Mar 04, 2016 12:44 UTC

shirin zai yi bayyani kan mahimancin kama baki ko kuma shuru matukar ba fadar Alheri ba


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, a shirin da ya gabata mu yi bayyani kan mahimancin kama baki ko kuma shuru matukar ba fadar Alheri ba, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


*************************Musuc***********************


Masu saurare, yin shuru ga kalaman da Allah madaukakin sarki ya ki, kamar kalaman da ba su da amfani,zarki, kirkirar magana, yin karya da makamantansu na  gadawa mai yinsa kekesar zuciya,rashin kunya da kuma mumunar makoma, a cikin Littafin Nahjul balaga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya bayyana cewa:(mai yuyuwar fadar wata kalma tayi sanadiyar korewar ni’ima, duk wanda maganarsa tayi yawa, kuskuransa zaiyi yawa, kuma duk wanda kuskuransa ya yi yawa, kunyarsa za ta ragu, duk kuma wanda kunyarsa ta ragu, tsoron Allansa zai ragu, duk kuma wanda tsoron Allansa ya ragu, zuciyarsa za ta mutu, duk kuma wanda zuciyarsa ta mutu, zai shiga wuta), a bangare guda kuma kiyaye harshe ko kuma rike baki daga fadar kalaman banza na kasancewa sanadiyar samun tsira da izza, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(tsirar mumuni, kiyaye harshensa) har ila yau a cikin wannan littafi an ruwaito wani hadisi, inda a cikin aka bayyana cewa wani Mutune ya je wajen Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce Ya Ma’aikin Allah ka yi mani wasici Sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce masa ka kiyaye harshenka, bayan wani lokaci wannan mutune ya sake komawa wajen Ma’aikin Allah a karo na biyu ya ce masa ya ma’aikin Allah ka yi mani wasici sai Ma’aikin Allah ya ce ka kiyaye harshenka, har ila ya sake komawa a karo na uku ya sake ce masa ya ma’aikin Allah ka yi mani wasici, a karo na uku ma’aikin Allah ya kara ce masa ka kiyaye harshenka kai conka!shin wai kana tunanin ana azabtar da Mutane da wuta, face ba abinda harsunasu suka shuka ba) har ila yau a cikin littafin Kafin an ruwaito wani hadisi, inda a cikinsa aka ce wani mutune ya zo wajen Imam Kazim (a.s) ya ce masa ya Dan Ma’aikin Allah ka yi mani wasici, sai Imam (a.s) ya ce masa ka kiyaye harshenka sai ka daukaka,kada ka matsawa Mutane a yayin dake jagorantarsu , idan kuma ka matsa musu mutuncinka zai zube)


Masu saurare rikon baki ga fadar maganar da Allah madaukakin sarki yake ki na samarwa mutune izza a duniya da Lahira,, idan mutune ya kiyaye zai samu tabbacin cewa duk abinda zai fito da bakinsa alheri ne,kuma hakan shine abinda Allah madaukikin sarki ke so ga bayinsa kamar kyakkyawar magana da Allah tabaraka wa ta’ala ya sanya ladanta a matsayin ladan sadaka,a cikin littatafan Khisal da Amaly shekh Saduk ya ruwaito hadisi daga shugabanin shiriya Sayyidi sajidin da kuma zainu Abidin suna cewa (kyakkyawar magana na kara Dukiya, na kuma bunkasa arzuki, tana kara kuma yawan kwanaki ko shekaru kuma tana janyo soyayya a cikin iyalai tana kuma yiwa mai yinta jagora zuwa gidan Aljanna) a cikin Littafin Al’ihtijaj an ruwaito wani hadisi , inda a cikinsa aka tambayi Imam Sajjad a kan magana da shuru wane ya fi? Sai Imam (a.s) ya ce ko wane daga cikinsu a kwai alfanonsa, idan kuma aibin yin shuru ya gushe to maganar tafi domin Allah madaukakin sarki bai aiko Annabawa ba don suyi shuru ya tayar da su domin suyi bayyani ,ban a kuma caccantar shiga Aljanna da shuru ba,kuma biyayya ga Allah bata tabbatuwa da shuru ba, kuma ba a samun kariya na shiga wuta da shuru,dukkanin wadannan sai da magana,ba zan iya daidaita wata da rana ba), a cikin Littafin Man La Yahduruhul fakih an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(magana a kan gaskiya ta fi shuru a kan karya) har ila yau a cikin Littafin Nahjul Balaga Imam Ali (a.s) ya ce:(babu alheri ga yin shuru a kan gaskiya kamar yadda babu alheri yin magana cikin jahilci).


*************************Musuc********************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan dabi’ar girmama fakirin ko kuma talaka na musulmi domin shi ma na daga cikin kyawawen dabi’u da Allah madaukakin sarki ke so kuma shine abinda Shugaban halittu ya yi wasici a kansa, a cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Man La Yahduruhul fakih ya ce:(wanda ya girmama fakiri musulmi zai hadu da Allah madaukakin sarki ranar Alkiya yana cikin yardarsa,ku saurara! Duk wanda ya girmama dan uwansa musulmi, hakika ya girmama Allah madaukakin sarki)  masu saurare, kamar yadda girmama fakiri musulmi ya kan sa a samu yardar Allah, haka zalika wulakantar da shi ,yakan janyo talauci da kuma fishin Ubangiji da fatan Allah yayi mana tsari da hakan, a cikin Littafin Uyunul Akhbaru Ridha, an ruwaito hadisi daga zabebben halittu yardar Allah ta tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce (duk wanda ya kaskantar da mumuni ko kuma ya wulakanta shi saboda talaucinsa da kuma karamcin abinda ke hanunsa,Allah zai sanya masa bakin ciki da bacin rai ranar Alkiyama) a cikin Littafin Ikabul A’amal an ruwaito hadisi daga shugabanmu Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce (kada ku wulakanta wani talaka mumuni , duk wanda ya wulakanta mumuni ko kuma ya kaskantar da shi, Allah zai wulakantar da shi, kuma zai kasance cikin wulakanta har sai ya dawo daga wannan dabi'a ta wulakanci ko kuma ya tuba).a cikin wani hadisi na daban kuma Imam Sadik (a.s) ya bayyana mana cewa misdakin rashin girmama musulmi shine ka ki taimaka masa a yayin da yake cikin bukata,hakika sikatu Islam kulaini ya ruwaito hadisi daga Abi Harun  yayin da ya kasance cikin wata jama’a na sahaban Imam Sadik (a.s) ya ce (minene ya sanya kuke wulakantamu? Sai wani mutune daga cikin mutanan Khurasan ya tashi, ya ce ma’azallah da in wulakanta ku ko kuma in yi sako sako da wani abu daga cikin Al’amarunku ba,sai Imam (a.s) ya ce haka ne hakika kana daga cikin wadanda suka wulakantmu , shin ba ka ji wani mutune ba yayin da muke kusa da ju’ufa ma’ana a hanyar Hajji yana ce maka, ka dora ni bisa dabbarka, a wannan lokaci ka ki ka taimake shi ba, wannan shi ke tabbatar da cewa ka wulakanta mu, kuma duk wanda ya wulakanta mumuni kamar ya wulakanta mu kuma ya kaita hurmar Allah madaukakin sarki) har ila yau a cikin littafin Ikabul A’amal an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) a yayin wata khudubarsa ya ce:(duk wanda ya wulakanta wani talaka musulmi saboda talaucinsa ya kuma yi wasa da Al’amarinsa kamar ya yi wasa da hakin Allah ne kuma zai kasance a madakar Allah da fishinsa har sai ya nemi yardar wanda ya wulakanta,kuma duk wanda ya girmama fakiri musulmi zai hadu da Allah madaukakin sarki cikin yardarsa) da fatan Allah madaukakin sarki ya sanya muna cikin wadanda Allah ya yarda da su don darajar shugaban halittu Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.


*******************************Musuc*********************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.