinsu.
*********************Musuc**************************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.