Mar 04, 2016 16:29 UTC
  • zababun Aiyuka-Taimakon Mumuni a Lokacin da ba ya nan

shirin na yau zai bayyani kan taimakon mumuni a lokacin da ba yanan,domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un dake sanya mumuni ya rabauta da taimakon Allah a Duniya da Lahira


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai bayyani kan taimakon mumuni a lokacin da ba yanan,domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un dake sanya mumuni ya rabauta da taimakon Allah a Duniya da Lahira, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


*************************Musuc****************************


Masu saurare, hakika babban malamin hadisin nan sheikh Barki cikin Littafinsa na Almahasin da kuma Sheikh Saduk cikin littafinsa Sawabul A’amal sun ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce (duk wanda ake kokarin cin naman dan uwansa mumuni a gabansa, sai ya taimakesa kuma ya kare sa, Allah zai temakesa kuma ya karsa a Duniya da Lahira,kuma duk wanda aka ci naman dan uwansa mumuni a gabansa ba tare da ya kare shi kuma ya taimake shi, alhali ya nada ikon yin hakan, Allah madaukakin sarki zai wulakantaci a duniya da Lahira) masu saurare kare mumuni yayin da ake cin namansa na daga cikin kyawawen dabi’un da suke yin sanadiyar rabauta da gidan Aljanna, kamar yadda shugaban halittu Muhamad zababen Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Sawabul A’amal ya ce (duk wanda ya kare dan uwansa musulmi yayin da aka kawo masa gulmarsa, Aljanna ta wajabta a gare shi). Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana mana irin girman Ladan dake tattare ga wanda ya taimaki Dan uwansa mumuni daga ciki har da taimakonsa a yayin da aka kawo gulmarsa, a cikin Littafin Almahasin an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa Imam (a.s) ya bayyana cewa:(babu wani mumuni da zai taimaki dan uwansa mumuni da aka zalunta sai ya kasance ya nada ladan da ya fi wanda ya yi azumi na wata guda, ko kuma ya yi I’itikafi a masallacin harami, babu wani mumuni da zai taimaki dan uwansa zai Allah ya taimake shi a duniya da Lahira,kuma babu wani mumuni da zai tozarta Dan uwansa a yayin da yake da ikon taimakonsa sai Allah ya tozar ta shi a Duniya da Lahira).


Masu saurare, daga albarkatun dake cikin wannan dabi’a na taimakon dan uwa, shine samun tsira daga duk wani nau’I na sharri da bala’I,a cikin littafin Ikabul A’amal an ruwaito hadisi daga shugaban masu gaskiya tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya kare dan uwansa mumuni yayin da aka kawo gulmarsa a wani gurin zama, Allah zai kare shi daga fanin shari dubu a duniya da Lahira,idan kuma ya ki kare sa har ma yayi al’ajabi da abinda aka fada na gulmar, za a rubuta masa zunubi daidai da wanda ya zo da gulmar), a cikin Littafin Amaly na shekh Tusy, an ruwaito hadisi inda a cikin aka ce wani mutune ya nuna rashin jin dadinsa  a yayin da wani ya kawo gulmar wani mutune a wajen Ma’aikin Allah (s.a.w) an ce mutuman da aka kawo gulamarsa dan kabilar mutuman da ya nuna rashin jin dadinsa sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(duk wanda ya mayar da martani a yayin da aka kawo gulmar dan uwansa , zai kasance ya nada hijabi ko kuma garkuwa daga wuta) har ila a yau a cikin wata wasiya da Ma’aikin Allah (s.a.w) ya yiwa shahararen sahabin nan Aba Zar Algaffari ya ce:(Ya Aba Zar, duk wanda ya kare dan uwansa a yayin da aka kawo masa gulmarsa, ya kasance hakki ne a kan Allah da ya ‘yantar da shi daga shiga wuta) a cikin wasiyar da yayiwa shugaban muwahidai, Aliyu bn Abi talib (a.s), Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Ya Ali, duk wanda aka kawo gulmar dan uwansa musulmi, alhali ya na iya kare shi da kuma taimakonsa, sai bai kareshi ba,Allah zai yulakanta shi a duniya da Lahira) muna neman tsari daga Allah madaukakin sarki daga wulakantarsa  na duniya da Lahira.


********************************Musuc*****************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimancin tausayin juna domin shima na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki ke so, har ila yau wannan hali na daga cikin halayen shugaban Halitta, abin koyi ga talikai, mai shiryarwa, zababben ubagiji tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka a cikin suratu Fatahi Aya ta 29 Allah madaukakin sarki ya ce:((Annabi) Muhammadu manzon Allah ne kuma wadanda suka bada gaskiya tare shi (masu) masu tsanani a kan kafirai kuma masu tausayin junansu ne …) masu saurare, tausayin juna na daga cikin ababen da suke yin sanadiyar saukar rahama ga mumunai, a cikin Littafi Risalatu Sa’adiya na Allama hilly, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce ga wadanda suke tare da shi,(na Rantse da wanda Raina ke hanunsa, Allah bay a sanya Rahama sai ga mai tausayi, sai suka ce ya ma’aikin Allah dukkaninmu masu tausayi ne sai Ma’aikin Allah ya ce mai tausayi bas hi ba ne mai tausayin kansa da iyalansa kawai ba, saidai mai tausayi shine wanda ke tausayin musulmi baki daya), har ila yau a cikin wannan Littafi, an ruwaito wani hadisin na daban daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce Allah madaukakin sarki ya ce:(in kun kasance kuna son Rahamata ku tausayawa junanku), a cikin Littafin Ja’afariyat, an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) shi kuma daga Ma’aifansa daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce :(duk wand aba ya tausayin Mutane, Allah ba zai ji tausayin sa ba), a cikin wani hadisin na daban kuma Manzon Allah (s.a.w) ya ce:(masu tausayi Allah Arrahamanu zai ji tausayinsu, ku tausayawa wadanda ke cikin kasa sai wanda ke sama ya ji tausayinku), shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya bayyana mana cewa tausayi juna na daga cikin misdakin tsoron Allah da ya tattara dukkanin Alkhairan Duniya da Lahira, cikin riwayar da Shekh Kulaini ya ruwaito cikin Littafinsa Kafi, yayin da yake tarbiyatar da sabansa da Dabi’un Allah madaukakin sarki, Imam (a.s) ya ce: ku ji tsoron Allah,kuma ku zamanto ‘yan uwa masu son juna saboda Allah masu  tausayi da ziyartar junansu, ku ziyarci junanku, ku tunawa junanku al’amuranmu kuma ku raya shi) bayan haka Imam (a.s) ya yi wasici na yin kokari wajen tausayin juna domin yin hakan na daga cikin ababen da Allah madaukakin sarki yayi umarni a kansa, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce (wajibi ne a kan musulmai yin kokari wajen sada zumunci, taimakawa juna bisa tausayi,girmamawa wajen taimakon mabukata har sai kun kasance kamar yadda Allah madaukakin sarki ya umarce ku masu tausayin junanku,kamar yadda ya kasance ga Mutanan Ansar wato mutanan madina a lokacin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka).


************************Musuc***************************


Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.