Dabi'ar Neman Tuba
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyani kan dabi'ar gaggauta tuba ga Allah madaukakin sarki, ma'ana shi ne Mutum ya tarbiyar da kansa wajen gaggauta nemam Tuba da yin Istigfari a duk Likacin da tsinci kansa ya aikata wani laifi ga Allah madaukakin sarki, kadan ne ko kuma babba ne, da gaggan ne ko kuma cikin halin rashin sani ne, har zuwa ya kasance ya mallaki wannan hali mai kyau, amma kafin mu shiga cikin Shirin ga wannan.
**************************Musuc*****************************
Masu Saurare, idan Mutum ya kasance cikin wannan hali watau na gaggauta tuba da Istigfari a duk Lokacin da ya samu kansa cikin sabon Allah kadan ne mai yawa da gagan ko kuma cikin rashin sani, hakan zai kasance masa malaka ta yadda zai cimma Soyayyar Ubangiji, Allah madaukakin sarki na cewa:( Hakika Allah Yana Son masu Tuba kuma yana son masu tsarki) karshen Aya ta 222 cikin Suratu Bakara.Masu saurare, maliman Lugga ko kuma yaran larabci sun bayyana cewa Kalmar Tawwab siga ce mubalaga daga Ismul fa'il kuma ma'anarta yawan tuba a kan ko wani irin aiki na kuskure a yayin da Mutum ya aikata shi, Masu saurare, Hakika dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a na gaggauta tuba na daga cikin alamomin gaskiyar Imani da Allah madaukakin sarki, kamar yadda wasila ce ko kuma hanya na tabbatar da Imani a zukata, a cikin Littafin Alkhisal, an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa, aka ce daga cikin wasiyoyin Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ga Sahabansa ya bayyana cewa:(Ku yawaita Tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki, ku shiga cikin soyayyarsa, domin Hakika Allah Yana Son masu Tuba kuma yana son masu tsarki, Kuma Hakika Mumuni mai yawan tuba ne). Masu saurare, Hakika Dabi'antuwa da Dabi'ar gaggauta Tuba na daga cikin hanyar rabauta da yardar Allah madaukakin sarki,Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Usul-Kafi ya bayyana cewa: (Hakika Allah madaukakin sarki yana matukar jin dadin Tubar Bawansa daga Mutuman da Abin hawansa ya bace ya kasance yana nemansa har tsakiyar duhun Dare sai ya same shi,(ma'ana duk Mutuman wata dabbarsa da yake hawa ta bace rakumi ko kuma makamincin hakan, yana ta nemansa har tsakiyar Dare, a yayin da ya same ta, ka ga zai kasance mai farin cikin gaske, To Imam (a.s) y ace Allah madaukakin sarki ya hi wannan Bawa jin dadi, a duk Lokacin da ya ji wani Bawansa ya tuba). Hadisai masu albarka sun yi mana albishir da cewa gaggauta Tuba a duk Lokacin da Bawa ya samu kansa ya aikata wani kuskure ko ya yi sabo ya kan yi sanadiyar samun ceto daga Azabar Allah madaukakin sarki tare kuma da samun tsira a Lahira, Hakika cikin Littafin Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Hakika, Allah madaukakin sarki ya baiwa masu tuba wasu halaye guda uku, da kuma za a bayar da hali guda ga dukkanin ahalin samai da Kassai da sun kubuta, da farko fadar Allah madaukakin Sarki:( Hakika Allah Yana Son masu Tuba kuma yana son masu tsarki) karshen Aya ta 222 cikin Suratu Bakara, duk wanda Allah yake so ba zai azabtar da shi ba, hali na biyu kuma shi ne fadar Allah madaukakin sarki:(Wadanda suke dauke da Al'arshi da wadanda suke kewaye da shi suna yin tasbihi da yabon Ubangijinsu, suna kuma yin Imani da shi, kuma suna neman gafararsa wadanda suka bada gaskiya (suna cewa)Ya Ubangijinmu!Kai ka yawalci kowane abu, da rahamarka da iliminka,to ka gafarta wa wadanda suka tuba, suka kuma bi hanyarka, ka kuma kiyaye su da azabar (wutar) Jahimu) suratu Gafiri Aya ta 7, sannan kuma Imam (a.s) ya ci gaba da bayyana hali na uku yana mai Ishara da Ayar karshe ta cikin Suratu Furkan wacce aka saukar dangane da siffanta Ubadul-Rahaman, Allah madaukakin sarki ya ce:(Sai dai wanda ya tuba ya kuma bada gaskiya kuma ya yi aiki nagari, to wadannan Allah zai musanya munanan aiyukansu da kyawawa. Allah kuwa ya kasance mai gafara ne mai jin Kai) Suratu furkan Aya ta 70.
**********************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zababbun aiyuka na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran, Ci gaban shirin zai fara da hadisin Annabin Rahama masoyinmu mai shiryarwa, Zababben Allah Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka wanda aka ruwaito cikin Littafin Kafi na Sikatu Islam Kulaini, inda ya ce:(Bawa da ya himmatu da aikata kyakkyawa, idan bai samu damar aikatawa ba Allah madaukakin sarki zai rubuta masa lada na kyakkyawar Niyarsa, idan kuma ya aikata, Allah zai rubuta masa Lada goma na aiki mai kyau)sannan Ma'aikin Allah ya ci gaba da cewa (duk Bawan da ya gudiri aikata mumuna, idan bai aikata ba, ba za a rubuta masa komai ba, idan kuma ya aikata za a jinkirta har tsahon sa'o'I 7, sai Mala'ika mai rubuta kyawawa yace wa Mala'ika mai rubuta munana, kadda kayi gaggauwa mai yiyuwa ya aikata wani aiki na alheri wanda zai shafesa wannan mumunan aiki nasa, domin Allah madaukakin sarki ya ce:( Hakika Kyawawan ayyuka suna shafe mumuna, wannan tunatarwa ne ga masu tunawa*Kuma ka yi hakuri, domin Hakika Allah ba ya tozarta Ladan masu kyautatawa) Suratu Hudu Aya ta 115 da ta 116. Ko kuma ya biyo wannan Lefi da Istigfari watau neman gabara, sannan sai Ma'aikin Allah ya ci gaba da cewa idan aka dauki tsahon sa'o'I bakwai bai aikata wani aiki mai kyau ko kuma Istigfari ba, sai Mala'ika mai rubuta Kyawawa yace wa mai rubuta munana rubuta ga wannan Shakiyi wanda ya harmatawa kanasa rahamar Ubangiji). Masu Saurare Hakika daga cikin kyawawan sakamako na dabi'ar gaggauta tuba, rabauta da samun suturcewar Ubbangiji a Duniya da Lahira. A cikin Littafin Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce: (Idan Bawa ya tuba tuba ta gaskiya, Allah madaukakin sarki zai so shi, ya kuma suturta shi a Duniya da Lahira) sai wanda ya ruwaito Hadisin ya tambaye Imam (a.s) yaya Allah zai suturta shi? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa( za a mantar da Mala'ikansa abinda suka ruba a kansa na zunubai, sannan kuma za a yi wahayi ga gabobinsa, su boye duk wani aiki na zunubi da ya aikata, sannan kuma a yiwa Kasa wahayi ta boye duk wasu aiyuka da ya kasance yana aikatawa na zunubai, to ka ga babu wata shaida da za tayi shaida kan aiyukan da ya aikata na zunubai zai ya hadu da Allah ba tare da ko wani zunubi ba).Masu Saurare, har ila yau daga cikin kyawawen sakamakon na tarbiyatar da kai wajen gaggauta tuba a yayin ko wani irin laifi ko kuskure, kare kai daga fadawa cikin manyan zunubai, Hakika cikin Littafin Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Iman Muhamad Bakir (a.s) ya cewa daya daga cikin Sahabansa:(Zunuban Mumuni idan ya tuba, za su kasance gafararru watau an gafarta masa,sai ya ci gaba da aiyukansa, bayan ya tuba ya kuma yi Istigfari, amma Wallahi ita tuba ba kowa ya ke samun yin taba face ahalin Imani, Shin kana ganin cewa Bawa Mumuni zai yi nadama a kan zunubansa ya kuma yi istigfari ya tuba sannan Allah ya ki karbar tubar sa? Duk lokacin da Mumuni ya koma ga Istigfari Allah zai dawo masa da gafara, domin Shi Allah mai gafara mai jin kai ne, yana karbar Tuba ya kuma yi afuwa ga munanan aiyuka, ka kuji debawa Mumuna kauna daga Rahamar Allah) da fatan Allah madaukakin sarki ya sanya mu masu gaggauta Tuba da Istigfari a duk Lokacin da muka samu kanmu cikin aikata wani kuskure domin mu rabauta da gafarar Ubangiji Allah madaukakin sarki dan albarkar riko da wulayar Annabi Muhamadu da kuma iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya.
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu